Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 24/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Shugaban Kenya na shan suka saboda ya ce ƴan Najeriya ba su iya turanci ba

    Shugaban Kenya William Ruto na shan suka a shafukan sada zumunta bayan wasu kalamai da ya yi na shaguɓe kan yadda ƴan Najeriya ke turanci. Ya ce idan ƴan Najeriya na turanci sai mutum ya nemi tafinta kafin ya gane abin da suke cewa.

    Yayin da yake yi wa ƴan Kenya mazauna Italiya jawabi a ranar Litini, Ruto ya ce: "Idan kana sauraren yadda ƴan Najeriya ke magana, ba za ka gane me su ke cewa ba - sai ka nemi wanda zai fassara maka," inda ya bugi ƙirjin cewa ƴan Kenya na daga cikin mutanen da suka fi iya magana turanci a duniya.

    Kalaman nasa na shan suka daga ƴan Najeriya da wasu ƴan Afrika da suka zargi shugaban Kenyan da cin fuskar ƙasar da take a Afrika.

  2. Ƙasashen Afirka za su fuskanci matsalar bashi

    Wani kamfanin bincike da nazari kan al'amuran da suka shafi kuɗaɗe da kimanta ƙarfin tattalin arziƙi na ƙasashen duniya mai suna S&P Global Ratings, ya yi gargaɗi cewa yawan bashin da ake bin ƙasashen Afirka na iya ta'azzara, idan har yakin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran ya tsawaita.

    Kamfanin ya ce bashin da ƙasashen na Afirka za su buƙata zai ƙaru ne matuka, a sakamakon tasirin yakin.

  3. Ghana ta koka da nuna ƙyamar mutanensu da ake a Afirka ta Kudu

    Gwamnatin Ghana ta ce mahukuntan Afirka ta Kudu sun fara gudanar da bincike kan wasu hare-haren nuna kyama da ake kai wa ƴan ƙasar mazauna Afirka ta Kudu.

    Hotunan bidiyo da ke nuna ana cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun karaɗe shafukan sada zumunta na Intanet a ƴan kwanakin nan.

    Hare-haren ƙyamar baƙi wani lamari ne mai sarƙaƙiya, wanda matsalolin tattalin arziƙi da labaran ƙarya da rashin fahimtar tarihi ke haifarwa.

    Ana dai samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali kan nuna ƙyama ga waɗanda ba ƴan asalin Afrika ta Kudu ba musamman a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙasar.

  4. Birtaniya ta ce ƴan China na sayar da bayanan sirrin jama'a

    Wani shirin tattara bayanai na lafiya na Birtaniya ya ɗora alhaki a kan masu bincike 'yan China marasa taka-tsantsan, kan yadda ake sayar da bayanan sirri na wajen mutum rabin miliyan da suka bayar da bayanansu bisa radin kansu.

    Ana dai sayar da bayanan ne a yanzu a wani shafin kasuwanci na intanet na China.

    Wata ƙungiyar agaji wadda ke gudanar da shirin tattara bayanan na Birtaniya ta gabatar da kanta ga hukumar da ke sa ido wajen kare bayanai ta Birtaniya.

    Shirin dai yana amfani da bayanan lafiya, na dubban mutane da na ƙwayoyin halittarsu na DNA, wajen inganta hanyoyin gano wasu cutuka masu tsanani da kuma magance su.

    Masu bincike a faɗin duniya na iya samun bayanan, amma bisa sharaɗi mai tsanani na tabbatar da kare sirri.

  5. Trump ya bayyana India da tambaɗaɗɗiyar ƙasa

    Gwamnatin India ta mayar da martani kan wasu kalamai da Shugaba Trump ya sake yaɗawa a shafin sada zumunta, kalaman da ke bayyana India a matsayin wata tambaɗaɗɗiyar ƙasa.

    Hukumomin Indiyar sun ce, kalaman ba su dace ba sam-sam kuma muzanci ne gare su.

