Haaland ya ci Arsenal karo na huɗu a jere a Premier League, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland ya zama ɗan wasa na biyu da ya ci Arsenal a wasa huɗu a jere a Premier League, bayan Diogo Jota a Liverpool tsakanin Satumbar 2022 zuwa Maris ɗin 2022.
Manchester City ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Arsenal ya koma saura uku, bayan da ta yi nasara 2-1 a wasan mako na 33 a Premier League a Etihad ranar lahadi.
Cherki ne ya fara ci wa City ƙwallo a minti na 16 da take leda, amma minti biyu tsakani Gunners ta farke ta hannun Havert, sakamkon kuskuren da golan City, Gianluigi Donnarumma ya yi.
Daga baya ne Haalnda ya ci wa City ƙwallon da take bukata da ya rage tazarar maki tsakaninsu.
Wannan nasarar na nufin ƙungiyar Etihad mai kwantan wasa za ta koma kan teburi da zarar ta ci Burnley a tsakiyar mako musammam da zura ƙwallo biyu a raga.
Wasannin da suke gaban Arsenal:
- Za ta karɓi bakuncin Newcastle
- Za ta buga da Fulham a Emirates
- Za ta je West Ham United
- Za ta kara da Burnley a gida
- Za ta kare wasa a gidan Crystal Palace
Wasannin da suka rage wa City:
- Za ta je Burnley
- Za kuma ta je gidan Everton
- Za ka karɓi bakuncin Bournemouth
- Za ka kara da Crystal Palace a gida
- Za ta fafata da Aston Villa a Etihad








