Yadda aka tono kabarin yara domin gwaji a Kenya
Yanzu haka hukumomi a yammacin Kenya sun ce an tono gawarwaki talatin da biyu da suka haɗa da ƙananan yara daga wani kabari da ke gundumar Kericho.
A baya dai an ruwaito cewa adadin gawarwakin kusan rabin hakan ne. Tono gawarwakin ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu, wanda ya sa ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike.
Yanzu haka dai an kai dukkan gawarwakin asibiti domin a yi musu gwaje-gwaje don sanin ko su waye, da kuma musabbabin mutuwarsu.
Binciken dai ya haifar da damuwa ga jama'ar ƙasar, da ya sa su tuna wani lamari makamancin wannan da ya faru a baya na Shakahola, ɗaya daga cikin ifta'ili mafi muni da ke da alaƙa da ƙungiyoyin asiri a Kenya, inda aka gano ɗaruruwan gawawwakin da aka binne a wani daji.

















