Bidiyon wasu jiragen yaƙin Amurka da aka lalata a Iran
Kafofin yaɗa labaran Iran sun wallafa wasu hotuna da bidiyo na tarkacen wasu jiragen da aka lalata a lokacin aikin neman matuƙin jirgin yaƙin Amurka na F-15 a Iran.
A cewar kafofin yaɗa labaran Amurka, a lokacin aikin ceton wasu jiragen jigilar mayaƙa biyu da ya kamata ya ɗauki kwamandoji da matuƙin jirgin zuwa wuri mai aminci sun fuskanci matsala.
Jaridar New Yorks Times ta ce kan haka ne ''sojojin Amurka suka lalata jiragen biyu domin kada su faɗa hannun dakarun Iran.''
To amma a cewar sansanin sojin sama na Khatam Al-Anbia na Iran ya ce dakarun ƙasar sun ''harbi jiragen maƙiya a kudancin Isfahan, ciki har da masu saukar ungulu biyu samfurin Black Hawk da kuma jirgin jigilar dakaru na C-130.