Masu zanga-zanga sun yanke hulda da gwamnatin Sudan
Asalin hoton, Reuters
Shugabannin masu zanga-zanga a Sudan sun ce ba su ba gwamnatin soja ta kasar wadda ta maye gurbin hambararren shugaba Omar al-Bashir.
Suna zargin gwamnatin tana dauke da sauran mambobin tsohuwar gwamnatin al-Bashir.
Dubban masu zanga-zangar sun mamaye harabar ma'aikatar tsaro ta kasar a birnin Khartoum domin tataunawa gabanin sanarwar wata sabuwar gwamnati ta farar hula da suke o ta karbi ragamar mulki daga hannun gwamnatin sojin kasar.
Asalin hoton, AFP
A nata bangaren kuwa, gwamnatin sojin ta ce a shirye take ta mika mulki, amma ta fi so a yi hadin gambiza, wato a kafa gwamnatin sojoji da fararen hula.
Amma kakakin masu zanga-zangar Mohamed al-Amin ya ce sun dawo daga rakiyar majalisar sojojin da ke mulkin kasar, kuma suna kallonta a matsayin "wani bangare na tsohuwar gwamnatin" kuma su sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya har sai sun cimma bukatunsu.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai