Abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga 1 zuwa 7 ga watan Maris 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Kocin Iraqi ya buƙaci a ɗage wasan cike-gurbin kofin duniya saboda yaƙin Iran

    Iraq

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Iraqi Graham Arnold ya yi kira a ɗage wasan cike-gurbi da tawagar ƙasar za ta fafata a ƙarshen wannan watan zuwa wani lokacin daban saboda yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a Iran.

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iraqi za ta fafata ne ko dai tawagar Bolivia ko kuma ta Suriname a birnin Monterrey da ke Mexico a ranar 31 ga Maris.

    Wanda ya samu nasara a wasannin ne zai samu gurbi a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da za a buga a ƙasashen Amurka da Mexico da Canada da za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni.

    Sai dai Iraqi na fargabar ba za ta iya tafiya zuwa ƙasar da za a buga wasan ba a Mexico saboda yanayin yanayin yaƙin ya kawo ƙalubale kan zirga-zirgan jiragen sama a Gabas ta Tsakiya.

    Tun ranar 28 ga watan Fabrairu da aka ƙaddamar da hare-hare a Iran ne aka rufe sararin samaniyar Iraqi domin tsaro.

  2. Wasannin ƙwallon ƙafa da za a fafata a ƙarshen mako

    Wasa

    Asalin hoton, Getty Images

    A ƙarshen makon nan ma za a fafata wasannin ƙwallon ƙafa a matakai daban-daban a ƙasashe da dama, musamman a nahiyar turai.

    Daga cikin wasannin da za a fafata akwai na wasannin gasar ƙalubale a Ingila kamar haka:

    • Mansfield da Arsenal
    • Wrexhan da Chelsea
    • Newcastle da Man City

    A ƙasar Spain kuma wasannin La Liga ne za a fafata. Daga ciki akwai:

    • Atletico Madrid da Real Sociedad
    • Athletic Club da Barcelona

    Italiya

    • Cagilari da Como
    • Atalanta da Udinese
    • Juventus da Pisa
  3. Faɗowa daga gasar Premier na iya janyowa Spurs asarar fam miliyan 250

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ya rage saura wasanni 10 a kammala wasannin kakar wasan bana, maki daya ne kacal raba Tottenham Hotspur da West Ham wadda ke matsayi na 18 akan teburin.

    Bugu da ƙari ƙungiyar na fuskantar wani irin mummunan yanayi a cikin filin wasa, lamarin da ke sanya alamar tambaya kan ko za ta iya samun makin da ta ke bukata domin ta tabbatar da tsirarta a gasar.

    Ana dai da kusan tabbas cewa Wolves da Burnley za su kasance a matakai biyu na ƙarshe a teburin, kuma ƙungiyoyi irin su West Ham da Nottingham Forest da Leeds United har yanzu suna cikin haɗari.

    Spurs ta samu kuɗin shiga na fam miliyan 690 a bara, bisa ga bayanai daga aka samu daga wani rahoton masana kan hada-hadar kuɗaɗen wasanni na Turai.

    Wannan kudin shiga zai fuskanci barazana idan har ta fado zuwa matakin gasar Championship.

    A cewar sashen nazarin wasanni na BBC, sarar da ƙungiyar za ta yi zai iya kai wa kusan fam miliyan 261 jimiila.

    Wani muhimmin ɓangare da zai cutar da ita shi ne rashin samun kuɗaɗen shiga na tikiti, wanda ya samawa ƙungiyar fam miliyan 130 a kakar wasan nan, wanda shi ne na biyar mafi girma a nahiyar.

  4. Harry Kane zai yi jinya na wai ɗan lokaci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin din Ingila Harry Kane ba zai buga wasan gasar Bundesliga na ranar Juma'a ba, wanda Bayern Munich za ta karɓi baƙuncin Borussia Monchengladbach sakamakon ƙaramin rauni da ya ji a ƙafarsa.

    Kane, mai shekaru 32, ya buga dukkan wasanni 24 na gasar lig ta Jamus a kakar wasan bana, kuma shi ne kan gaba wajen zura ƙwallo a raga da ƙwallaye 30.

    Kocin Bayern Vincent Kompany ya jaddada cewa raunin Kane "ba wani abu bane mai tsanani" kuma tsohon ɗan wasan na Tottenham ya kamata ya buga wasan gasar cin kofin zakarun Turai da Bayern za ta fafata da Atalanta a ranar 10 ga watan Maris.

