Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na ranar 17/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin na yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

  2. Trump ya gargaɗi jiragen Nato kan bi ta mashigar Hormuz

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake caccakar ƙungiyar tsaro ta NATO, inda ya gargaɗe ta da ta nisanci mashigin Hormuz bayan buɗe ta.

    Faransa da Birtaniya sun ce a yau Juma’a sun jagoranci wata rundunar ƙasashe da dama, domin tabbatar da ƴancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan.

    Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya yi watsi da duk wani tayin taimako, yana mai jaddada cewa kada jiragen ƙasashen ƙungiyar su kusanci mashigar.

    A baya ma ya sha sukar ƙasashen da ke cikin kungiyar ta NATO, kan abin da ya kira ƙin mara wa Amurka baya a yaƙin da ta yi da Iran.

  3. Ƴanbindiga sun sace ɗaliban da suka tafi rubuta JAMB a Benue

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴanbindiga a jihar Benue sun sace wasu ɗalibai da ke kan hanyarsu ta zuwa jarrabawar shiga jami'a ta JAMB a ƙasar, wani abu da ke nuna ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar.

    Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da sace fasinjoji 14 ciki har da ɗaliban.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ƴansandan jihar Ifeanyi Emenari, ya ce an tura jami'an tsaro yankin da abin ya faru domin ceto mutanen.

    Harin na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara rubuta jarrabawar shiga jami'a ranar Alhamis a ƙasar.

    An sace ɗaliban ne lokacin da ƴanbindigar suka tare motar da suke ciki a kan hanyarsu tsakanin Makurɗi zuwa Otukpo.

    Shaidu sun ce ƴanbindigar sun tare motar da ɗaliban ke ciki da misalin ƙarfe 8 na dare, inda suka ƙwace musu kayayyakinsu, daga baya kuma suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji.

  4. Wakilan Amurka za su koma Pakistan don ci gaba da tattaunawa da Iran

    yansanda

    Asalin hoton, Pool/Getty Images

    Kafar ya da labaran CBS, abokiyar hulɗar BBC a Amurka, ta bayar da rahoton cewa, jamai'an Amurka ka iya komawa Pakistan domin faɗaɗa tattauanwa da Iran nan da ƴan kwanaki masu zuwa.

    Yayin da ta ambato wasu ''majiyoyi masu alaƙa da tattaunawar'', CBS ta ce gwmanatin Trump na duba yiwuwar aika manyan jami'anta zuwa Pakista don sabunta tattauanwa da Iran.

    Akwai yiwuwar a koma tattaunawar a ranar Litinin mai zuwa, a cewar kafar yaɗa labaran

    A makon da ya gabata ne birnin Islamabad na Pakistan ya karɓi baƙuncin tattaunawar cimma yajejeniyar tsagaita wutar yaƙin Iran da Amurka, kodayake ba ta samu nasara ba.

    Awaki rahotonin da ke cewa babban hafan sojin Pakistan ya gana da jami'an Iran abirnin Tehran ranar Alhamis, a wani yunƙuri na tsawaita wa'adin tsagaita wutar wucin gadi.

  5. Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 da ɗage fara aiwatar da na 2025

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban kasa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce cikin wannan adadi za a ware naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashi.

    Kasafin ya kuma ware naira tiriliyan 15.4 domin ayyukan gudanarwar yau da kullum, yayin da aka ware naira tiriliyan 32.2 don gudanar manyan ayyuka.

    “Yayin da kusan rabin kasafin zai tafi a manyan ayyuka, hakan na nuna burin gwamnati na ci gaba da ayyukan daidaita tattalin arziki ta hanyar bunƙasa ɓangaren tsaro da samar da ayyukan more rayuwa da ci gaban kowane fanni'', in ji sanarwar.

    Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci hukumomin gwamnati su tabbatar da bin ƙa'ida da yin komai a bayyane da amfani da kuɗaɗen da aka ware musu ta hanyoyin da suka dace.

    Haka kuma sanarwar ta ce shugaban na Najeriya ya ɗage fara aiwatar kasafin kuɗin ƙasar na 2025 zuwa 30 ga watan Yunin 2026.

    Tun da farko an tsara fara aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 ɗin a ranar 31 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

  6. Manyan kamfanonin fito na mayar da martani kan buɗe mashigar Hormuz

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan kamfanonin fito na duniya na ci gaba da martani haɗe ga gargaɗi kan sake buɗe mashigar Hormuz da Iran ta sanar.

    Kamfanin fito no Denmark, Maersk, ya ce yana nazarin sanarwar da Iran ta fitar game da buɗe mashigar, kuma jiragenta za su bi ta mashigar ne bayan yin nazarin kasadar da ke tattara da yin hakan.

    Shi ma takwaransa na Jamus, Hapag-Lloyd ya ce kwamitinsa mai kula da matsaloli na wata ganawa, amma yana ƙoƙarin ganin jiragensa sun bi ta mashigar.

    Rahotonnin na cewa za a duba yiwuwar la'akari da biyan kuɗi domin wucewar man fetur da iskar gas ta mashigar.

  7. Sai da izinin rundunar IRGC za a wuce ta mashigar Hormuz - Rahotonni

    Iran

    Asalin hoton, Telewebion/IRINN

    Gidan talbijin na Iran ya ambato wani ''babban jami'in sojin ƙasar'' na cewa jiragen ruwan da za su wuce ta mashigar Hormuz za su yi hakan ne kawai ta ''hanyoyin da ka tsara'' da kuma amincewar rundunar juyin juya halin ƙasar.

    Babban jami'in sojin ya ce jami'an tsaron Iran ne za su tsara hanyoyin da jiragen ruwan za su bi domin wucewa.

    Tun da farko ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ne ya bayyana buɗe mashigar ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    A cewar gidan talbijin na Iran ɗin, buɗe mashigar ya keɓanta ne kawai ga jiragen ƴan kasuwa, ban da na soji.

  8. Yaƙin Sudan: Akan tilasta mana cin abincin dabbobi

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  9. Atiku ya kai wa Kwankwaso ziyara a gidansa na Abuja

    Atiku da Kwankwaso

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan/Facebook

    Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya kai wa jagoran Kwankwasiyyar,Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ziyara a gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja.

    Ziyarar na zuwa ne kwanaki bayan babban taron jama'iyyar haɗaka ta ADC, wadda duka ƴansiyasar biyu ke cikinta.

    Atiku da kwankwaso

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan

    Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da jagororin siyasar biyu suka tattauna ba, amma ana ganin ba ta rasa nasaba da batun siyasa.

    Atiku da Kwankwaso

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB

  10. Amurka ba za ta biya Iran kuɗi kan miƙa sinadaran da ta inganta ba - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka ba za ta biya Iran ko wani irin kuɗi ba kan miƙa sinadaran uranium ɗin da ta inganta, yana mai jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma ba za ta ƙunshi biyan kuɗi ba.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Amurka za ta karɓi duk wani “tarkacen nukiliya” da jiragen yaƙinta na B-2 suka samar, tare da jaddada cewa babu wani kuɗi da za ta biya.

    Ya kuma ƙara da cewa yarjejeniyar ba ta shafi ƙasar Lebanon ko kaɗan, amma Amurka za ta yi aiki da ita domin magance batun ƙungiyar Hezbollah. Haka kuma ya ce Isra’ila ba za ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon ba, domin Amurka ta hana hakan faruwa.

    Wannan na zuwa ne ‘yan mintoci bayan Trump ya gode wa Iran bisa buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya domin zirga-zirgar jiragen ruwa.

  11. Trump ya gode wa Iran kan buɗe mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gode wa Iran bayan sanarwar da ta yi na buɗe mashigar ga dukkan jirage har zuwa ƙarshen tsagaita wuta.

    Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce: “Iran ta sanar da cewa ta buɗe mashigar Hormuz ga dukkanin jirage. Nagode!”

    Wannan na zuwa ne bayan Iran ta ce za ta bar jirage su riƙa wucewa cikin sauƙi har zuwa ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma a yankin.

    Matakin buɗe mashigar Hormuz na daga cikin muhimman abubuwan da ake ganin zai rage tashin hankali a yankin, tare da taimakawa harkokin kasuwanci na duniya, musamman ma a fannin man fetur.

  12. Iran ta buɗe mashigar Hormuz ga dukkanin jirage

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta sanar da buɗe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen kasuwanci domin su rika wucewa har zuwa ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma.

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya ce: “A cikin tsarin tsagaita wuta a Lebanon, an ayyana cewa dukkan jiragen kasuwanci za su rika wucewa cikin ‘yanci ta mashigar Hormuz har zuwa ƙarshen wannan tsagaita wuta.”

    Ya ƙara da cewa wannan zirga-zirga za ta gudana ne ta wata hanya da aka tsara tun da farko, wadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Iran ta sanar.

    A wani ɓangaren kuma, kafar labarai ta Axios ta ruwaito jami’an Amurka na cewa ana tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan wani shiri mai shafuka uku domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Rahoton ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa a kai shi ne yiwuwar Iran ta miƙa sinadarin uranium ɗinta , a musayar Amurka ta saki dala biliyan 20 na kuɗaɗen Iran da aka daskarar.

  13. 'Iran ba za ta amince da tsagaita wuta na wucin gadi ba'

    Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta amince da duk wani tsagaita wuta na wucin gadi ba, yana mai cewa abin da Iran ke nema shi ne kawo ƙarshen yaƙi gaba ɗaya a duk faɗin yankin.

    Khatibzadeh ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen taron Antalya Diplomacy Forum, inda ya ce duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta dole ne ta shafi yankuna daga Lebanon har zuwa Tekun maliya.

    A cewarsa, “ba za mu amince da tsagaita wuta na ɗan lokaci ba,” yana mai ƙara da cewa tashin hankalin dole ne ya tsaya gaba ɗaya har abada.

    Dangane da mashigar Hormuz, ya ce wannan hanya ta kasance a buɗe a koda yaushe.

    Haka kuma, ya zargi Amurka da Isra’ila da haddasa rashin zaman lafiya a yankin, yana mai cewa matakan da suke ɗauka na da mummunan tasiri ga harkokin kasuwanci na duniya da tattalin arziki.

  14. Me sabuwar dokar zaɓen Najeriya ta ce kan yin takara da takardun bogi?

    ..

    Asalin hoton, @aonanuga1956/X

    A Najeriya masana na ci gaba da fashin baƙi da bayyana damuwa kan yadda ƴan majalisar ƙasar suka amince da dokokin zaɓen 2026 da aka yi wa gyaran fuska ba tare da cikakken nazari kan wasu abubuwan da dokar ta ƙunsa ba.

    Ɗaya daga cikin dokokin da ke ta da ƙura ita ce wadda ta hana a ƙwace wa ƴan takarar da suka ci zaɓe da takardar bogi kujerarsu, sannan ta tanadi hukunci ga wanda ya kai su ƙara bai yi nasara ba.

    Dokar ta kuma sanya tarar naira miliyan 10 ga mutumin da ya kai ƙara ba tare da samun nasara a kan mai takardun bogin ba.

    A ranar 18 ga watan Fabrairun 2026 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar bayan majalisun dokokin ƙasar sun amince da gyaran dokar a ranar Talata bayan kwashe watanni ana mahawara kan sauye-sauye

  15. Abin da muka sani game da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Lebanon da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta na kwanaki 10 da zai fara aiki da karfe 5:00 agogon ƙasar.

    Sai dai bai yi wani ƙarin bayani game da ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Labanon ba, wadda Isra'ila ke ta musayar wuta da ita cikin makonni shida da suka wuce.

    Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social daga bisani, ya buƙaci ƙungiyar ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, inda ya ce, "Ina fatan Hezbollah za su yi biyayya a wannan lokaci mai muhimmanci."

    Bayan sanarwar, shugaban na Amurka ya kuma gayyaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Lebanon Joseph Aoun zuwa fadar White House domin ci gaba da tattaunawa.

  16. Iran ta yi maraba da tsagaita wutar Lebanon

    Ƙasar Iran ta ti maraba da tsagaita wuta a Lebanon, inda ta bayyana ta da nasarar diflomasiyya da kuma "kin miƙa wuya ga zalunci na Hezbollah".

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta bakin mai magana da yawunta, Esmail Baqael ta ce Tehran ta kalli tattaunawar a matsayin wani ɓangare na fahimtar juna da Amurka da aka cimma ta hanyar Pakistan.

