Mun duƙufa wajen sake ƙere makamai cikin hanzari a lokacin tagaita wuta- Iran
Kamfanonin dillancin labaran Iran masu alaƙa rundunonin soji da hukumomin tsaron ƙasar sun wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda ake ci gaba da ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a ƙasar da abubuwan harba makaman.
A cikin bidiyon an ga kwamadan IRGC mai kula da dakarun saman ƙasar, Majid Mousavi na ziyartar ɗaya daga cikin cibiyoyin - wanda ke ƙarƙashin ƙasa.
Baya ga bidiyon kamfanonin labaran sun kuma wallafa wani saƙo daga Majid Mousavi da ke cewa ''saɓanin Iran maƙiya ba su iya sake ƙera makamai a lokacin tsagaita wuta''
''A lokacin tsagaita wuta yawan ƙera makamanmu masu linzami da jirage marasa matuƙa ya ma fi sauri a kan yadda muke ƙerawa kafin fara yaƙin. Mun sani maƙiya ba za su iya ƙera wa kansu makamai ba...''.
''Sun yi asarar wannan lokaci, sun kuma yi rashin nasara a yaƙin, sun gaza a Hormuz, sun gaza a Lebanon sannan kuma a duka yankin ma gaba ɗaya'', in ji shi.