Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ta shirya wani babban taro na kwana uku kan nazarin waƙoƙin maza da tarihin shahararren mawakin nan, Muhammadu Bawa Ɗan Anace 'Yartsakuwa.
Taron ya samu halartar masana kusan 100 a Najeriya da ma jamhuriyar Nijar, waɗanda suka gabatar da muƙaloli daban-daban a kan ɓangarorin da suka shafi harshe da al'ada da kuma adabi.
A samu halartar sarakunan ciki har da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu da makada ciki har da wasu daga iyalan Ɗan Anaci da suka rage da kuma mutum biyu da ya yi wa waƙa wato Umaru Gindumi da Bagobiri Dantcimau da sauran mahalarta da manazarta.
An haifi Muhammadu Bawa Ɗan Anace Gandi a shekarar 1901 inda ya rasu a 1986 yana da shekara 85, a duniya.
Ya yi shuhura a waƙoƙinsa da suka fi mayar da hankali kan noma da dambe da kuma kokowa, waɗanda aka fi sani da "waƙoƙin maza".
Bawa Ɗan'ance ya fara waƙa ne tun yana yaro matashi, saboda tasowarsa a wurin kawunsa Anace.
Ya yi wa manyan ƴanwasan dambe irin su Dan Dunawa da Shago da Ado Dankore da sauran su waƙa.
Da farko dai Ɗan'ance ya fara ne da kiɗin dambe, sannan daga baya ya watsar ya koma kiɗan noma.
A kiɗin noma ne ya yi fice duk da cewa daga baya ya koma kiɗan dambe, inda ya haɗu da su Muhammadu Shago da Ɗandunawa da sauran 'yan dambe da ya yi wa waƙa.
Wasu daga waƙoƙinsa sun haɗa da waƙar Shago da ta Ado Ɗan Kore da Audu Kai Kaɗai Gayya, da Maigidan Gona da ta Garba na Godi da waƙar Basabce da sauran su.