Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba, inda ya ce wannan ne kaɗai hanyar da za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi.

    Mista Trump ya kuma ce bayan ta yi saranda, sai kuma ta zaɓi sabon shugaba wanda gwamnatinsa ta amince da shi, inda ya ce daga nan ne kuma Amurka da ƙawayenta za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.

    A gefe guda kuma sakatare janar na Majalisar ɗinkin duniya Antonio Gutteress ya yi kiran a kawo ƙarshen yaƙin, inda ya ce tashin hankalin da ake samu a Gabas ta Tsakiya na yin mummunan illa ga fararen hula.

  2. Akwai ƴan mata da suka fuskanci cin zarafi da fyaɗe a rikicin Habasha - Amnesty

    AMNESTY INTERNATIONAL

    Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗanadam ta Amnesty International ta ce mata da ƴan mata a gabashin yankin Oromia na ƙasar Habasha na fama da cin zarafi ta hanyar lalata, da bautarwa da tilasta musu barin muhallansu a yakin da yankin da ke fama da rikici.

    Faɗa tsakanin dakarun gwamnati da na ƴan tawayen Oromo Liberation Army ya fantsama sassan ƙasar, musamman yankin Kellem Wallaga.

    Wakilin BBC ya ce Amnesty ta zanta da mata 10 da suka kuɓuta a yankin Kalamogazan, kuma 7 daga cikinsu sun ce ba su kai shekara 18 ba a lokacin da aka ci zarafinsu.

    Sun ce an gana musu azaba ta hanyar lakaɗa musu duka da fyade inda a wasu lokutan akan shafe mako guda ana yi, kuma dukkan ɓangaren sojin gwamnati da na tawayen ake zargi da aikatawa.

  3. Iyalan El-Rufai sun buƙaci a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba

    El-Rufai

    Asalin hoton, Bello El-Rufai/Facebook

    Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun bayyana cigaba da riƙe shi da ake yi a matsayin karan-tsaye ga dokokin Najeriya, sannan suka yi zargin ana amfani da hukumar yaƙi da cin hanci a matsayin karen farauta domin muzgunawa ƴan hamayya.

    Iyalan sun bayyana haka ne a wata sanarwa da Bello El-Rufai ya fitar a madadinsu a ranar Juma'a, 6 ga watan Maris, inda ya bayyana tsare mahaifin nasu da "saɓa doka."

    "Har yau Juma'a 6 ga watan Maris, Nasir El-Rufai na tsare a hannun ICPC wanda ba bisa doron doka suke yi ba. Muna sanar da al'umma cewa babu dokar da ta amince a cigaba da tsare shi."

    Iyalan sun ce an fara tsare tsohon gwamnan ne a ranar 18 ga Fabrairun 2026, "sannan hukumar ta nemi izinin tsare shi na kwana 14. Amma har yanzu da kwanakin suka ƙare, ICPC ba ta kai shi kotu ba, sannan tana cigaba da tsare shi. Wannan karan-tsaye ne ga dokokin Najeriya, saboda hukumar ta gaza wajen gabatar da shi a kotu, ko kuma ta sake shi."

    Bello ya bayyana a sanarwar cewa cigaba da tsare El-Rufai ya ƙara tabbatar "abin da muka daɗe muna fargaba cewa ana amfani na hukumar ne domin muzgunawa abokan hamayya. Don haka ne muke nema da a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba."

  4. Tinubu ya tura jakadun Najeriya 65 zuwa ƙasashe

    Shugaban ƙasa

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da aika jakadun Najeriya zuwa ƙasashen duniya domin wakiltar ƙasar a can.

    Wannan na zuwa ne bayan majalisar dattawar ƙasar ta tantance jakadun a watan Disamban shekarar 2025 da ya gabata bayan shugaban ya buƙaci su yi hakan.

    Daga cikin waɗanda ak aika akwai:

    • Ita Enang - Afrka ta Kudu
    • Ikpeazu Victor - Spain
    • Mahmud Yakubu - Qatar
    • Vice Admiral Ibok-Ete Ibas - The Philippines
    • Reno Omokri - Mexico
    • Aminu Dalhatu - Birtaniya
    • Laftanal Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya - China
    • Femi Fani-Kayode - Jamus
    • Ayodele Oke - Faransa
    • Yakubu N. Gambo - Saudiyya

    Akwai wasu da aka tura, inda jimilla waɗanda aka tura zuwa yanzu sun kai 65, kamar yadda mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Trump ya ce babu yarjejeniya da Iran sai ta miƙa wuya gaba ɗaya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu wata yarjejeniya da za a yi da Iran face idan ta amince da miƙa wuya gaba ɗaya.