    Ya ƙara da cewa Iran a koyaushe tana nanata buƙatar samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Esmail ya kuma yaba wa ƙokarin Hezbollah da kakakin majalisar dokokin Iran, Mohamed Baqer Qalibaf inda yake cewa fadi a saƙon da aka rubuta da Larabci a X cewa cimma tsagaita wutar ya faru ne sakamakon dakewar ƙungiyar ta Hezbollah.

  17. Harin Isra'ila ya kashe mutum 13 a Lebanon gabanin aiwatar da tsagaita wuta

    Dakarun Isra'ila sun kai farmaki a birnin Tyre na ƙasa lebanon a daren da ya gabata, inda suka kashe mutum 13 tare da jikkata 55 gabanin fara aiwatar da tsagaita wuta, kamar yadda kafar watsa labaran National News Agency ta rawaito.

    Da sanyin safiyar ranar Juma'a tawagar da ke aikin ceto na neman mutum 15 a ƙarkashin ɓuraguzan gini.

    Harin ya faru ne jim kaɗan kafin fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a tsakiyar dare, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP wanda ya rawaito jami'an gwamnati.

  18. Starmer ya ce zai yi duk abin da zai iya don ganin an bude Hormuz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Birtaniya, Keir Starmer ya isa Fadar gwamnatin Faransa ta Elysee Palace a birnin Paris, inda tun kafin haɗuwarsa da shugaba Emmanuel Macron, ya tsaya kai da fata cewa "zan yi duk abin da zan iya wajen rage radaɗin tasirin yaƙin Iran a kan al'umma da kuma buɗe mashigar Hormuz".

    Da yake magana da manema labarai, Stermer ya " Abu ne mai matuƙar amfani cewa za mu gina ƙawancen ƙasashe da ke son wanzuwar tsagaita wuta zuwa ta dundundun, sannan ya kamata a samu yarjejeniya sannan kuma a buɗe mashigar Hormuz."

    "Duka waɗannan suna cikin muradanmu ne saboda abin da ke faruwa a yaƙin Iran na shafar tattalin arziƙin ƙasashenmu. Shi ya sa ƙasashen ke haɗa kansu," in ji Stermer.

    Stermer da Macron a yammacin ranar Juma'ar nan na jan ragamar wani shiri tabbatar da buɗe mashigar Hormuz.

  19. Hezbollah ta ce a shirye take ta mayar da martani idan Isra'ila ta saɓa tsagaita wuta

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce a shirye take ta mayar da martani da zarar Isra'ila ta karya ƙa'idojin tsagaita wutar da ta fara aiki.

    A wani saƙon da ta wallafa a shafin Telegram, ƙungiyar ta Hezbollah ta ce "dole ne tsagaita wutar ta kunshi dukkannin sassan Lebanon ba wani ɓangare guda ba," inda kuma ta ƙara da cewa ta kai hare-hare 2,184 kan Isra'ila tsakanin ranar 2 ga watan Maris zuwa 16 ga Afirlun 2026.

    Ba a shigar da ƙungiyar ta Hezbollah cikin zaman tattauna yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 10.

    Firaiminista Benjamin Netanyahu ya tsaya kai da fata cewa dakarun Isra'ila za su ci gaba da kasancewa a wasu wurare a Lebanon a tsawon kwanakin tsagaita wutar.

  20. 'Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto'

    ..

    Asalin hoton, Ahmed/Facebook

    Wani rahoto da hukumar ƙididdigar jihar Sokoto ta fitar ya nuna cewa yanzu haka girman talaucin ya faɗo ƙasa warwas daga kaso 91 zuwa 41.

    Rahoton ya alƙanta cigaban da aka samu da irin ƙokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta rayuwar al'ummar karkara, inda a shekarar 2026 gwamnatin ta ware kaso 70 na kasafin kuɗinta ga fannin samar da kayan more rayuwa.

    Rahoton ya alaƙantatalauci da matsalar tsaro, inda al'amarin ya fi ƙamari a wasu ƙananan hukumomi kamar Tangaza da Binji wadanda ke fama da matsalar tsaro.

    A 2022 dai rahotanni sun nuna girman talauci a tsakanin al'ummar jihar ta Sokoto, inda ya kai kaso 91, abin da ya sanya jihar ta Sokoto a jerin jihohin da suke kan gaba a fannin talauci.