Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 28/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 28/02/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Trump ya ce an kashe jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa an kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    A cikin saƙon, Trump ya ce "wannan adalci ne ba ga al'ummar Iran kawai ba, har da Amurkawa, da kuma al'ummar ƙasashen duniya waɗanda Khamenei da ƴan korensa suka kashe ko suka azbtar.

    "Ya gaza zulle wa bayanan sirrinmu da kuma fasaharmu ta bibiya, tare da aiki kafaɗa da kafaɗa da Isra'ila, yanzu babu shi, ko sauran jagororin da ak kashe tare da shi.

    "Wannan ce babbar dama ga al'ummar Iran su sake karɓe iko da ƙasarsu.

    "Amma gagarumin luguden wuta na ɗauki ɗaiɗai zai ci gaba, ba tare da ƙaƙƙautawa ba a tsawon mako ko kuma har zuwa lokacin da ya kamata domin cimma manufarmu ta zaman lafiya a faɗin Gabas ta Tsakiya da duniya baki ɗaya."

  2. Ana tantama game da jagoran addinin Iran

    Bayan iƙirarin firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa "alamu na ƙara tabbatarwa" cewa jagoran addinin Iran "ya rasu", ana samun rahotanni masu karo da juna game da hakan.

    A tattaunawarsa da ƴan jarida, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi "amannar" cewa an kashe jagoran addini na Iran.

    Lokacin da aka tambaye shi ko yana da "tabbas" game da kisan na Khamenei, sai Trump ya ce "Ba na son na ce ina da tabbas har sai mun ga yadda abubuwa suke, amma na yi amannar haka".

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani babban jami'in gwamnatin Isra'ila na cewa an ga gawar jagoran addinin.

    Me Iran ta ce?

    Gabanin haka, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei ya faɗa a kafar yaɗa labarai ta ABC cewa Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei da shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian duk suna "cikin ƙoshin lafiya".

    Haka nan ma kamfanin dillancin labarai na ISNA, na Iran ya ambato jami'in hulɗa da jama'a na ofishin Khamenei na cewa "maƙiya sun koma yaƙi ta hanyar amfani da dabarun yaudara. Ya kamata mu yi taka-tsantsan kan haka".

    Abin da muka sani

    Sashen tantance gaskiyar labari na BBC ya samu hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka a yau wanda ya nuna cewa an illata wani ɓangare na ofishin Khamenei a babban birnin Iran.

    Ba a ji daga bakin jagoran addinin ba tsawon yau, kuma babu tabbacin inda yake, da kuma ko yana raye ko kuma a mace.

  3. Kwamitin tsaro na MDD ya kira taron gaggawa

    babban sakataren MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa yau a birnin New York na Amurka.

    Taron na zuwa ne bayan da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Antonio Guterres ya yi Allah wadai da matakin soji a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mista Gutterres ya ce ''matakin zai kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar duniya''.

    Ya kuma yi kiran gaggauta kawo ƙarshen yaƙin.

  4. Iran ba ta da hujjar kawo mana hari - Saudiyya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Saudiyya sun yi Allah wadai da babbar murya kan harin da Iran ta kai gabashin birnin Riyadh, wanda ta ce dalarun tsaron kasar sun samu nasarar kakkaɓowa.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ambato wata sanarwa da fadar Saudiyyar ta fitar, da ke cewa Iran ba ta da dalilin kai harin.

    Saudiyya ta ce ta yi mamaki da harin, duk kuwa da cewa Iran ta sani hukumomin Saudiyya ba za su bari a yi amfani da sararin samaniyar ƙasar wajen kai wa Iran hari ba.

    Ƙasar Saudiyyar ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace don kare ƙasarsu da al'ummarsu, ciki har da zaɓin kai harin ramuwa.

  5. Hayaƙi ya turnuƙe wani gini a Dubai

    hoto

    Hotuna da bidiyoyin da muke samu daga shaidu a Dubai sun ce haya ki ya turnuƙe a kusa ginin otal ɗin Fairmont The Palm da ke birnin.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce kasar ta kaddamar da jari Dubai.

    Sai dai ba su bayyana abin da Iran ke tai wa harin ba, amma dai akwai jami'an tsaron Amurka a ƙasar.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar daular larabawa ta ce ta kakkaɓo wasu makamai mas linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta harba ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato.

  6. 'Mutum 40 sun mutu bayan hari kan makarantar yanmatar Iran'

    Wani jami'i a Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA cewa mutum 40 ne harin Ira'ila ya kashe a wata makarantar furamaren ƴanmata da ke garin Minab a lardin Hormozgan na kudancin ƙasar.