    A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumuntansa na Truth Social, Trump ya rubuta cewa “babu wata yarjejeniya da za a yi da Iran sai idan ta miƙa wuya ba tare da wani sharadi ba.”

    Ya ƙara da cewa bayan haka, idan aka samu shugabanni da suka dace kuma aka amince da su, su da ƙawayensu za su yi aiki tukuru domin taimaka wa Iran ta farfaɗo daga matsalolin da take ciki.

    Trump ya ce idan hakan ta faru, Iran za ta iya zama ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki fiye da da, mai ƙarfi da kuma ci gaba.

  6. UAE ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami tara da jirage marasa matuƙa 109

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin tsaron ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ce rundunar saman kasar sun kakkaɓo makamai masu linzami guda tara da kuma jiragen sama marasa matuƙa guda 109 a yau ranar Juma’a.

    Ma’aikatar tsaron ƙasar ta bayyana cewa dukkan makamai masu linzami tara da aka gano a wannan rana an lalata su kafin su kai ga inda suka nuai.

    Haka kuma jami’ai sun gano jiragen sama marasa matuƙa guda 112. Daga cikinsu, an kakkaɓo 109 yayin da uku suka faɗi a cikin ƙasar.

    Tun bayan fara rikici a yankin gabas ta tsakiya, mutane uku sun mutu yayin da wasu 112 suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai kan UAE.

    Ma’aikatar tsaron ta ƙara da cewa rundunar sojin ƙasar a shirye take domin fuskantar duk wata barazana, tana mai jaddada cewa za ta kare ƙasarta da kuma muradun ƙasarta.

  7. Iran ta gargaɗi yankin Kurdawa ta Iraq kan kai mata hari

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta yi gargaɗi ga yankin Kurdawa na arewacin ƙasar Iraq cewa idan wasu ƙungiyoyin 'yan aware suka kai hari kan Iran daga yankin, to za ta kai hare-hare kan wurare daban-daban a yankin.

    Wani jami’in Iran mai suna Ali Akbar Ahmadian ya ce a baya Iran ta kai hare-hare ne kawai kan sansanonin Amurka da Isra’ila da kuma wasu ƙungiyoyin Kurdawa da take zargi. Amma ya ce idan aka bari waɗannan ƙungiyoyi suka yi amfani da yankin Kurdistan domin kai hari kan Iran, to Iran za ta kai hari kan duk wasu wurare da take zargin suna taimaka musu.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa a wata hira ta waya da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa yana goyon bayan yiwuwar harin Kurdawa kan Iran.

    Amma lokacin da aka tambaye shi ko Amurka za ta taimaka da jiragen yaƙi, sai ya ce ba zai iya bayyana hakan ba.

    A gefe guda kuma, wasu ƙungiyoyin Kurdawa da ke adawa da gwamnatin Iran sun musanta rahotannin da ke cewa mayakansu sun shiga cikin ƙasar Iran.

  8. Kotu ta bayar da belin Malami kan naira miliyan 200

    ...

    Asalin hoton, Malami/X

    Bayanan hoto, Tsohon Ministan shari'ar Najeriya

    Babbar koytun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta amince da belin tsohon ministan shari'ar ƙasar, Abubakar Malami da iyalinsa.

    Alƙaliyar kotun, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik, ta amince da belinsu a kan kuɗi naira miliyan 200 kowanennsu da kuma mutane biyu da za su tsayawa kowa daga cikinsu.

    Kotun ta kuma saka sharaɗin cewa dole ɗaya daga cikin masu tsaya musun ya kasance yana da gida a unguwar Maitama ko Asokoro, yankuna mafiya daraja a Abuja.

    Alƙaliyar kotun ta kuma umurci waɗanda ake tuhuma su mika fasfo ɗinsu ga kotu.

    Kotun ta ce tsohon ministan shari'ar Najeriya da iyalinsa za su kasance a gidan yari har sai sun cika sharuddan belin.

