Abiola Ajimobi: Wasu zaɓaɓɓun hotunan rayuwarsa

A ranar Alhamis ne Allah Ya yi wa tsohon gwamnan rasuwa. BBC ta zabo wasu daga cikin hotunansa lokacin da yake raye.

Asalin hoton, twitter/Ajimobi

Bayanan hoto, Abiola Ajimobi a wajen wani taro a birnin Ibadan na jihar Oyo

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Ajimobi yana jawabi yayin da yake kan kujerar gwamnan Jihar Oyo

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Abiola Ajimobi tare da matarsa, wadda ta ce ba ta fiya tunaninsa ba yayin da suke yaƙin neman zaɓe a tutar jam'iyyar APC

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Cif Ajimobi kenan lokacin da ya haɗa wata cashiya a yankin Scotland na Birtaniya

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Ajimobi tare da Shugaba Muhammadu Buhari, a Fadar Aso Rock Villa da ke Abuja

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Abiola Ajimobi tare da tsohon gwamnan Ekiti, Fayose

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Ajimobi tare da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a wurin wani taron ƙara wa juna sani

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Ajimobi kenan tare da sarakunan Jihar Oyo a birnin Ibadan

Asalin hoton, twitter/Ajimobi

Bayanan hoto, Abiola Ajimobi tare da tsohon gwamnan Oyo, Alao Akala

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Ajimobi tare da ɗaya daga cikin sarakunan gargajiyar Jihar Oyo a Ibadan

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Abiola Ajimobi tare da jagoran jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Ajimobi tare da Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, waɗanda dukansu 'yan jam'iyyar APC ne mai mulkin Najeriya

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Gwamna Abiola Ajimobi tare da tsofaffin 'yan ƙwallon Najeriya: Joseph Yobo, Daniel Amokachi, Mutiu Adepoju yayin bikin ranar haihuwarsa

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Ajimobi tare da Shugaba Buhari da kuma Adams Oshiomole, shugaban APC na ƙasa da kotu ta sauke daga muƙaminsa a makon nan

Asalin hoton, Twitter/ajimobi

Bayanan hoto, Sanata Ajimobi tare da Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Adams Oshiomhole

Asalin hoton, Twitter/abiola ajimobi

Bayanan hoto, Ajimobi tare da Gwamnan Oyo na yanzu, Seyi Makinde.