Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Harin Amurka da Isra'ila ya kashe shugaban sashen leƙen asirin IRGC

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta tabbatar da mutuwar shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar, Majid Khademi.

    Cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar da safiyar yau Litinin ta zargi Isra'ila da Amurka da kai masa hari.

    BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Isra'ila, wadda ta ce za ta ''duba'' rahoton.

    Khademi ne ya maye gurbin Mohammad Kazemi, wanda ya mutu a hare-haren Isra'ila ranar 15 ga watan Yunin 2025, lokacin yaƙin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran.

    A watan Fabrairun da ya wuce lokacin zanga-zangar ƙasar, Khademi ya zargi Shugaba Trump na Amurka da tunzura abinda jami'an Iran suka bayyana da kitsa dabarar ''kashe mutane'', da nufin kafa hujjar far wa ƙasar daga ƙetare.

    A lokacin Khademi ya yi iƙirarin cewa fiye da jami'an leƙen asiri 10 daga ƙasashen waje, ciki har da sashen yaƙin Intanet na Isra'ila ne suka taka raw a kitsa zanga-zangar.

    Wani kamfanin dillancin labarai na Amurka da ke gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama, ya ce aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe a lokacin zanga-zangar ta watan Janairu.

  2. Iran ta ce babu tabbas kan shigarta Gasar Kofin Duniya

    Iran ta ce babu tabbas ga me da shigar tawagar 'yan wasanta a gasar kwallon kafa ta Kofin Duniya mai zuwa, har sai Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, Fifa ta sauya wasannin da Iran ɗin za ta yi daga Amurka zuwa Mexico.

    Ministan wasanni na Iran Ahmad Donyamali ya ce ba shi da tabbacin samun tsaron lafiyar ƴanwasan Iran a Amurka.

    Fifa ta ƙi sauya wasannin Iran ɗin duk kuwa da cewa Shugaba Trump ɗin kansa ya ce, shigar tawagar Iran Amurka ka iya jefa su cikin hadari.

    Iran za ta kara da New Zealand da Belgium da kuma Masar a biranen California da Seattle.

  3. 'Za mu buɗe mashigar Hormuz idan jiragen sun amince su biya ɓarnar da yaƙin ya yi mana'

    Wani hadimin fadar shugaban Iran, Mahdi Tabatabaei ya ce za a sake buɗu mashigar Hormuz idan har ''jiragen da za su wuce ta mashigar sun amince su riƙa biyan harajin da za a yi amfani da shi don gyara ɓarnar da yaƙin ya yi wa ƙasar''.

    A baya jami'ai da ƴanmajalisar Iran sun bayyana yiwuwar sanya haraji kan duka jirgin da zai wuce ta mashigar.

    Yayin da yake mayar da martani da barazanar Trump ta baya-bayan nan, Tabatabaei ya ce shugaban na Amurka ''ya riga ya haifar da yaƙi a Gabas ta Tsakiya yanzu kuma yana sake wata barazana''

    Ya ce ''ɓaɓatu da hauragiyar'' da Trump ke yi alamu ne ya yadda ya ''kiɗime da ruɗewar'' da yake ciki.

  4. An gano gawa biyu a Isra'ila bayan harin Iran kan wani gida

    Hukumomin Isra'ila sun ce an gano gawarwakin wasu mutum biyu a cikin ɓaraguzai, bayan wani harin makami mai linzami na Iran a kan wani gida a birnin Haifa na arewacin Isra'ilar.

    Har yanzu kuma ba a san inda wasu mutum biyu suke ba.

    Can a Iran ɗin kuwa kafofin yaɗa labaran Iran sun ce wani harin sama da aka kai kan wani gini da jama'a ke zama a ciki a babban birnin ƙasar, Tehran ya kashe mutum 13.

    Wasu ƙarin hare-haren da aka kai a babban birnin sun faɗa kan wata jami'a da kuma wani wajen rarraba iskar gas, abin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a birnin.

    Jami'an Iran sun ce hare-haren Amurka da Isra'ila a birnin Qom na tsakiyar ƙasar, sun kashe aƙalla mutum biyar.

  5. Iran ta ce mummunan ramuwar gayya za ta biyo idan Trump ya aiwatar da barazanarsa

    Iran ta yi gargaɗin cewa muddin Shugaba Trump, ya ci gaba tare da aiwatar da barazanarsa ta kai hari kan wuraren farar hula da suka hada da gadoji da tasoshin wutar lantarki, to shakka babu ramuwar-gayya da za ta yi za ta kasance mummunar gaske kuma ba ƙarama ba.

    Yau ne ya kamata ya zama ƙarshen wa'adin da Shugaba Trump ya ɗeba wa Iran ta buɗe mashigar Hormuz, ko ta fuskanci munanan hare-hare na lalata kayayyakinta da ba na soji ba - ciki har da tashoshin samar da lantarki.

    A ranar Lahadi ne, shugaban na Amurka ya kara sanya sabon wa'adi na zuwa gobe Talata, ga Iran ɗin ta sake buɗe mashigar.

    Kafofin yaɗa labarai na Amurka na cewa masu shiga tsakani - na can suna ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta tsawon kwana 45 - kodayake rahotanni na cewa ba lalle a samu nasarar hakan ba.

    A dalilin sabuwar barazanar ta Trump, farashin mai ya yi sama a Asia a yau Litinin, amma kuma kasuwannin hannun jari na nan yadda suke - ba su tashi ba, kuma ba su yi kasa ba.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-sate barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.