    Sannan kotun ta saka ranar16 ga Maris domin fara sauraron shari’ar.

    Ana zargin Malami tare da iyalan nasa da ɓarnatar da kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 8.7 ta hanyar wasu kamfanoni da mallakar kadarori.

  9. Kamfanin man Amurka a Kurdistan ta Iraq ya dakatar da aiki bayan kai masa hari

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Kurdistan ta ƙasar Iraq sun ce an dakatar da aikin haƙar mai a wani filin mai na Amurka da ke wurin bayan an kai masa hari.

    A wani sako da gwamnatin yankin ta wallafa a X, an bayyana cewa wasu ƙungiyoyi masu aikata laifi a Iraq ne suka kai wai filin man wanda kamfanin HKN Energy na Amurka ke gudanarwa a lardin Dohuk hari.

    Harin ya haifar da “lalacewar kayan aiki a filin da kuma dakatar da haƙar mai.”

    Kamfanin dillancin labaran AFP ta ruwaito cewa an kai harin ne da jiragen sama marasa matuƙa guda biyu a ranar Alhamis.

  10. Mazauna Tehran sun bayyana dare mafi muni yayin da Iran ke ci gaba da hari

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Yau ce rana ta bakwai ta rikicin da ake fama da ita a Gabas ta Tsakiya.

    Mazauna Tehran sun shaida wa BBC cewa daren jiya shine “mafi muni” tun farkon rikicin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kai wani sabon harin dare a kan Lebanon, musamman birnin Beirut.

    A daidai lokacin kuma Isra'ilar ta yi gargaɗin karin yiwuwar hare-haren Iran a ƙasarta.

    Hukumomin gaggawa na ƙasar sun ce ba a samu rahoton mutuwa ko raunuka ba tukuna.

    Ƙasashen Gulf, ciki har da Saudiyya da Qatar da Bahrain, sun ce sun kakkabo makaman da Iran ta harba masu cikin dare.

    Ana gudanar da ayyukan kwashe mutane yayin da dubban mutane suka makale a yankin Gulf din. Jirgin farko na haya daga Oman ya sauka a tashar jirgin Stansted na Landan a daren jiya, inda wani mutum ya bayyana tafiyar da shiga jirgin a matsayin “abin mamaki.”

    Mataimakin Firaminista Birtaniya, David Lammy, ya ce gwamnati na fatan ganin karin jiragen haya daga Oman da jiragen kasuwanci daga yankin Gulf.

    A yayin hira da BBC, Lammy ya ce Birtaniya ta kasance “a bayyane” cewa ba ta so ta shiga cikin “harin da Amurka da Isra’ila, ke kai wa Iran amma za ta goyi bayan duk wani mataki na kariya.

    A gefe guda, shugabar jam’iyyar Tory, Kemi Badenoch, ta soki martanin gwamnati kan hare-hare a wani sansanin soja a Cyprus.

  11. Iran ta ce ta kai wa jirgin yaƙin Amurka farmaki

    XX

    Asalin hoton, Iran's official news agency, IRNA

    Dakarun juyin juya halin Iran sun sanar da fara zagaye na 22 na aikin soji mai suna “True Promise 4”, inda suka tabbatar da kai farmaki kan wani jirgin yaƙin Amurka F-15E a wani ɓangare na ci gaban hare-haren da suke kai wa.

    A wannan zagaye na hare-hare, rundunar ta harba makamai da dama da suka haɗa da Khorramshahr 4, Khaibar, da Fateh, a kan Isra'ila

    Kafar yaɗa labaran ƙasar Iran, IRNA, ta ruwaito cewa rundunar sojin Iran ta kuma kai harin jirgin sama maras matuƙi kan birnin Tel Aviv na Isra'ila tare da yin alƙawarin faɗaɗa hare-haren kan abin da suka kira “gurin abokan gaba.”

    Wannan yana nuna cewa Iran na ƙara tsananta hare-haren ta wajen amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi a kan Isra’ila da Amurka.

  12. Yaƙin Iran: Maersk ya dakatar da wasu ayyukan jigilar kaya na ɗan lokaci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin jigilar kaya na Maersk, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin jigilar kaya a duniya, ya dakatar da wasu daga cikin ayyukan tankokinsa na jigilar kaya na ɗan lokaci .

