Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 10/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 10 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Amurka ta ce tana yunƙurin wargaza cibiyar makamai masu linzami na Iran

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar White House ta ce sojojin Amurka na shirin wargaza cibiyar sarrafa makamai masu linzami na Iran, a rana ta goma sha daya na yakin.

    Mai magana da yawun fadar gwamnatin Karoline Leavitt ta ce jiragen saman kasar samfurin b-2 masu dogon zango sun yi amfani da bama-bamai kan cibiyoyin da aka binne a karkashin kasa.

    Tun da farko Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce hare-haren da Amurka ke kai wa Iran a yau za su kasance mafi tsanani tun farkon yakin.

    Ya ce a rana ta goma ta aikin sojin da aka yi wa lakabi da Epic Fury, muna samun nasara, inda muke mayar da hankali ba tare da gajiyawa ba kan manufofin mu.

    Mista Hegseth ya ce manufar Amurka da Isra'ila ita ce ta lalata karfin makamai masu linzami na Iran da sojojin ruwanta - da kuma hana ta mallakar makaman nukiliya.

  2. Hare-haren Isra'ila sun raba aƙalla kashi 10 na mutanen Lebanon da muhallansu

    Beirut

    Gwamnatin Lebanon ta ce hare-haren Isra'ila sun raba aƙalla mutum dubu ɗari bakwai da hamsin da muhallansu, wato kimanin kashi 10 na al'ummar ƙasar.

    Tuni hukumomin ƙasar suka fara kafa tantuna a cikin filayen wasanni domin tsugunar da dubban mutane. Isra'ila ta fara luguden wuta ne a Lebanon bayan ƙungiyar Hezbollah ta kai hare-haren jirage marasa matuka a Isra'ila domin goyon bayan Iran.

    Sojojin Isra'ila na cigaba da kutsawa kudancin Lebanon, wanda a cewarta take yi dominkare arewacin Isra'ila daga hare-haren Hezbollah.

  3. Iran ta kama mutum 30 bisa zarginsa da yi wa Amurka da Isra'ila leƙen asiri

    Iran

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ruwaito cewa hukumomin ƙasar sun kama mutum 30 bisa zarginsu da yi wa Amurka da Isra'ila leƙen asiri.

    Kafar ta ce daga cikinsu akwai mutum ɗaya ɗan ƙasar waje, kuma ma'aikatar tattara bayanan sirrin ƙasar ne suke tsare da su.

    Haka kuma an kama wasu waɗanda Iran ta bayyana "masu leƙen asiri na cikin gida" da "wakilan Isra'ila da Amurka" a kwanakin baya.

  4. Sakataren tsaron Amurka ya buƙaci Mojtaba Khamenei ya yi watsi da shirin nukiliya

    Iran

    Sakataren tsaron Amurka ya buƙaci Khamenei ya yi watsi da shirin nukiliya

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegsett ya yi kira ga sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da ya yi watsi da shirin ƙasarta na samar da makamin nukiliya.

    Haka kuma da yake amsa tambayoyin manema labarai kan rahoton da ke cewa Iran ta fara ƙarar da makamanta masu linzami, Hegsett ya ce hakan ba yana nufin ƙasar ba za ta iya ci gaba da harba makaman ba ne.

    Da aka tambaye shi game da rahoton da ke yawo cewa sabon jagoran addinin ya samu rauni, Mr Hegsett ya ce zai yi kyau sabon jagoran ya saurari shawarar Trump.

    Ya buƙaci Mojtaba ya yi amfani da shawarar Trump, inda shugaban na Amurka ya buƙaci sabon jagoran ya yi watsi da shirin ƙasarta na makamin nukiliya.

  5. Birtaniya na shirya jirgin ruwa domin yiwuwar tura shi Tekun Bahar Rum

    ....

    Asalin hoton, PA Media

    Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ce ana shirin sanya jirgin ruwan soji mai suna RFA Lyme Bay cikin yanayin shiri na musamman, idan har za a buƙaci a tura shi domin taimaka wa ayyukan ruwa a yankin gabashin Tekun Bahar Rum.