    Gwamnan lardin, Mohammad Radmehr ya ce fiye da mutum 48 ne suka jikkata yayin da ake sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

    Kawo yanzu dai BBC ba ta ita tabbatar da sahihancin labarin ba - Ana hana manyan kafofin yaɗa labarai na duniya izinin shiga Iran, wani abu da ke taƙaita damarsu ta tattara labaran haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasar.

  7. Najeriya ta shawarci ƴanƙasarta mazauna Gabas ta Tsakiya

    Shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/X

    Gwamnatin Najeriya ta buƙaci yanƙasarta mazauna Iran da sauran ƙasashen yankin Gulf su zama masu kula da sanya idanu sosai, bayan da yaƙi ya ɓarke a yankin.

    Da safiyar yau ne Amurka da haɗin gwiwar Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare cikin Iran, yayin da ita ma Tehran ta mayar da martani da hanyar harba makamai masu linzami cikin Isra'ila da wasu sansanonin sojin Amurka a yankin Gulf.

    Cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar ta bai wa ƴan ƙasarta da ke zaune a ƙasashen yankin wasu shawarwarin kula da kai da suka haɗa da:

    • Kasancewa cikin shiri ta hanyar sanya idanu sosai kan abubuwan da ke faruwa.
    • Taƙaita zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci sosai.
    • Bin umarnin hukumomin ƙasashen da suke ciki.
    • Sanin halin da ake ciki ta hanyar bibiyar sahihan kafofin yaɗa labarai.
  8. Iran ta gargaɗi ƙasashen Gabas ta Tsakiya kan 'tallafa wa Amurka'

    Ministan wajen Iran

    Asalin hoton, EPA

    Iran ta ce za ta yi amfani da duka karfin sojinta wajen kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila.

    Cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya fitar ya ce ya yi waya da ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Qatar da Kuwait da Bahrain da Iraƙi, inda ya shaida musu cewa Iran za ta yi amfani da duka karfin sojinta wajen kare kanta.

    Araghchi ya kuma "tunasar da" ƙasashen game da "damarsu ta hana amfani da kayayyakinsu ko yankunansu ta hanyar da ba ta dace ba" yana nufin kada su bai wa Amurka ko Isra'ila damar amfani da su don ƙaddamar da hari cikin Iran.

  9. Muna sane da shirin Amurka da Isra'ila na kawo mana hari - Iran

    Iran ta ce dama tana sane da shirin Amurka da Isra'ila na kai mata hare-hare.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta ce duk ta kasar na sane da shirin ƙasashen amma ta shiga tattaunawar nukiliyar ƙasar.

    A ranar 26 ga watan Fabarirun da muke ciki ne Amurka da Iran suka yi tattaunawar karo na uku game da shirin Nukiliyar Iran.

    Sau biyar ƙasashen biyu na zaman tattaunawa kan batun shirin Iran ba tare da cimma matsaya ba.

  10. Bidiyon yadda Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke Bahrain

    Bidiyoyin harin ramuwar gayyar Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da ɓulla.

    Akwai sansanonin sojin amurka masu yawa a yankin gabas ta Tsakiya, da za a iya kai wa hari.

    Bahrain na ɗaya daga ƙasashen yankin Gulf da dama da Iran ta kai wa hari bayan hare-haren amurka da Isra'ila a ƙasarta.

    Iran ta kai hari babban sansanin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar ta Bahrain.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. Iran na kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya

    ..

    Asalin hoton, ..

    Rundunar sojin Qatar ta tabbatar da hare-haren Iran a ƙasar - inda Amurka ke da sansanin sojin sama na Al-Udeid, mafi girma da take da shi a Gabas ta tsakiya.

    Sai dai ƙasar ta ce ta samu nasarar kakkaɓo hare-haren.

    Can ma a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa hukumomin ƙasar sun tabbatar da mutuwar mutum guda bayan kakkaɓo harin Iran a ƙasar.

    Haka ma hukumomin Bahrain sun tabbatar da hari kan sansanon sojin ruwan Amurka da ke ƙasar, kodayake ba ta alaƙanta harin da kowace ƙasa ba.

    Ita ma ƙasar Kuwait ta ce ta kakkaɓo harin Iran da ya tunkari sansanin sojin Amurka da ke ƙasar.