    Wannan ya haɗa da tankar FM1, wanda ke haɗa Gabas ta Nesa da Gabas ta Tsakiya, da tankar ME11, wanda ke haɗa Gabas ta Tsakiya da Turai.

    Kamfanin ya bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan gudanar da wani bincike domin gano matsaloli ko barazanar da ka iya tasowa ga ma’aikata da jiragen ruwa a wanna yanayi da ake fama ta yakin tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

    A cikin sanarwa, Maersk ta ce matakin na ɗan lokaci ne domin kare lafiyar ma’aikata da jiragen ruwa, da kuma rage tasirin katsewar aiki a sauran ayyukan kamfanin a faɗin duniya.

    Kamfanin ya jaddada cewa wannan mataki na tsaro ne kuma wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da ci gaba da ingantaccen aiki a dukkan sassan ayyukansa.

  13. Ƙasashen tekun Fasha sun ce sun daƙile hare-haren sama daga Iran

    Ƙasashen yankin tekun Fasha sun ce, sun dakile hare-hare ta sama da Iran ke kai musu.

    Qatar ta ce ta dakile wani harin jirgin sama maras matuki da aka nufa kan sansanin sojin sama na Al Udeid - wanda shi ne mafi girma na sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

    Saudiyya ma ta ce, ta kakkabo tare da lalata makamai masu linzami guda uku, da aka hari sansanin sojin sama na Yarima Sultan, wanda shi ma, sojin Amurka ke wajen.

    Haka ita ma Bahrain, ta ce ta tare makamai masu linzami uku.

  14. 'Iran ta kasance ba ta da intanet na tsawon kwanaki shida'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Iran ta kasance ba ta da intanet na tsawon kwanaki shida, in ji ƙungiyar masu sa ido kan intanet ta NetBlocks.

    Ƙungiyar ta ce ƙasar tana da “ kaso 1 da haɗin intanet a sa’o’i 144 da suka wuce.”

    Katsewar intanet yana daga cikin abubuwan da ke sanya wahalar rahoton labarai daga ƙasashen waje kan abin da ke faruwa a ciki Iran.

    Haka kuma, gwamnatin Iran ta rufe ayyukan intanet a baya yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a farkon wannan shekara.

  15. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana aiki domin kakkaɓo makaman Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce tana aiki don kakkaɓo sababbin makamai da Iran za ta harba zuwa ƙasar

    “A ɗan lokaci da ya gabata, IDF ta gano wasu makamai da aka harba daga Iran zuwa cikin ƙasar Isra'ila” in ji ta a cikin wani sanarwa da ta wallafa a shafin Telegram.

    An kuma aika wa mutanen kasar “gargadi da umarnin kiyaye kai” ta wayoyin salula“

    An gargadi wadanda suka samu wannan sakon su shiga wani wuri mai tsaro su tsaya har sai an ba da ƙarin sanarwa.

  16. An kama mutum huɗu a Landan kan zargin taimakawa Iran

    ’Yan sanda a Landan sun kama mutum huɗu a wani binciken yaki da ta’addanci da ake yi wanda ke da alaƙa da Iran, a cewar rundunar ’yan sandan Metropolitan .

    ’Yan sandan sun kama wani ɗan Iran da kuma wasu uku masu waɗanda suke da shedar yan kasar Birtaniya da Iran a lokaci guda, bisa zargin taimakawa wata hukumar leƙen asirin Iran.

    Rundunar ta ce binciken ya shafi zargin sa ido da aka yi kan wasu wurare da kuma mutane da ke da alaƙa da al’ummar Yahudawa a Landan.

    Har yanzu ana ci gaba da bincike a yankunan Watford, Barnet, da kuma wani adireshi a Wembley.

  17. China na tattaunawa da Iran kan wucewar tankokin man Qatar cikin aminci

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    China na cikin tattaunawa da Iran domin ba da damar jiragen da ke ɗauke da mai da iskar gas na Qatar su wuce cikin aminci ta mashigar Hormuz, kamar yadda rahoton Reuters ya nuna, bisa ga wasu majiyoyi da ba a ambata sunayensu ba.