    Bayern mai riƙe da kofin Bundesliga ta bayar da tazarar maki 11 a saman teburin gasar bana bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2 a ranar Asabar.

    Kane ya zura ƙwallaye biyu a wannan wasan inda yawan ƙwallayen da ya ci a duk gasanni na bana suka kai 45.

  5. Kocin Brighton ya caccaki ƴan wasan Arsenal kan ɓata lokaci

    Mai horas da ƙungiyar Brighton Fabian Hurzeler, ya soki Arsenal kan dabarar da ta yi amfani da ita na ɓata lokaci, sa’ilin da ya gana da manema labarai bayan kashin da suka sha a hannun Arsenal ɗin ranar Laraba.

    Lokacin da ya yi Magana da BBC, Hurzeler ya ce “abin da masu kallo ke son gani shi ne wasa sosai, ba ɓata lokaci ba.”

    “Ban zan taɓa zama mai horaswa da zai so ya ci wasa ta wannan hanyar ba. So nake na yi wasa da kyau. Ina son ƴan wasana su riƙa ci gaba, su riƙa taka leda sosai a filin wasa," in ji Hurzeler.

  6. Arsenal ta ƙara bai wa City tazara

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙwallo ɗaya tilo da Bukayo Saka ya zura a ragar Brighton ce ta wadatar, inda Arsenal ta haɗa makinta uku bayan tashi 0-1 a wasanta da Brighton a daren ranar Laraba.

    Wannan ya sa Arsenal ta ƙara wa Manchesty City rata a kan teburin Premier da maki 7, duk da dai City na da kwantan wasa ɗaya.

    Nottingham Forest, wadda ke fama da kanta ta yi nasarar riƙe Manchester City da ci 2-2 a filin wasa na Etihad.

    A sauran wasannin:

    • Aston Villa 1-4 Chelsea
    • Fulham 0-1 West Ham United
    • Newcastle United 2-1 Manchester United
    Ƙungiyoyi shida na saman teburin Premier
    Bayanan hoto, Ƙungiyoyi shida na saman teburin Premier
  7. An yanke wa maguire hukuncin gargaɗi na watanni 15

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Girka ta yanke wa ɗan wasan bayan Manchester United Harry Maguire hukuncin gargaɗi na tsawon watanni 15 sakamakon wani lamari da ya auku a tsibirin Mykonos a watan Agustan 2020.

    An yanke wa Maguire hukuncin ɗaurin watanni 21 da kwanaki 10 a gidan yari a shekarar 2020, bayan da aka same shi da laifin yunƙurin cin hanci da rashawa, da cin zarafin ma’aikatan gwamnati da kuma cin mutunci.

    Kashegari tawagar lauyoyin Maguire ta shigar da ƙara a kan hukuncin. Kuma bisa dokar Girka, ɗaukaka ƙarar ta soke hukuncin da aka yanke masa kuma za a sake shari'ar gaba ɗaya.

    An ɗage shari’ar ne sau huɗu tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kafin a sake fara shari’ar a Syros ranar Laraba.

    Shari’ar yanke cewa an samu Maguire da laifin cin zarafi, da yunƙurin hanawa a kama shi da kuma yunƙurin cin hanci.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa Maguire ya musanta aikata ba daidai ba kuma yana shirin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli.

  8. Liverpool za ta iya asarar Fam miliyan 120 idan ta rasa gurbin Champions League

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ya ce shi da abokan wasansa suna cikin jimami bayan da Wolves ta doke su da ci 2-1 a gasar Premier ranar Talata.

    Rashin nasarar da ta yi a Molineux ya bar Liverpool a matsayi na biyar, a halin da ake ciki zai iya ba ta damara samun gurbi a gasar zakarun Turai ta baɗi.

    Amma teburin gasar Premier ta bana a matse ya ke.

    Tawagar ta Anfield ta tserewa Chelsea da maki uku ne kacal wadda za ta kara da Aston Villa da ke matsayi na huɗu a wasan da za su fafata a ranar Laraba a filin wasan Villa park.

    "Idan ka na takawa Liverpool leda, kodayaushe kana iya samun kanka a wannan matsayi. Ya rage gare mu, tare da magoya bayanmu, mu yi yunƙurin samun sakamakon da muke buƙata don shiga gasar zakarun Turai." in ji Van Dijk

    Masana harkar hada hadar kuɗi a fannin wasanni sun bayyan cewa rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta kaka mai zuwa zai iya janyowa Liverpool asarar da ta kai fam miliyan 120.

  9. Tottenham na fuskantar barazanar faɗawa Championship - Tudor

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Tottenham Hotspur Igor Tudor ya soki ƴan wasansa bayan da ƙungiyarsa ta sha kashi a hannun Fulham da ci 2-1, yana mai nuni da cewa akwai manyan matsaloli da ƙungiyar.

    "Ba mu yi ƙoƙari ba, mun kasa yin komai," in ji shi. "Fulham sun fi mu kyau. Akwai matsaloli a nan, manyan matsaloli. Muna buƙatar mu kwantar da hankalinmu, mu amanna da abin da muke yi a lokacin atisaye, kuma mu kasance kan mu a haɗe.''

    Idan sakamakon sauran wasannin d a za a fafata da yammacin laraba su ka ƙi yi wa Tottenham kyau, ƙungiyar Igor Tudor za ta iya kammala ranar da tazarar maki ɗaya tsakaninta da ukun ƙarshe da za su iya faɗawa matakin gasar Championship tun ma kafin wasansu da da Crystal Palace a daren ranar Alhamis.

    A halin yanzu dai suna matsayi na 16 inda suke da maki 29 bayan wasanni 28 da aka buga.

    A daidai wannan lokaci a kakar da ta gabata, Spurs sun kasance a matsayi na 13 da maki 34.

  10. Rodrygo ba zai buga gasar cin kofin duniya ba saboda raunin ACL

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan gaba na Real Madrid da Brazil, Rodrygo, ya kira ta "daya daga cikin mafi munin ranaku a rayuwata" bayan da aka tabbatar da cewa ba zai sake taka leda a kakar wasan bana da kuma gasar cin kofin duniya ta 2026 ba saboda rauni a gwiwarsa.

    Rodrygo ya buga wasansa na ƙarshe a lokacin da ya shigo fili a minti na 55 a wasan da Madrid ta sha kashi a hannun Getafe a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

    Wannan dai shi ne wasansa na farko tun farkon watan Fabrairu.

    Wannan koma baya da Rodrygo ya samu ya zo ne a daidai lokacin da dan wasan gaban Real Kylian Mbappe shi ma yake fama da rauni a gwiwa.

    Ɗan wasan gaban na Faransa bai buga wasanni biyun da kungiyarsa ta buga ba saboda yana fama da rauni a gefen gwiwa na hagu tun karshen shekarar 2025.

  11. Dole United ta nemi ƴan wasan gefe - Carrick

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Michael Carrick ya ce Manchester United za ta iya neman siyan ɗan wasan gefe na hagu a wannan bazarar - duk da cewa ta shafe tsawon bazara uku a ƙarƙashin Ruben Amorim tana rabuwa da ƴan wasan gefenta.

    A bisa tarihi dai ƴan wasan gefe sun saba zama ginshiƙan tawagogin ƴan wasan Manchester United Manchester.

    Ana ɗaukar irin su George Best da Ryan Giggs da David Beckham da Cristiano Ronaldo a mantsayin manya ƴan wasan ƙungiyar.

    United ta fara kakar wasan bara da gogaggun ƴan wasan gefe guda biyar.

    A halin yanzu dai Amad shi ne kaɗai ɗan wasan gefe da Carrick ke da shi, kodayake ya yi amfani da mai tsaron baya Patrick Dorgu, wanda ya koma United daga Lecce a ƙarƙashin Amorim, a matsayin mai kai hari.

    United na cikin manyan ƙungiyoyin Premier da dama da ake alaƙanta su da ɗan wasan RB Leipzig dan ƙasar Ivory Coast Yan Diomande mai shekaru 19, wanda ake ganin farashinsa zai kai kusan fam miliyan 70 idan ya zaɓi ya tafi a bazara.

    An kuma ambaci Anthony Gordon na Newcastle, ko da yake ba a bayyana ko United na zawarcin ɗan wasan na Ingila ba.

  12. Athletico ta yi wajerod da Barcelona daga Copa Del Rey

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta yi barazanar farfaɗowa a wasanta da Atletico Madrid amma ta yi ƙasa a gwiwa yayin da ƙungiyar wadda ke riƙe da kambun gasar ta fice daga gasar Copa del Rey a matakin wasan kusa da na karshe.

    Duk da cewa Barcelona ta yi nasara a wasan da aka buga a filin wasan Spotify Camp Nou da ci 3-0 ta kasa kai labari sakamakon kashin da ta sha a wasan farko da ci 4-0.

    Marc Bernal ya ci wa Barcelona ƙwallo biyu yayin da Raphinha ya zura ɗaya daga bugun fenariti.

    Tawagar Diego Simeone ta riƙe wuta kuma yanzu za ta kara a wasan ƙarshen gasar da ƙungiyar da ta yi nasara tsakanin Real Sociedad da Athletic Club da za su fafata a ranar Laraba.

  13. An hana Adama Traore ɗaga ƙarfe a West Ham

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin West Ham Nuno Espirito Santo ya dakatar da Adama Traore daga ɗaga ƙarfe a dakin motsa jiki da ke filin atisayen kulob ɗin.

    Nuno ya bayyana ƙirar ɗan wasan gefen a matsayin "abin mamaki", amma ya gargaɗi Traore mai shekara 30 cewa ya riga ya yi nauyi dayawa.

    A baya ɗan ƙasar Sifaniyan ya yi ikirarin cewa ba ya ɗaga ƙarfe, amma abokin wasansa Crysencio Summerville ya wallafa wani bidiyo a shafinsa sada zumunta da ke nuna Traore yana danna ƙarfe mai nauyin 145kg a filin atisayen kungiyar da ke Rush Green a makon jiya.

    "Na gaya masa ya ɗan ƙauracewa ɗakin motsa jiki, yana ɗaya daga cikin abubuwan da nake ganin ya kamata ya gane. Nauyin da yake ɗauka ya isa haka.'' In ji Nuno

    Traore ya buga wa Fulham wasanni 20 a dukkan gasanni a kakar wasa ta bana kafin ya koma West Ham a watan Janairu kan yarjejeniyar da ta kai fam miliyan biyu.

  14. Flamengo ta sallami Filipe Luiz a matsayin kocinta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An kori tsohon ɗan wasan baya na Chelsea Filipe Luis a matsayin kocin Flamengo sa'o'i kaɗan bayan da ƙungiyar ta Brazil ta samu nasara da ci 8-0 a wasan kusa da na ƙarshe na Campeonato Carioca a ƙarshen mako.

    Luis, mai shekaru 40, ya jagoranci Flamengo ta lashe kofuna bakwai a cikin wasanni 100 da ya yi tun bayan maye gurbin tsohon kocin Brazil Tite a watan Satumban 2024.

    Flamengo ta yi rashin nasara a gasannin 2026, inda ta zama ta biyu a Supercopa do Brasil da Recopa Sudamericana a watan jiya.

    Amma, bayan kammala nasara da jimillar ci 11-0 a kan Madureira bayan nasarar da ta yi a daren ranar Litinin da ci 8-0 a wasansu na biyu, za ta samu damar lashe kofin Carioca karo na uku a jere inda za ta kara da Fluminense a wasan ƙarshe na ranar Lahadi mai zuwa.

    Sai dai Luis ba zai jagoranci ƙungiyar a wannan wasan ba bayan da ta fitar da wata ƴar gajeriyar sanarwa da ke bayyana korar shi.

    Daga cikin nasarorin da ya samu Luis, wanda ya lashe gasar Premier da Chelsea a ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho a 2015, ya jagoranci Flamengo zuwa lashe gasar Copa Libertadores a 2025.

    Flamengo ta kuma kai zagayen ƙungiyoyi 16 na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na bara, inda ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 4-2.

  15. Real Madrid ta sake yin tuntuɓe a La Liga

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta rasa damar rage tazarar da ke tsakaninta da Barcelona a saman teburin la Liga zuwa maki ɗaya bayan da ta sha kashi a hannu Getafe da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasan Bernabeau.

    Martin Satriano ne ya zura Getafe ƙwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci kiuma Madrid ta klasa farkewa har aka tashi wasa.

    Wanna sakamakon dai na nufin Madrid ta yi rashin nasara a gasar sau biyu ke nan ka jere bayan da ta sha kashi a hannun Osasuna da ci 2-1.

    Yanzu dai Kocin Madrid Alvaro Arbeloa ya yi rashin nasara sau huɗu cikin wasanni 12 da ya yi.

    Madrid za ta kara da Celta Vigo ranar Juma'a yayin da take ƙoƙarin kaucewa shan kashi na uku a jere a gasar.

  16. Ya kamata mu rage yawan katin da muke samu - Rosenior

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Chelsea Liam Rosenior ya koka kan yadda ƴanwasansa ke karɓar kati da kuma yanayin kwallayen da ake zura mata a raga a wasanninta na baya bayan nan.