    A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron ya fitar da safiyar yau, ya ce: “A matsayin wani ɓangare na tsare-tsaren kariya, mun ɗauki matakin sanya jirgin RFA Lyme Bay cikin shirin gaggawa, domin ya zama a shirye idan an buƙaci taimakonsa wajen ayyukan ruwa a gabashin Tekun Bahar Rum.”

    Jirgin RFA Lyme Bay jirgin saukar da sojoji ne wanda kuma ke ɗauke da kayan jinya da wuraren kula da marasa lafiya.

    A halin yanzu yana ajiye ne a Gibraltar.

    Haka kuma Birtaniya na shirin tura jirgin ruwan yaki mai suna HMS Dragon zuwa Tekun Bahar Rum.

    Ministan tsaron ƙasar, John Healey, ya bayyana jiya cewa jirgin zai bar tashar ruwa ta Portsmouth cikin kwanaki kaɗan masu zuwa.

  6. Iran ta yi barazanar kawar da Trump

    ....

    Asalin hoton, EPA

    Wani babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya yi gargaɗi ga shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ce ya kamata ya yi hankali domin kada a “kawar da shi daga duniya”.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Larijani ya ce Iran ba ta jin tsoron abin da ya kira "barazanar Trump mara amfani."

    Ya ce, “Ko waɗanda suka fi ka ƙarfi ba su iya kawar da al’ummar Iran ba.”

    Sai ya ƙara da cewa, “Ka yi hankali, kada a kai ga kawar da kai daga duniya.”

    Wannan furuci na Larijani ya zo ne bayan Trump ya yi barazana a dandalinsa na Truth Social cewa Amurka za ta zafafa hare-harenta kan Iran idan ba ta buɗe mashigar Hormuz ba wadda ke da muhimmanci wajen safarar man fetur a duniya.

  7. Yau ne za a kai hare-hare mafi muni kan Iran - Sakataren tsaron Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth, ya ce za a zafafa hare-haren da ake kai wa Iran, kuma a yau ne za a kai hare-hare mafi muni tun da aka soma yakin.

    Hegseth ya ce cikin sao'i ashirin da hudu, Iran ba ta harba makamai masu linzami masu yawa ba, kuma Amurka za ta ci gaba da kai mata hare-hare har sai ta yi nasara kan ta.

    Tun da farko dai Rundunar juyin juya halin Iran ta yi watsi da kalaman da shugaba Trump ya yi na cewa yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran ya kusa zuwa karshe, inda suka ce su ne za su faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙin ba Amurkawa ba.

  8. Sama da mutum 100,000 sun rasa muhallansu a yaƙin Lebanon da Isra'ila - MDD

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu ɗari ne suka rasa muhallansu sakamakon yaƙin da ake yi a kasar Lebanon a cikin yini guda.

    Hukumar ta UNHCR ta ce sama da kashi biyu cikin uku na mutane miliyan daya ne a yanzu suka yi rajista a matsayin yan gudun hijira.

    Isra'ila ta fara luguden wuta a Ƙasar Lebanon ne bayan da Ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa Isra'ila domin nuna goyon baya ga Iran.

    Gwamnatin Lebanon ta sake yin kira da a soma tattaunawa ta kai tsaye da Isra'ila game da kawo karshen yakin, kuma ta yi kakkausar suka ga kungiyar Hizbullah da ta janyo kasar cikin yakin.

  9. Amurka ta gargaɗi sabon jagoran addinin Iran kan makaman nukiliya

    ....

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya gargaɗi sabon shugaban addinin Iran, Mojtaba Khamenei, da kada ya bi hanyar samar da makaman nukiliya.

    Hegseth ya ce zai zama "mai hankali" idan Mojtaba Khamenei ya saurari saƙon shugaban Amurka, Donald Trump, game da wannan batu.

    A yayin amsa tambayoyi kan raguwar ƙwarewar makaman Iran da jiragen sama marasa matuƙa da aka ruwaito cewa an rage su da kashi 90, Hegseth ya bayyana cewa hakan ba yana nufin Iran ba za ta iya harba makami ba.

    Dangane da rahotannin da ke cewa an ji wa Mojtaba Khamenei rauni, Hegseth ya ce ba zai iya yin sharhi kan ko an ji masa rauni ba, amma ya jaddada muhimmancin kada sabon shugaban ya shiga harkar nukiliya.

  10. Ƙasashe na ɗaukar matakan gaggawa kan rufe jigilar mai ta mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashe da dama na ɗaukar matakan gaggawa sakamakon rufe jigilar mai da iskar gas ta mashigar Hormuz da Iran ta yi yayin da Donald Trump da dakarun juyin juya halin Iran ke musayar barazana kan batun.

    Rundunar sojin ruwan Pakistan ta addamar da wani shiri na tsaron teku domin kare hanyoyin jiragen ruwa da kuma samar da kariya ga shigo da makamashi.

    Hukumomin ƙasar sun ce shirin na da nufin tabbatar da cewa iskar gas da man fetur da Pakistan ke shigo da su daga ƙasashen yankin Tekun Fasha ba su fuskanci tsaiko ba.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa zai ɗauki matakin “mai tsanani na kai wa Iran hari mafi muni idan ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz”.

    A martaninsu kuwa, dakarun juyin juya halin Iran sun ce ba za su bari ko lita ɗaya na mai ya ratsa ta mashigar ba matuƙar Isra'ila da Amurka na ci gaba da hare-haren da suke kai wa Iran.

    Shugaban kamfanin man fetur na gwamnati a Saudiyya, Amin Nasser, ya yi gargain cewa wannan rikici shi ne “babban rikicin da masana’antar makamashi ta yankin ta taɓa fuskanta”.

    Ya ƙara da cewa idan rikicin ya ci gaba kuma an ci gaba da rufe mashigar Hormuz, hakan na iya janyo mummunan tasiri ga kasuwannin man fetur a duniya.

  11. Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra’ila da Qatar da UAE

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Isra’ila, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun bayar da rahoton sabbin hare‑haren makamai masu linzami da Iran ta kai wa ƙasashensu.

    Rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta ce dakarunta na aiki domin kakkaɓo makaman, sannan an tura saƙon gargaɗi ga mutanen da abin ya shafa.

    A UAE, ma’aikatar tsaro ta bayyana cewa dakarunta na aiki domin daƙile makaman da Iran ta harba, tana kuma kira da mutanen da ke kusa su bi umarnin tsaro da kariya.

    Haka kuma, ma’aikatar tsaron Qatar ta ce rundunar sojojinta na aiki domin kakkaɓo makami mai linzami da aka harba zuwa ƙasar.

  12. An kashe fiye da mutum 1,300 a Iran tun bayan fara yaƙi - Gwamnati

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a ƙasar tun bayan fara yaƙin da ƙasar ke yi da sojojin Amurka da Isra’ila ya kai mutu 1,332.

    Wannan adadin ya haɗa da fararen hula dayawa ciki har da yara da mata, kuma dubban mutane sun jikkata sakamakon harin jiragen sama da rokaki.

    Gwamnatin ta ce an kai hari kan cibiyoyin kiwon lafiya, wanda ya ƙara taarbarewar yanayin jin ƙai da a wasu yankuna.

  13. Erdagon ya ce Iran ba ta da hujjar ƙeta sararin samaniyar Turkiyya

    ...

    Asalin hoton, REUTERS/Dilara Senkaya

    Shugaban ƙasar Turkey, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ƙeta sararin samaniyar Turkiyya da Iran ta yi ba ta da wata hujja da za ta kare ta, yana mai gargaɗin cewa hare-haren da ake kai wa ƙasashen yankin ba sa taimaka wa kowa.

    A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, Erdogan ya ce Turkiyya na ƙoƙarin buɗe ƙofar diflomasiyya domin taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka.

    A wani taron majalisar ministoci da aka yi a jiya da daddare, Erdogan ya ce: “Duk da gargaɗin da muka yi, ana ci gaba da ɗaukar matakai marasa kyau da kuma masu tayar da hankali, waɗanda za su iya jefa dangantakar Turkiyya cikin haɗari.”

    Wannan furuci ya zo ne bayan na'urar kare sararin samaniya ta Nato ya harbo makami mai linzami na Iran karo na biyu da ya shiga sararin samaniyar Turkiyya a ranar Litinin.

    Turkiyya na da rundunar soji ta biyu mafi girma a cikin ƙungiyar NATO, kuma tana da raba kan iyaka da Iran wadda ta kasance cikin kwanciyar hankali tsawon kusan shekaru 500.

