Amurka ta ce tana yunƙurin wargaza cibiyar makamai masu linzami na Iran
Fadar White House ta ce sojojin Amurka na shirin wargaza cibiyar sarrafa makamai masu linzami na Iran, a rana ta goma sha daya na yakin.
Mai magana da yawun fadar gwamnatin Karoline Leavitt ta ce jiragen saman kasar samfurin b-2 masu dogon zango sun yi amfani da bama-bamai kan cibiyoyin da aka binne a karkashin kasa.
Tun da farko Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran a yau za su kasance mafi tsanani tun farkon yakin.
Ya ce a rana ta goma ta aikin sojin da aka yi wa lakabi da Epic Fury, muna samun nasara, inda muke mayar da hankali ba tare da gajiyawa ba kan manufofin mu.
Mista Hegseth ya ce manufar Amurka da Isra'ila ita ce ta lalata karfin makamai masu linzami na Iran da sojojin ruwanta - da kuma hana ta mallakar makaman nukiliya.