  12. Netanyahu: Ba za mu bari Iran ta mallaki nukiliya ba

    Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce bai kamata a bar gwamnatin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar bayan harin haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila kan Iran, Netanyahu ya gode wa Amurka game da harin.

    ''Cikin shekara 47 gwamnatin Ayatollah na ambata mutuwa ga Isra'ila da mutuwa ga Amurka'', in ji shi.

    ''Gwamnatin Iran ta kashe ƴan Isra'ila da Amurkawa masu yawa, don haka bai kamata a bar wannan gwamnati ta malaki makamin nukiliya ba'', in Netanyahu.

    Yana mai cewa harin da suka kai zai bai wa Iraniyawa damar ƙwace gwamnatinsu da hannunsu.

  13. Trump ya buƙaci Iraniyawa su ƙwace gwamnatin ƙasar

    ..

    Asalin hoton, ..

    Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci Iraniyawa su yi amfani da manyan hare-haren Amurka da Isra'ola wajen kifar da gwamnatin ƙasar.

    Cikin wani jawabi da ya yi ta bidiyo, Mista Trump ya ce ''Idan muka gama namu, ku kuma ku ƙwace gwamnatin, taku ce, ina ganin wannan ce damar da kuka samu ta yin hakan''.

    Ya kuma faɗa wa dakarun sojin Iran cewa za a ba su ''kariya'' idan suka amince su ajiya makamansu, ko kuma su ''fuskanci mutuwa''.

    A farkon watan Janairu ne Trump ya yi barazanar kai harin bom kan Iran saboda yadda jami'anm tsaron ƙasdar ke far wa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta ce an kashe mutum 6,480.

  14. Iran ta ƙaddamar da hara-haren ramuwar gayya

    hari

    Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya game da hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila, IDF ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin Isra'ila, amma tana ƙoƙarin ganin ta kakkaɓo su.

    Haka ma Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasaer, kodayake ta ce an kakkaɓo hare-haren.

    Ita ma ƙasar Bahrain ta tabbatar da kai hari kan sansanonin sojin ruwan Amurka da ke ƙasar, kodayake ba ta alaƙanta harin da kowace ƙasa ba.

  15. Mun gaji da batun yarjejeniya - Trump

    Trump

    Asalin hoton, ..

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta gaji da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran.

    Cikin wani bidiyon minti takwas da ya fitar a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka ya tabbatar da hannun AMurka a harin Iran.

    Ya tabbatar da cewa Amurka ta ƙaddamar da ''babban faɗa'' da Iran.

    ya ƙara da cewa ''Za mu wargaza makamanta masu linzami tare da lalata kamfanin ƙera makamanta da ke ƙarƙashin ƙasa...''

  16. Biranen Iran biyar da hare-haren suka faɗa

    Kamfanin dillancin labaran Iran na Fars ya bayar da rahoton birane biyar da aka samu faɗawar hare-hare a cikinsu.

    Biranen sun haɗa da Isfahan da Qom da Karaj da Kermanshah da kuma babban birnin ƙasar Tehran

    biranen Iran
  17. Hotunan yadda yahaƙi ke tashi a Iran bayan harin Isra'ila da Amurka

    Hoto

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Da safiyar yau Asabar en aka ji ƙarar abubuwan fashewa a birnin Tehran
    Iran
    Bayanan hoto, Tuni Iran ta rufe sararin samaniyarta
    Hoto

    Asalin hoton, Reuters

  18. Isra'ila da Iran sun rufe sararin samaniyarsu

    Isra'ila ta sanar da rufe sararin samniyartya bayan harin da haɗa gwiwa da Amurka suka kai wa Iran da safiyar yau Asabar, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

    Can a Iran kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da dakarun juyin juya halin ƙasar, ya bayar da rahoton cewar Iran ta rufe sararin samaniyarta.

    Ana sa Iran za ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan Isr'ila da sansanonin sojin AMurka da ke gabas ta tsakiya.

  19. Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an ji ƙarar manyan abubuwan fashewar uku a birnin Tehran.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ce ya samu rahatonnin faɗawa makamai masu linzami a babban birnin Iran.

    Kafofin yaɗa labaran Amurka da na Isra'ila sun ce Amurka da Isra'ila ne suka haɗa gwiwa wajen ƙaddamar da harin.

    Dama dai Amurka ta jima tana barazanar far wa Iran da yaƙi saboda shirinta na nukiliya.

    A makon da ya gabata Shugaba Trump na Amurka ya bai wa ƙasar wa'adin kwana 10, don ta cimma yarjejeniya ko ta ɗauki matakin soji a kanta.