    Ma'aikatar harkokin waje ta India ta ce kalaman ko alama ba su nuna irin ainahin alaƙar da ke tsakanin India da Amurka ba.

    Shugaban na Amurka ya yaɗa takardar bayanan wani shiri ne na siyasa wanda Micheal Savage ya gabatar, inda Savage din ya yi ƙorafi da cewa - duk jaririn da aka haifa a Amurka, nan take kai tsaye yake zama ɗan ƙasa, kuma wanda aka haifa ɗin nan sai ya shigo da gaba ɗayan 'yan uwansa daga China ko India ko kuma wata lalatacciyar ƙasa a duniya.

  6. BBC ta gano gidan da Jeffrey Epstein ke ajiye matan da yake lalata da su

    BBC ta bankado shedar da ke nuna cewa matan da Jeffrey Epstein, mutumin nan da aka kama da laifin lalata da ƙananan yara, ya riƙa ajiye su a gidaje daban-daban a birnin London, bayan da 'yansanda suka yanke shawara cewa ba za su bincike shi ba.

    Wakiliyar BBC ta ce, bincike a takardun da ma'aikatar sharia ta Amurka ta fitar, mun gano cewa yana biyan haya a aƙalla gidaje huɗu a London inda yake ajiye mata ɗaya daga cikin matan Virginia Giuffre.

    Ya kuma faɗa wa hukumar 'yansandan London a 2015 cewa - ta kasance wadda masu safarar mutane na ƙasa da ƙasa don lalata, wadda take da alaƙa da London, ta ci zarafi.

    A lokacin hukumar 'yansandan London din ba ta bude wani cikakken bincike ba kan lamarin, da cewa ba ita ce hukumar da ya kamata ta yi bincike ba.

    A yanzu ta ce, an shigar da ita tare da wasu hukumomin tsaron masu alaƙa ciki har da na Amurka, domin samun ƙarin bayanai don tabbatar da musayar bayanai a tsakaninsu.

  7. Amurka ta kama sojan da ya shiga cacar $400,000 kan cire Maduro

    Ma'aikatar sharia ta Amurka ta ce an kama wani sojin musamman na ƙasar wanda ake zargin ya samu sama da dala dubu 400, ta hanyar caca kan batun cire shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

    Wakilin BBC ya ce maiakatar sharia ta gano sojan a matsayin Gannon Ken Van Dyke, wanda ta ce yana daga cikin wadanda suka tsara da aiwatar dakama Maduro a watan Janairu.

    'Yan sa'o'i kafin Shugaba Trump ya sanar da kama Nicolas Maduro, ana ganin sojan, Gannon Ken Van Dyke ya sanya caca - kan ko za a cire Maduro daga mulki, da kuma ko Amurka za ta mamayi Venezuela.

    Nan da nan wannan caca ta canke ta janyo aka fara bincike. Sojan na fuskantar tuhume-tuhume da dama, ciki har da satar jin bayanai, da samun kudin da hanyar da ba ta halal ba.

    Idan aka same shi da laifi zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara har 50

  8. Trump ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar Lebanon

    Shugaba Trump ya ce za a tsawaita yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta Lebanon inda Isra'ila ke yaƙi da ƙungiyar Hezbolla da Iran ke mara wa baya da ƙarin mako uku.

    Wa'adin wadda ake kai yanzu zai ƙare ne a ranar lahadi.

    Trump ya sanar da ƙara wa'adin ne bayan wata ganawa ta biyu da manyan jami'an Lebanon da Isra'ila a Washington.

    Hezbollah ta yi suka ga tatattaunawar, yayin da Israila ta ci gaba da mamaye wasu sassan kudancin Lebanon.

  9. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Juma'a. Da fatan za mu samu albarkacin da ke cikin wannan rana. Allah ya sa hakan.

    Kamar kullum yau ma mun sake dawo muku da shafin BBC Hausa na kai tsaye inda muke kawo muku labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.