Hotunan ziyarar da Buhari ya kai Bauchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi domin jajantawa wadanda gobarar da aka yi a kasuwar garin Azare ta shafa da kuma bala'in guguwa a jihar.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Shugaban ya isa jihar da ke arewa maso gabashin kasar ne a ranar Alhamis da safe.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne aka yi wata mummunar guguwa a jihar wacce ta yi sanadin mutuwar mutum tare da jikkata wasu da dama, ta kuma lalata dukiyoyi.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Bayan wannan iftila'i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum a ranar Lahadi da daddare.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Bayan da ya sauka a garin Bauchi, shugaban ya wuce garin Azare ne inda ya fara kai ziyara fadar Sarkin Katagum kafin ya kai ziyara kasuwar Azare.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Dubban magoya bayan shugaban ne suka yi masa maraba.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Wani magoyin bayan shugaban rike da hotonsa cikin annashuwa.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Wadansu mata magoya bayan shugaban lokacin da suke kukan farin ciki bayan yin tozali da shugaban.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, An tsaurara tsaro a wuraren da shugaban ya ziyarta.

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Gobarar ta jawo asarar dumbin dukiya da kawo yanzu ba a tantance adadinta ba.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da Shugaba Buhari ke da goyon baya sosai