Mece ce makomar Kwankwasiyya bayan sauya sheƙar Kwankwaso?
Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
Tun bayan ficewar tsohon jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwanso daga jam'iyyar, mutanen da ke bibiyar al'amuran siyasa suka fara magana game da makomar tafiyar kwankwasiyya da ya assasa.
Sauya shekar tasa na zuwa ne watanni bayan ficewar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Fitar Abba daga NNPP ya tafi da kaso mafi yawa na magoya bayan tafiyar Kwankwasiyyar zuwa APC, waɗanda har yanzu ke sanya jar hula, wata alama da ake alaƙanta ƴan Kwankwasiyyar.
Ficewar jagororin tafiyar biyu zai sauya fasalin ƙungiyar siyasar Kwankwasiyyar, wadda tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kafa tun bayan komawarsa kan karagar mulki tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Mece ce Kwankwasiyya da manufofinta?
Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Jaafar Jaafar babban editan Jaridar Daily Nigerian, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mai bibiyar siyasar jihar Kano ya ce Kwankwasiyyar wata aƙidar siyasa ce da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa.
Ya ce an assasa wannan aƙida ne sakamakon gwamnan jihar Kano har sau biyu da Sanata Rabiu Musa kwankwanso ya yi.
Fitaccen ɗan jaridar ya kuma ce daga cikin manufofin aƙidar sun haɗa da kare muradun talakawa, kamar yadda ƙungiyar ke iƙirari lokacin kafa ta.
''Aƙidar Kwankwasiyya ta ƙunshi duk abin da ya shafi talaka, gwamnati ta mayar da hankali kan abin da ya shafi ci gaban talakawa, musamman fannin ilimi'', in ji shi.
Jaafar Jaafar ya ƙara da cewa fannin ilimi na daga cikin muhimman fannonin da aƙidar Kwankwasiyya ta sanya a gaba.
''A tsarin Kwankwasiyya an zayyana wasu abubuwan da duk wanda ya hau mulki a kan doron Kwankwasiyya dole ne ya ba su fifiko, wato waɗanda Kwankwason ya assasa, kamar ciyar da ƴan makaranta, da ba su kayan makarantu da tura ɗalibai karatu ƙasashen waje'', in ji shi.
Tarihin kafuwar Kwankwasiyya
Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Jaafar Jaafar ya ce aƙidar Kwankwasiyya ta kafu ne a lokacin da Kwankwaso ya yi yunƙurin komawa gwamnan Kano karo na biyu a 2011.
"A lokacin ne ya karaɗe dukkan ƙananan hukukomin Kano 44, a yaƙin neman zaɓe wanda a wannan zagaye ne aka far ambaton kalmar a matsayin taken gangamin yaƙin neman zaɓensa'', in ji shi.
Fitaccen ɗan jaridar ya ce tun daga lokacin ne aƙidar Kwankwasiyya ta yaɗu tare da yin suna sosai a ciki da wajen Jihar Kano.
Wannan ƙungiya dai ta yi suna sosai a Najeriya, inda magoya bayan tsohon gwamnan, ke tawassali da irin ayyukan ci gaba da suka ce shugaban nasu ya yi a wancan lokacin, domin kafa hujjar farin jinin da ƙungiyar take da shi a fagen siyasa.
Wanne tasiri Kwankwasiyya ta yi a siyasar Kano?
Asalin hoton, Rabiu Kwankwaso/FB
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aƙidar Kwankwasiyya ta yi matuƙar tasiri, musamman a siyasar jihar Kano, da ake yi wa kirarin ''Siyasar Kano sai Kano''.
Jaafar Jaafar ya ce aƙidar Kwankwasiyya ta yi tasiri a Kano, domin tun bayan kafuwawarta babu wani ɗansiyasa da ya kai Sanata Kwankwaso tasiri a fagen siyasar jihar.
''Duk wanda zai faɗi gaskiya kan siyasar jihar Kano, zai maka siyasar Kano ta mutum biyu ce, wato Kwankwaso da sauran'', kamar yadda mai bibiyar siyasar Kanon ya bayyana.
''Ya gwada haka a zaɓen 2019, lokacin da ba shi da gwamnati ya tsayar da ɗantakarar gwamna, kuma ya samu ƙuri'un da kowa bai yi tsammani ba, har sai da aka yi zaɓen cike gurbi sannan aka kayar da shi'', in ji shi.
Jaafar Jaafar ya ƙara da cewa Kwankwaso ya kuma sake jam'iyya a 2022, wadda ba kowa ne ya santa ba, kuma ya shiga zaɓukan 2023 ya kayar da gwamnati mai ci ya kafa sabuwar gwamnati da gagarumin rinjayen ƴan majalisar jiha da na tarayya ciki har da sanataci biyu cikin uku na Kano.
Ina makomarta bayan rabuwar Kwankwaso da Abba?
Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB
Tun bayan ficewar Sanata Rabiu Kwankwanso daga NNPP, mutanen da ke bibiyar al'amuran siyasa suka fara magana game da makomar tafiyar kwankwasiyya da ya assasa.
Kan haka ne Jaafar Jaafar ya ce jama'a Kwankwaso suke bi, domin kuwa shi ne Kwankwasiyyar.
''Ko yanzu tun bayan da ya ayyana shiga jam'iyyar ADC alƙaluma sun nuna cewa an samu tururuwar mutane da suka riƙa rajista a jam'iyyar tun ma kafin ya shiga'', in ji shi.
Ya ci gaba da da cewa rabuwar Abba da Kwankwaso ba sabon abu ba ne a siyasar Kwankwasiyya, domin hakan ta taɓa faruwa a 2017, lokacin da Kwankwaso ya fice daga APC zuwa PDP bayan samun saɓani da Ganduje.
''A lokacin Ganduje na tare da kusan duka shugabannin ƙananan hukumomi da kwamishinoni da ƴan majalisa, amma duk da haka sai da ya bayar da mamaki a zaɓen 2019'', in ji shi.
Don haka ne fitaccen ɗanjaridar mai zaman kansa ke ganin Kwankwaso zai sake haɗa tafiyar aƙidarsa a sabuwar jam'iyyar da ya koma.
"Kwankwaso na riƙe da kaso mafi yawa na masu dangwale, yayin da su kuma sauran ƴansiyasar Kano ke riƙe da kaso 80 na manyan ƴansiyasar jihar'', in ji shi.
Me ya sa har yanzu Abba ke saka jar hula?
Asalin hoton, Isah Muhammad Salisu/FB
Ɗaya daga cikin alamomin aƙidar Kwankwasiyya shi ne sanya jar hula ga maza da kuma jan mayafi ga mata.
Wani abu da ke ɗaukar hankali mazanarta siyasar jihar Kano shi ne yadda har yanzu Gwamna Abba da ƴantawagarsa da suka koma APC ke ci gaba da amfani da jar hula, ko hakan na nufin har yanzu su ƴan aƙidar Kwankwasiyya ne?
Jaafar Jaafar ya ce har yanzu suna so su riƙa alaƙanta kansu da aƙidar Kwankwasiyya, saboda sun san manufofin aƙidar.
''Sun san yadda aƙidar take a zukatan talakawa, da farin jininta, don haka ne suke ci gaba da ayyana kansu a matsayin ƴan aƙidar'', in ji shi.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai