Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 21/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Claudia Sheinbaum ta Mexico ta jajanta kan harin wani ɗan bindiga a ƙasar

    Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta bayyana goyon bayanta ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka jikkata a wani harin bindiga da ya faru a ɗaya daga cikin muhimman wuraren yawon buɗe ido na ƙasar.

    Wani ɗan bindiga, wanda ba a san asalinsa ba ne ya buɗe wuta kan masu yawon buɗe ido a tsohon wurin tarihi na Teotihuacan, inda ya kashe wata mata ‘yar ƙasar Canada tare da jikkata aƙalla mutane 13.

    Daga bisani kuma ya kashe kansa. Yanzu haka, saura kusan makonni bakwai kacal a fara wasan farko na gasar cin kofin duniya ta ƙwallon ƙafa ta maza, wadda za a gudanar a birnin Mexico City.

  2. Firaiministan Japan ta janyo cece-kuce kan aikewa da hadaya wurin bauta

    Firaministar Japan, Sanae Takaichi, ta aika da hadayar addini zuwa wani wurin ibada mai ciki da cece-kuce da ke girmama waɗanda suka mutu a yaƙin ƙasar.

    Wannan wuri da ke Tokyo yana ɗauke da sunayen mutane fiye da miliyan biyu, ciki har da wasu shugabannin Japan da aka yanke musu hukunci kan laifukan yaƙi.

    Ana ganin matakin zai iya tayar da hankalin makwabtan Japan din. Takaichi ta jima tana yawan kai ziyara zuwa wannan wuri tun kafin ta hau mulki a shekarar da ta gabata.

    China da kuma Korea Ta Kudu suna kallon wurin a matsayin alamar zaluncin Japan a lokacin yaƙi.

  3. Japan za ta fara sayar da jiragen yaƙi ga Turai

    Gwamnatin Japan ta bayyana cewa za ta soke wasu ƙa’idojin hada-hadar makamai da kasashen duniya a karon farko cikin shekaru da dama.

    Wannan sauyi, wanda majalisar ministoci ta amince da shi, an yi shi ne da nufin ƙarfafa masana’antar tsaron Japan.

    Wakiliyar BBC ta ce Japan ta jima da haramta fitar da makamai, kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi bayan yakin duniya na biyu, sai dai matakin na yanzu ya nuna a shirye take ta dawo da huldar tsaro da kasashen duniya a karfon farko cikin gwamman shekaru.

    Sabbin dokokin za su buɗe ƙofa ga yiwuwar sayar da makamai kamar makamai masu linzami, jiragen ruwa na yaƙi, da sauran makaman soja ga ƙasashen Turai da Asiya da ke neman hanyoyin sauya dogaro daga masu samar da makamai na Amurka.

  4. Apple ya naɗa John Ternus a matsayin shugaba

    Kamfanin Apple ya nada John Ternus a matsayin sabon shugabansa, inda zai maye gurbin ɗaya daga cikin manyan shugabanninsa da suka yi tasiri a masana’antar fasaha, Tim Cook.

    Mr Ternus, wanda a halin yanzu ke shugabantar sashen injiniyanci da kayan aiki na kamfanin, zai karɓi ragamar mulki a watan Satumba.

    Mr Cook zai sauka daga mukaminsa ne bayan shekaru goma sha biyar (15) yana jagorantar Apple, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da kamfanin ɗaya daga cikin manyan kamfanoni masu darajar tiriliyyoyin daloli a duniya.

    Sai dai a ‘yan shekarun nan, kamfanin ya dan fuskanci jan kafa musamman wajen rungumar fasahohin AI da zamani ya zo da su.

  5. Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar mutanen da ta zarga da kitsa juyin mulki

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar mutanen da ta zarga da kitsa juyin mulki ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda take tuhumar su da laifuka 13.

    Mutanen da gwamnatin ke ƙara sun hada da tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma ministan mai na ƙasar, Timipre Sylva da wani tsoffin sojoji da jami'in ƴan sanda da kuma wasu ƙarin mutum uku.

    Wasu takardu da BBC ta gani sun nuna yadda gwamnati ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ake sa ran mutanen da ake zargin za su bayyana a ranar Laraba, a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik.

    Daga cikin laifukan da ake tuhumar mutanen da su sun haɗa da cin amanar ƙasa da laifuka masu alaƙa da ta'addanci da kuma ƙin bayyana bayanan tsaro.

    A ƙarƙashin dokar Najeriya dai, cin amanar ƙasa na ɗaya daga cikin manyan laifuka da ka iya janyo hukunci mai tsananin da ya haɗa da ɗaurin rai da rai.

  6. Kotu ta umarci ICPC ta ci gaba da tsare Malam Nasiru El-Rufai har zuwa Yuni

    Babbar kotun jihar Kaduna ta ɗage zaman sauraron bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru ElRufai har zuwa farkon makon watan Yuni.

    Mai Shari'a Darius Khobo wanda ya sanar da hukuncin ya yi umarnin cewa Nasiru ElRufai ya kasance a hannun hukumar ICPC domin cigaba da tsarewa.

    Kotun ta kuma sanar da tsohon gwamnan cewa ya kame bakinsa daga yin maganganu sannan kuma dole ne ya rinƙa halartar dukkannin zaman kotu.

    A makon da ya gabata ne dai hukumar ICPC ta gurfanar da Malam Nasiru ElRufai a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda 9.

  7. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi ƙarar Mali

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama guda uku sun shigar da ƙasar Mali ƙara a kotun kare haƙƙoƙin ɗan adam bisa zargin ƙasar da gaza kare cin zarafin da sojoji suka yi a 2022.

    Ƙungiyayoyin sun ce ba ta taɓa jin faruwar irin wannan al'amari ba kuma hakan ka iya janyo abin da zai saka a tuhumi ƙasar saboda aikin da ta yi da sojojin.

  8. Harin Yahudawa ƴan kama wuri zauna ya kashe Falasɗinawa

    Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce Falasdinawa biyu ciki har da wani yaro mai shekara 13 sun mutu a wani hari da Yahudawa ƴan kama wuri zauna suka kai a Yamma da Kogin Jordan.

    Kungiyar ta ce wasu ƙarin mutane huɗu sun jikkata a ƙauyen Al-Mughayyir da ke kusa da Ramallah.

    Magajin garin ƙauyen ya ce sojojin Isra’ila ne suka kashe su. Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce tana binciken lamarin.

    A ƙarshen watan da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun kusan hare-hare 6 a kowace rana daga ‘yan kama wuri zauna.

  9. Babu tabbas Iran za ta shiga gasar cin kofin duniya ta 2026

    Ministan harkokin wasannin ƙasar Iran Ahmad Donyamali ya ce shawarar aikewa da tawagar ƴan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar zuwa gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na 2026 ya rataya a wuyan dakarun soji.

    Amurka dai na ɗaya daga cikin ƙasashe uku da ke karɓar baƙuncin gasar da za a fara a watan Yuni.

    Ministan ya ce Iran za ta duba yiwuwar aika tawagar ko akasin haka ne bayan da al'amura suka daidaita sannan kuma idan Amurka ta daina nuna halinta na "rashin kirki".

  10. Sojoji Iran sun ce jirgin ƙasar ya kutsa ta shingen Amurka zuwa tashar ruwa

    Sojojin jamhuriyar Musulunci ta Iran sun ce wani jirgin dakon mai mallakar Iran ya bujere wa shingen da Amurka ta saka inda ya shiga tashar ruwan ƙsar da ke kudanci.

    A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, sojojin sun ce " duk da yawan gargaɗi da barazanar da sojojin ruwan Amurka ke yi, jirgin na Iran mai suna Silica City, ya kutsa ya shiga tashar da taimakon sojojin ruwan Iran ɗin a daren da ya gabata, bayan ratsawa ta ruwan Arabian sea.

    Amurka dai har kawo yanzu ba ta ce uffan ba dangane da iƙrarin sojojin ƙasar Iran din.

    Cibiyar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, a wata sanarwa jiya ta ce tun bayan toshe tashoshin Iran, sojojin sun tilasta wa jiragen ruwa 27 ƙin shiga tashoshin ruwan Iran.

  11. Wane tasiri toshe hanyoyin ruwa ke yi a yaƙin Iran?

    Iran ta kaddamar da hare-haren jirage mara matuki kan jiragen ruwan sojin Amurka a yankin Oman, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran Tasnim ya ruwaito, bayan da Amurka ta ƙwace wani jirgin ruwa ɗauke da tutar Iran.

    Amurka ta ce an tarwatsa jirgin na Iran bayan "kasa yin biyayya ga gargadin da aka yi ta yi" daga sojojin ƙasar na kusan sa'o'i shida.

    Bayanai sun nuna cewa jirgin na Touska ya kasance yana da nisan mil 40 da tashar jiragen ruwa na Chabahar, a kudu maso gabashin Iran, bayan barin tashar Klang, a Malaysia, a ranar 12 ga Afrilu.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sun yi ta "gargaɗin dakatar da zirga-zirga" bayan kokarin bi ta hanyar da Amurka ta kulle a tashar jiragen ruwa na Iran.

    "Ma'aikatan jirgin na Iran sun ki bin umarni, saboda haka ne sojojin ruwan mu suka ɓula wani wuri a injin jirgin," in ji shi. A yanzu katon jigin ruwan yana karkashin ikon Amurka, a cewar Trump. Ya kuma kasance cikin takunkuman Amurka "saboda tarihin aikata ba daidai ba".

  12. Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC

    Magoya bayan tsoffin ƴan takarar shugaban ƙasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata ƙungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam'iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe.

    Ƙungiyar, wadda aka kafa a Abuja a ranar Litinin, ta ce tuni ta soma samar da rassanta a jihohi 36 na ƙasar da Abuja, tare da naɗa shugabanninta na jihohi da yankuna domin jagorantar yaɗa ayyukanta.

    Sakataren watsa labaran ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana ta a matsayin gamin gambiza, don haɗa karfi da karfe tsakanin ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta Obidient Movement, da kuma ta magoya bayan Kwankwaso, wato Kwankwasiyya.

    Wannan dai na nuna wani irin sabon salo na sake ɗaure ɗamara yayin da ake ta ƙulla mu'amalar siyasa, sakamakon rashin tabbacin wanda zai lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na ADC kafin babban zaɓen 2027.

    Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ta kunshi mambobi daga Kwankwasiyya, da Obidients, da jam'iyyar NNPP, da Labour da kuma wasu daga ADC.

  13. Dalilai huɗu da suka sa tattaunawar Iran da Amurka ke cikin ƙila-wa-ƙala

    Makomar tattaunawar Iran da Amurka ta shiga cikin rashin tabbas yayin da lokacin da aka kebe na tsagaita wuta ke daf daƙkarewa. Abin da ya sa ake gani a yanzu ba wai rashin cimma matsayar diflomasiyya ba ce kaɗai, har ma da kalamai masu zafi da tsauri tsakanin ɓangarori, barazana da kuma bayanai masu cin karo da juna daga dukkan ɓangarori.

    A cewar rahotanni da dama, babu tabbas cewa Iran za ta shiga tattaunawar da aka tsara za a yi wanda Pakistan ke shiga tsakani. Yayin da wasu majiyoyi ke bayyana cewa Iran na duba yiwuwar shiga tattaunawa, wasu kuwa sun ce ƙasar za ta iya janye wa watakila saboda yanayin da ake ciki.

    A ɗaya gefe, lamarin yana ci gaba da zama mai tsarkakiya bayan da rahotanni suka ce mataimakin shugaban Amurka wanda ke jagorantar tawagar tattaunawar, JD Vance, bai ma je Pakistan ba watakila saboda rashin tabbas da ake da shi kan tattaunawar.

    A nan, tattaunawar za ta iya kawo fatan cimma matsayar diflomasiyya ko kuma barazanar komawa fagen daga.

  14. Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami'an tsaro uziri

    A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al'ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani.

    Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kafar Television ta RTN, inda ya ƙara da kira ga yan Nijar da su fahimci cewa jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a kowane ƙauye ba, duba da cewa Nijar na da kusan ƙauyuka 32,000.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan ta'adda musamman a kan sojojin ƙsar.

  15. Rundunar IRGC ta bayyana Donald Trump a matsayin "maƙaryaci kuma mayaudari"

    Kamfanin dillancin labarai na Fars da ke da alaƙa da dakarun juyin-juya hali na Iran ya wallafa maganar wani babban sojan ƙasar a shafinsa na Telegram.

    Manjo Janar Abdullahi wanda ya rubuta saƙon da Farsi ya ce rundunar IRGC ta wahalar da Amurka da Isra'ila inda ta tilasta musu neman tsagaita wuta ido biyu.

    Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta bar "maƙaryaci kuma mayaudarin shugaban Amurka ya rinƙa ƙirƙirar labaran ƙarya dangane da haƙiƙanin abin da ke faruwa ba," musamman a kan batun mashigar Hormuz.

  16. Har yanzu tawagar Iran ba ta je Pakistan ba

    Gidan talbijin na ƙsar Iran ya wallafa wani saƙo a shafin Telegram cewa kawo yanzu babu wata tawagar ƙasar da ta tafi zuwa Islamabad domin tattaunawa da Amurka.

    Saƙon ya yi watsi da abin da ya kira jita-jita dangane da tashin tawagar zuwa Islamabad ko kuma saukarta da kafafen watsa labaran ƙasashen duniya keta yaɗawa.

    Saƙon ya kuma nanata matsayar jami'an Iran da suka hada da kakakin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf wanda a baya ya ce Iran ba za ta amince da duk wata yarjejeniya ba a ƙarƙashin matsin lamba.

  17. China ta yaba wa Pakistan a ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka

    Jakadan China a Pakistan ya bayyana cikakken goyon bayan ƙsarsa ga ƙoƙarin shiga tsakanin da ƙasar Pakistan ke yi domin sasanta Amurka da Iran.

    Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce mataimakin firaiminista Ishaq Dar wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen Pakistan ya gana da Jiang Zaidong domin tattauna halin da ake ciki.

    A lokacin ganawar tasu, mista Zaidong ya bayyana farin cikinsa ga yadda Pakistan take ci gaba da ƙoƙarin samar da tattaunawa tsakanin Iran ɗin da Amurka.

  18. Har yanzu Iran ba ta yanke ko za ta je Pakistan tattaunawa da Amurka ba

    Kwana guda ya rage yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta kare, yayin da har yanzu babu tabbacin ko Iran din za ta halarci tattaunawar tsagaita wuta a Pakistan.

    Tehran ba ta tabbatar ko za ta tura tawaga ba, yayin da mataimakin shugaban Amurka JD Vance wanda zai jagoranci tawagar Amurka, har yanzu bai tashi daga Washington ba.

    Shugaba Donald Trump ya ce ba zai ɗage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin Iran ba har sai an cimma yarjejeni

    Wakilin BBC ya ce mista Trump na son a sake bude mashigin Hormuz, kana Iran ta mika wa Amurka sinadarin Uranium din ta da ta sarrafa, abun da Iran din ta bayyana a matsayin wasan yara.

    Jagoran masu tattaunawar zaman lafiyar na bangaren Iran Mohammad Bagher Qalibaf, ya bayyana cewa ba za za su amince da tattaunawa ƙarƙashin matsin lamba ba

  19. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da warhaka da fatan an yi wayi garin ranar Talata lafiya. Yau ma kamar kullum mun dawo muku da shafin namu na kai tsaye inda muke kawo muku muhimman labarai dangane da al'amuran yau da kullum.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.