    A yayin da aka shiga rana ta bakwai na yakin da ke tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka, dubban jiragen ruwa sun tsaya cak a kusa da wannan muhimmiyar hanya, wacce ke ɗaukar kusan kashi ɗaya cikin biyar na mai da iskar gas na duniya.

    Biyo bayan wannan sabon rikici a Gabas ta Tsakiya, farashin makamashi ya tashi.

    Rahotannin Reuters da Bloomberg sun nuna cewa wani jirgin mai da ake tsammanin na China ne ya wuce ta tekun a ranar Alhamis, duk da cewa BBC ba ta samu tabbatarwa ba tukuna.

    China na ɗaya daga cikin manyan masu sayen mai na Iran kuma ta bayyana rashin amincewa da hare-haren IIsra'ila da Amurka ke kai wa kan Iran.

  18. Majalisa ta gayyaci Kyari kan zargin ɓatan maƙudan kuɗi a NNPCL

    Tsohon shugabna NNPCL

    Asalin hoton, MELEKYARI/NNPC

    Kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar Dattawan Najeriya ya gayyaci tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasar, Mele Kyari, domin ya yi bayani kan zargin wasu kuɗaɗe da yawansu ya kai naira tiriliyan 210 da ake cewa ba a yi cikakken bayanin yadda aka kashe su ba tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023, lokacin da yake jagorantar kamfanin.

    An gayyaci Kyari tare da tsohon babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan kula da harkokin zuba jari na kamfanin, Bala Wunti.

    Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ne ya bayar da umarnin gayyatar a ranar Alhamis bayan da kwamitin ya duba rahotannin binciken kuɗi da suka shafi kamfanin NNPCL.

    Kwamitin ya kuma yi gargaɗin cewa zai iya fitar da sammacin kama waɗanda abin ya shafa idan suka gaza bayyana a gaban kwamitin a ranar da za a sanar nan gaba.

    Sanata Wadada ya bayyana wannan matsaya ta kwamitin ne yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani bayan kammala taron kwamitin.

    A cewarsa, ana sa ran tsoffin shugabannin kamfanin za su bayyana tare da shugabancin kamfanin na yanzu ƙarƙashin jagorancin sabon Babban Darakta, Bayo Ojulari, da kuma masu binciken kuɗi na waje da suka yi aiki da kamfanin a lokacin da ake magana a kai.

  19. Ukraine ta ce Amurka ta nemi taimakonta kan yaƙin Iran

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce Amurka ta buƙaci ƙasarsa ta taimaka wajen kawar da hare-haren da ake kai wa yankin Gabas ta Tsakiya da jirage marasa matuƙa samfurin Shahed, ƙirar Iran.

    Ukraine na ƙera na’urori masu araha kuma masu tasiri sosai wajen kakkabo jiragen sama marasa matuƙa na kai hari, a ƙoƙarin da take na kare kanta daga ruwan bama-bamai da Russia ke yi mata.

    Wannan fasaha da ƙwarewar amfani da ita za su kasance masu amfani sosai ga ƙasashe wajen kare kansu daga hare-haren da Iran ke kaiwa a halin yanzu.

    Zelensky ya yi wa kawayen Amurka a Gabas ta Tsakiya tayin musayar na’urorin, inda shi kuma yake so su ba shi wasu daga cikin na’urorinsu na garkuwar hare-hare ta sama, waɗanda Ukraine ke buƙata.

  20. Yaƙin Iran: Amurka ta sassauta takunkumi kan man Rasha

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta sassauta takunkumin da ta sanya a kan man Rasha, bayan da farashin mai ya tashi saboda yakin na Iran.

    Ta ce za ta bar India ta rika sayen man na Rasha, amma wanda daman tuni yana jiragen ruwan dakon mai da ke teku.

    Ko wannan zai haifar da wani sauyi, wani abu ne na daban. Sakataren baitul-malin Amurkar, Scott Bessent, ya ce an yi hakan ne domin bayar da damar ci gaba da kai mai kasuwannin duniya.

    Ya kuma ce yana fatan Indiya za ta kara yawan man da take saya daga Amurka.

    Barazanar da Iran ta yi, ta kai hari kan jiragen ruwa da ke bi ta Zirin Hormuz, ta sa jirage daina bin yankin, inda ta nan ne ake safarar kashi daya bisa biyar na man duniya.