Hotunan bikin Ranar Mata ta 2018 a sassan duniya

Kalli wasu zababbun hotuna daga sassan duniya daban-daban na yadda aka gudanar da bikin Ranar Mata ta 2018.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata sun shiga yajin aiki a Spain a yau ranar mata ta duniya inda suka fito suna kiran a ba su hakki daidai da maza a wuraren aiki.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Domin bikin ranar Mata ta duniya an yi wasan kwaikwayo a Karachi na Pakistan inda aka nuna yadda Maza ke azabtar da Mata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Rasha ma mata sun hada gangami a Saint Petersburg kan kare hakkinsu albarkacin ranar Mata ta duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata a Iraqi sun yi tseren gudun mita 900 domin bikin ranar Mata ta duniya a birnin Mosul da dakarun kasar suka kwato daga hannun mayakan IS.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gangamin Mata a Turkiyya inda wasu suka rike sako mai cewa " Mata ne za su tabbatar da zaman lafiya".

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata sun yi gangamin tabbatar da 'yancinsu a London a ranar Mata ta duniya.

Asalin hoton, Aliyu Dahiru Facebook

Bayanan hoto, A Najeriya kuma, wasu mata ake wayarwa da kai kan fasahar sadarwa ta zamani a Ranar Mata Ta Duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dalibai 'yan mata sun halarci babban bikin ranar Mata ta duniya da aka gudanar a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Falasdinawa dalibai 'Yan Mata a Gaza sun yi bikin ranar Mata ta duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata a Thailand sun gudanar da bikinsu a tsohon gari Chiang Mai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gudanar da taro a sassan duniya domin bikin ranar Mata ta duniya da ake gudanarwa a duk ranar 8 ga Maris. 'Yan rajin kare hakkin mata a Somalia sun yi taro a Mogadishu kuma sun rike sako ne mai taken "A kare Mata da yara kanana a Somalia."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata 'yar India ta fito aikinta na ma'adinin Kwal a Dhanbad da ke gabashin kasar duk da yau ce ranar Mata ta duniya.