'Yan Sudan na neman sojoji su hambare Omar al-Bashir
Asalin hoton, Reuters
A Sudan dubban masu zanga-zanga ne suka sake taruwa a dare na biyu suna neman Shugaba Omar al-Bashir ya sauka daga mukaminsa.
Da alama suna son sojojin kasar su hambare shugaban ne, kuma a kafa wata gwamnatin rikon kwarya kafin a yi zabe.
Wannan ne bore mafi muni ga mulkin al-Bashir da 'yan kasar suka yi tun watan Disambar bara.
Shugaba al-Bashir ya ki sauka daga mukaminsa, inda yake cewa masu adawa da shi su nemi mulki ta hanyar kayar da shi a zabe.
Kawo yanzu dai sojojin kasar ba su dauki wani mataki ba.
Asalin hoton, AFP
A Khartoum, jami'an tsaro sun rika amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar da suka mamaye shakwatar sojojin kasa ta kasar.
Wannan zanag-zangar ta zo daidai da cika shekara 34 da juyin mulkin da al-Bashir yayi wa Shugaba Jaafar Nimieri.
Kawo yanzu dai rahoanni na cewa mutum daya ya rasa ransa a birnin Omdurman da ke tsallaken kogn Nil daga Khartoum.
Abin lura da shi a nan shi ne al-Bashir na neman 'yan adawa su bi hanyar demokradiyya, bayan shi da kansa juyin mulki yayi wa gwamnatin da yake adawa da ita.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai