Majalisar dokokin Iran ta samar da wani daftarin dokoki kan yadda ƙasar za ta riƙa iko da mashigar Hormuz, kuma ana sa ran kaɗa ƙuri'a kan daftarin a cikin mako mai zuwa.
Shugaban hukumar kula da ayyuka na majalisar, Mohammed Reza Rezaei Kochi ya ce daftarin ya ƙunshi sauye-sauye kan yadda jiragen ruwa ke ratsawa ta mashigar Hormuz sannan kuma akwai tsarin karɓar kuɗaɗe daga jiragen.
Mista Kochi ya bayyana wa kafar dillancin labarai ta Fars cewa "ɗaukacin ƴan majalisar za su amince da daftarin sannan daga baya a sanar da fara amfani da shi".
Bayanai sun nuna cewa daftarin ya ƙunshi wasu matakai guda biyar:
- Haramcin ratsawar jiragen abokan gaba: Za a haramta wa duk wani jirgin dakon man fetur mai alaƙa da Amurka da Isra'ila ratsawa ta mashigar Hormuz har abada.
-Karɓar haraji: Za a karɓi kuɗi a matsayin jangali kan aikin yin jagora da tabbatar cewa jiragen ruwa sun ratsa ta wannan mashiga cikin aminci.
-Tallafa wa takardar kuɗin Iran: A ƙoƙarin bunƙasa darajar takardar kuɗi ta riyal, duk wani jirgi mai ratsawa zai biya jangali ne ta amfani da takardar kuɗin Iran ta Riyal.
-Amfani da sunan Mashigar Gulf: Za a buƙaci duk wani jirgin da zai ratsa ya yi amfani da asalin sunan da aka san mashigar da shi, wato mashigar Persia a duk takardun da za a cike da kuma bayanan da suke bayarwa na tafiya.
-Yadda za a kasafta kuɗi: Za a kasafta kuɗaɗen jangali da aka samu kamar haka: Za a kashe kashi 30% wajen ƙarfafa soji da tabbatar da tsaron yanki, sai kuma kashi 70% don inganta rayuwar al'umma.