Hotunan yadda aka yi wasan kokawar mata a Saudiyya

An gudanar da wasan kokawa na Wrestling na mata a karon farko a Saudiyya ranar Alhamis.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da wasan kokawar na Wrestling na mata a karon farko ne a birnin Riyadh na kasar Saudiyya ranar Alhamis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An shirya wasan ne lokacin da kasar ke daukar matakan sassauta dokokinta masu tsauri kan nishadi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Natalya ta doke Lacey Evans a wasan da aka yi wa lakabi da Crown Jewel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan na cikin taron WWE Crown Jewel da aka yi a filin wasa na Sarki Fahd wanda ke daukar 'yan kallo 68,000

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Saudiyya tana kokarin sauya irin kallon da ake yi mata a duniya na wadda ta ke tauye hakkin mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai dai har yanzu mata na fuskantar matsi kuma an sha kama masu fafutukar kwato hakkin mata da yawa da ke kamfe a kan matsin