Zainab Aliyu: Kalli hotunan zanga-zangar neman sakin budurwar

Da safiyar ranar Talata ne dalibai a birnin Kano akasari na jami'ar Yusuf Maitama Sule suka fito zanga-zanga a birnin don neman a saki abokiyar karatunsu da ke tsare a kasar Saudiyya.

Bayanan hoto, Da safiyar ranar Talata ne dalibai a birnin Kano akasari na jami'ar Yusuf Maitama Sule suka fito zanga-zanga a birnin

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Suna zanga-zangar ne don kiran da a yi wa abokiyar karatunsu Maryam Aliyu adalci, wadda jami'an tsaro suka tsare a Saudiyya bisa zargin safarar kwayar Tramadol zuwa ciikin kasar.
Bayanan hoto, An kama Zainab jim kadan bayan isarsu kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umara tare da mahaifiyarta Maryam da 'yar uwarta Hajara
Bayanan hoto, Hukumomi a Najeriya sun ce Zainab ba ta da laifi domin wasu ne suka saka mata kwayar a wata jaka kuma suka makala sunanta a jiki
Bayanan hoto, Kwalin da ke hannun wadannan yana cewa ne: "Muna kira ga hukumomin Najeriya da su mika wadanda suka saka wa Zainab kwaya ga Saudiyya a madadain Zainab din".
Bayanan hoto, Tuni hukumar NDLEA ta ce ta kama mutum shida wadanda ake zargi da hannu wajen jefa Zainab wannan hali da take ciki
Bayanan hoto, Daliban sun fara zanga-zangar ne daga harabar jami'ar, inda suka hau tituna da ke makwabtaka da ita
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun je har gaban karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke jihar Kano