Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Liberia ta biya $71,000 kan maganin Covid-19 na bogi
Kasar Laberiya ta kashe $71,000 a matsayin kudin dakon wasu kananan katon-katon uku na maganin korona da aka hada a Madagascar, inji ma'aikatar lafiya ta kasar.
Bayyanar wannan labarin ya ja hankulan mutanen kasar, musamman bayan da ma'aikatar lafiya ta kasar ta sauya sanarwar da a baya ta fitar cewa ruwan maganin kyauta ce daga gwamnatin Madagascar, inda ta ce gwamntin Laberiya ta biya kudin jigilar maganin ne kawai wanda ke cikin wasu kananan katon-katon uku.
An kuma rika yada bidiyon lokacin da Shugaba George Weah ke karbar maganin a filin jirgin saman Monrovia shekara daya da ta gabata, a shafukan sada zumunta.
Zuwa wannan lokacin babu wanda ya tabbatar da sahihancin maganin duk da gwaje-gwajen da aka yi a sassan duniya daban-daban.
Kasar Madagascar, wadda a baya ta dogara kan wannan maganin nata, yanzu ta sauya taku - inda ta koma amfani da alluran riga-kafin da WHO ke samar wa.
Ba san ko gwamnatin Laberiya ta rabawa 'yan kasar maganin na Madagascar ba.
Wannan ne abin kunya na baya-bayan nan da ya dabaibaye gwmanatin Mista Weah kan yadda ta ke watanda da kudaden al'ummar kasar.