Yau ce rana ta bakwai ta rikicin da ake fama da ita a Gabas ta Tsakiya.
Mazauna Tehran sun shaida wa BBC cewa daren jiya shine “mafi muni” tun farkon rikicin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kai wani sabon harin dare a kan Lebanon, musamman birnin Beirut.
A daidai lokacin kuma Isra'ilar ta yi gargaɗin karin yiwuwar hare-haren Iran a ƙasarta.
Hukumomin gaggawa na ƙasar sun ce ba a samu rahoton mutuwa ko raunuka ba tukuna.
Ƙasashen Gulf, ciki har da Saudiyya da Qatar da Bahrain, sun ce sun kakkabo makaman da Iran ta harba masu cikin dare.
Ana gudanar da ayyukan kwashe mutane yayin da dubban mutane suka makale a yankin Gulf din. Jirgin farko na haya daga Oman ya sauka a tashar jirgin Stansted na Landan a daren jiya, inda wani mutum ya bayyana tafiyar da shiga jirgin a matsayin “abin mamaki.”
Mataimakin Firaminista Birtaniya, David Lammy, ya ce gwamnati na fatan ganin karin jiragen haya daga Oman da jiragen kasuwanci daga yankin Gulf.
A yayin hira da BBC, Lammy ya ce Birtaniya ta kasance “a bayyane” cewa ba ta so ta shiga cikin “harin da Amurka da Isra’ila, ke kai wa Iran amma za ta goyi bayan duk wani mataki na kariya.
A gefe guda, shugabar jam’iyyar Tory, Kemi Badenoch, ta soki martanin gwamnati kan hare-hare a wani sansanin soja a Cyprus.