Bashir Tofa: Hotunan jana'izar tsohon dan takarar shugaban Najeriya

Bayanan hoto, An yi jana'izar tsohon dan takarar shugaban Najeriya Bashir Othman Tofa a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa a birnin Kano na Najeriya
Bayanan hoto, Dimbin mutane suka halarci jana'izar ciki har da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero
Bayanan hoto, Tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau da dattijo Uba Lida na cikin fitattun mutanen da suka halarci jana'izar
Bayanan hoto, Shi ma tsohon Ministan Harkokin Noma na Najeriya Alhaji Sabo Nanono ya halarci jana'izar
Bayanan hoto, An binne shi ne a tsakanin kabarin mahaifinsa da na mahaifiyarsa
Bayanan hoto, Mutane da dama sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai son ci gaban Najeriya da taimakon jama'a
Bayanan hoto, Bashir Tofa ya rasu da asubahin nan yana da shekara 74 a duniya