  14. Ƙasashen yankin Gulf sun ba da rahoton sabbin hare-hare daga Iran cikin dare

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen yankin Gulf sun ce sun sake fuskantar sabbin hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka daga Iran cikin dare, yayin da ake ci gaba da artabu a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yayin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama kan Iran, tare da harin da Isra’ila ke kai wa a Lebanon, ƙasashen Gulf sun ce sun kakkaɓo wasu makamai da Iran ta kai musu harin ramuwar gayyar da take yi.

    Saudiyya ta ce ta kakkaɓo makami mai linzami guda ɗaya da kuma jirage marasa matuƙa guda biyar da aka harba cikin dare.

    Sojojin Kuwait kuma sun sanar da cewa sun samu nasarar kakkaɓo jirage marasa matuka guda shida.

    Bayan mutuwar wata mata mai shekaru 29 sakamakon wani hari da aka kai a Manama, babban birnin Bahrain, a daren Litinin, hukumomi sun ba da gargaɗi tare da kira ga mazauna yankin su nemi mafaka.

    Ma’aikatar tsaron Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa har yanzu tana ci gaba da kakkaɓo makamai masu linzami da jirage marasa matuka daga Iran.

    Haka kuma UAE ta ce an kai hari da jirgi mara matuƙi kan ofishin jakadancinta da ke Erbil a arewacin Iraƙi, lamarin da ya janyo ɓarna amma babu wanda ya jikkata.

  15. Wane zaɓi ya rage wa ƴaƴan jam'iyyar PDP gabanin zaɓe?

    ....

    Asalin hoton, @kabiruturakisan

    A ranar Litinin 9 ga watan Maris ne kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar soke hukuncin kotun farko, wadda ta hana hukumar INEC amincewa da sakamakon babban taron jam'iyyar PDP da aka yi a ranar 31 ga Oktoba.

    A bara ne dai mai shari'a James Omotosho na babban koton tarayya da ke Abuja ya soke babban taron PDP da aka yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban bara.

    A hukuncin, wanda dukkan alƙalan kotun guda uku suka yanke, kotun ɗaukaka ƙarar ta amince da hukuncin na ƙaramar kotun, inda ta ce hukuncin watan Oktoban ya yi daidai.

    Tun da farko dai wata kotu ta dakatar da jam'iyyar daga gudanar da taron, wanda a wajen ne aka zaɓi sababbin shugabanninta a ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, duk da cewa wata kotun daban ta amince mata.

    Sai dai kuma a ranar Alhamis na kafin babban taron ne wata babbar kotun jihar Oyo ta goyi bayan ci gaba da shirin gudanar da taron, inda ta jaddada umarnin da ta bayar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙorafin da mai ƙara ya shigar.

  16. Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon kocin Super Eagles Onigbinde

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa iyalai da abokan hulɗar fitaccen jami’in harkar ƙwallon ƙafa kuma tsohon kocin tawagar ƙwallon kafar Najeriya, Adegboye Onigbinde, wanda ya rasu yana da shekara 88.

    Shugaban ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya NFF da hukumar wasanni ta ƙasa tare da abokan aikinsa da magoya bayan ƙwallon ƙafa, yana mai tuna gudummawar da marigayin ya bayar a matsayin kocin Super Eagles na farko a shekarar 1982.

    Saƙon ta’aziyyar shugaban ƙasar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata.

    Shugaba Tinubu ya yaba da gudummawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa tun daga matakin ƙananan yara, da kuma ƙarfafa tsarin tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa a Najeriya.

    Ya kuma tuna da rawar da marigayin ya taka lokacin da ya jagoranci tawafar ƙwallon ƙafar Najeriya zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa ta Afrika a shekarar 1984..

    Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwarsa a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin ‘yan uwansa, Bolade Adesuyi, ya fitar.

    Iyalan sun ƙara da cewa za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa a gaba.

  17. Abin da ya sa na koma APC - Gwamnan Zamfara

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma shari’o’in da suka dabaibaye tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne babban dalilan da suka sa ya fice daga jam'iyyar zuwa APC.

    A ranar Litinin ne gwamnan ya sanar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a hukumance bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

    A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ficewar gwamnan zuwa APC ya zama dole saboda muradun al’ummar Zamfara.

    Sanarwar ta ce gwamnan ya ɗauki matakin komawa APC ne bayan shawarar masu ruwa da tsaki a jihar, musamman duba da matsalolin shari’a da jam'iyyar PDP ke fuskanta a halin yanzu.

    Gwamna Dauda Lawal ya ce ya yi baƙin ƙoƙarinsa don ganin ya sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin jam’iyyar domin tabbatar da haɗin kai da kuma damar tsayar da ƴan takara a zaɓuka masu zuwa.

    “Amma ƙoƙarin samar da zaman lafiya da sasanci ta hanyar sulhu bai yi nasara ba, lamarin da ya haifar da jerin shari’o’i da ka iya yin tasiri ga ‘yan siyasar da za su nemi takara a zaɓen shekarar 2027.” in ji sanarwar.

    Ficewar Dauda Lawan daga PDP na zuwa ne mako guda byan ficewar gwamnan Adamawa daga PDP zuwa APC, inda a yanzu jam'iyyar na da gwamnoni 2 kacal, inda APC ke da 31.

  18. Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasarta kan yiwuwar hari a Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da sanarwar tsaro inda ya gargaɗi ‘yan kasarsa kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyinta da kuma makarantu masu alaka da ƙasar a fadin Najeriya.

    A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar Amurka ko kuma cibiyoyin da ke da alaka da kasar.

    Sanarwar ta ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Legas, inda aka buƙaci ‘yan kasar su kasance cikin lura tare da ɗaukar ƙarin matakan tsaro idan za su je waɗannan wurare.

    Ofishin jakadancin ya ce "yana da muhimmanci mutane su riƙa canza hanyoyin tafiya da lokutan da suke fita, su guji yin abu iri daya a kai a kai, tare da kasancewa masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallinsu domin rage haɗarin da ka iya tasowa."

    Sanarwar ta ce: “Ya kamata ‘yan Amurka su ɗauki ƙarin matakan tsaro idan suna tafiya zuwa ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja, ko ƙaramin ofishin jakadancin ƙasar da ke Legas, da kuma makarantu masu alaka da Amurka.”

    Haka kuma sanarwar ta shawarci ƴan ƙasar da su guji cunkoson jama’a ko zanga-zanga, sannan su sake duba tsare-tsaren tsaron kansu tare da iyalansu.

    Sauran matakan kariya da ofishin ya bayar sun haɗa da tabbatar da cewa wayoyin hannu suna da caji idan wani lamarin gaggawa ta taso, da kuma sanin hanyoyin fita na gaggawa idan aka shiga wani gini.

  19. Kasuwannin mai sun fara farfaɗowa bayan kalaman Trump na kawo ƙarshen yaƙin Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasuwannin mai da hannayen jari sun yi armashi sakamakon tabbacin da Trump ya bayar na kawo karshen yankin Iran nan kusa.

    Farashin gangar ɗanyen man fetur ya fadi zuwa dala casa'in.

    Hannun jari a kasuwannin Asiya sun farfaɗo, idan aka kwatanta da irin asarar da aka tafka a ranar Litinin.

    Sai dai har kawo yanzu babu wani abu a kƙasa da ya sauya, domin har yanzu jiragen ruwa ba sa iya ratsa mashigin Hormuz.

    Trump ya ce taɓarɓarewar farashin mai da kuma faɗuwar kasuwar hannun jarin bata kai yadda ake ta faman zuzutawa ba.

    Sai dai ya sake tsokaci kan yadda hakan ya janyo tashin farashin kayayakin masarufi a cikin gida.

    Trumo ya yi alƙawarin sassauta takunkumin cinikayyar da ya sanya wa wasu kasashe don wadata yan kasar da abubuwan da suke bukata.

  20. Trump ya nuna damuwa kan ci gaba da rufe mashigin Hormuz da Iran ke yi

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana takaicinsa game da ci gaba da rufe mashigin Hormuz da Iran ke yi.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya yi barazanar kai wa Iran hari mafi muni idan ba ta buɗe mashigin ba.

    A baya ya ce hare-haren Amurka da Isra'ila ke kai wa basu shafi kayayyakin more rayuwa na Iran kamar wutar lantarki da cibiyoyin man fetur ba, amma hakan na iya sauyawa.