An sace dalibai mata shida a jihar Kaduna

Asalin hoton, Kaduna State Government

Bayanan hoto, "Maharan sun shiga makarantar ne ta bangaren da katangar makarantar ta rushe"

Wasu 'yan bindiga sun sace wasu dalibai mata su shida a makarantarsu a jihar Kaduna, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Bayanai sun ce an yi awon gaba har da malaman makarantar mai zaman kanta su biyu a lokacin da 'yan bindigar suka shiga makarantar a cikin daren Laraba.

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan ya tabbatarwa da BBC faruwar al'amarin.

Mista Aruwan ya ce abin ya faru ne a makarantar Engravers College wadda take kauyen Kakau a karamar hukumar Chikun - makarantar tana da nisan kilomita 10 daga kamfanin mai na NNPC da ke Kaduna.

Har wa yau, Aruwan ya ce "sai bayan kammala bincike ne za a iya tabbatar da abin da ya faru."

Hazalika jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar DSP Yakubu Sabo ya ce jami'ansu sun bazama cikin daji domin neman "mutum takwas din da aka sace a makarantar."

Ya kuma ce maharan sun shiga makarantar ne ta bangaren da katangar makarantar da ta rushe.

"An tura jami'an tsaro makarantar domin kwantar wa da sauran dalibai hankali," in ji shi.