    Kungiyar Rosenior ta sake samun wani jan kati a wasan da suka sha kashi a hannun Arsenal da ci 2-1 inda aka danna wa Pedro Neto katin gargadi biyu.

    Hakan na nufin Chelsea ta samu jan kati bakwai a gasar Premier bana kaɗai, tana kuma da guda tara a duk gasa a kakar wasan bana.Na tam

    "Ina tsammanin, a matsayin mu na kungiya, kuma da ni a matsayin jagora, dole ne mu dauki alhakin wasu abubuwan da muka yi a cikin wasa, musamman kan abubuwan da suka shafi ladabi a fagen wasa." in ji Rosenior bayan da suka sha kashi a hannun Arsenal.

    Ya ƙara da cewa "Abu ne da na yi tunanin mun magance. Mun yi wasanni 10 ba tare da jan kati ba, yanzu [mun samu] biyu a wasanni biyu kuma wannan matsala ce da ya kamata mu magance cikin gaggawa."

    Chelsea za ta buga wasanta na gaba a gasar Premier a ranar Laraba mai zuwa inda za ta fafata da Aston Villa a filin wasan Villa Park.

  17. Teburin gasar Premier bayan wasannin mako na 28

    Yadda teburin gasar Premier ya kasance bayan wasannin mako na 28.

    ...

    Asalin hoton, Premier League/FB

  18. Messi ya zura ƙwallo biyu a wasan Miami da Orlando a gasar MLS

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi ne ya zura ƙwallaye biyu a wasan da Inter Miami ta doke Orlando City da ci 4-2 a fafatawar da suka yi a Florida.

    Zakarun da ke riƙe da kofin, wadanda suka yi rashin nasara a wasansu na farko a kakar wasa ta bana da Los Angeles FC a watan da ya gabata, sun kusa sake shan kaye lokacin da Marco Pasalic da Martin Ojeda suka ci wa Orlando ƙwallo biyu cikin mintuna 25.

    Amma bayan da ɗan wasan tsakiya Mateo Silvetti ya jefa ƙwallo bayan an dawo hutun rabin lokaci ya bai wa Miami fatan cewa za su iya taɓuka abin kirki,

    Gwarzon ɗan wasan Argentina ya mai shekaru 38 ya zura ƙwallonsa ta farko a kakar wasa ta bana inda ya jefa ƙwallo a minti na 57

    Messi ya tabbatar da nasarar ƙungiyarsa a 90 jefa ƙwallonsa na biyu daga bugun tazara.

    Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau takwas a yanzu ya zura ƙwallaye 898 wa ƙungiyoyi da kuma ƙasarsa, ciki har da 79 a wasanni 90 da ya buga wa Miami.

    Nasarar ita ce ta farko da Miami ta yi a cikin ziyara tara zuwa Orlando, kuma yanzu za su fuskanci wasa a gidan DC United ranar Asabar.

  19. Arsenal ta ci gaba da riƙe wuta a saman teburin Premier

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta ci gaba da zama kan teburin gasar Premier a Ingila bayan ta lashe wasanta da Chelsea da ci 2-1.An dai ci duka ƙwallayen ne ta hanyar bugun ƙusurwa.

    Duk da cewa Arsenal ba ta buga ƙwallo mai ƙayatarwa ba a wasan, to amma nasarar da ƴanwasanta suka yi na zura ƙwallo biyu ta sanya ƙungiyar ta ci gaba da zama ɗare-ɗare kan teburi da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City wadda ke a matsayi na biyu.

    A yanzu Arsenal ta ci ƙwallaye 16 ke nan ta hanyar ko dai bugun tazara ko na ƙusurwa a wannan kaka, inda ta fi kowace ƙungiya ta wannan fanni a kakar.

    A wasan na ranar Lahadi, mai tsaron baya William Sliba ne ya jefa ƙwallon farko ta hanyar kara wa ƙwallon kai bayan bugun ƙusurwa da Bukayo Saka ya ɗauko.

    Sai dai gab da zuwa hutun rabin lokaci Chelsea ta rama ta hanyar bugun ƙusurwa, inda Piero Hincapié ya ci gida, ya kara wa ƙwallon kai ta faɗa ragar Arsenal.

    Can bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Jurrien Timber ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Chelsea bayan bugun kusurwa da Declan Rice ya ɗauko.