Hotunan zanga-zangar adawa da kasafin kudi a Nijar

Kungiyoyin fararen hula na adawa da kasafin kudin na 2018 saboda, abin da suka kira takurawa talaka.

Bayanan hoto, Kungiyoyin farar hula sun ce ba su gamsu da kudurin kasafin kudin 2018 na Jamhuriyar Nijar ba.
Bayanan hoto, Kungiyoyi na da karfin iko sosai a kasar.
Bayanan hoto, Wannan ne karo na hudu da kungiyoyin ke fitowa dan nuna kin amincewarsu ga kasafin kudin shekarar 2018.
Bayanan hoto, Sun yi tur da shirin da gwamnati ke yi na karbar wani kaso a cikin kudin magada.
Bayanan hoto, Kungiyoyin sun yi gangamin ne tare da hadin gwiwar jam'iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar.
Bayanan hoto, 'Yan majalisar dokokin sun ce za su duba batun.
Bayanan hoto, 'Yan kasar ta Nijar sun sha kokawa kan matsin halin rayuwa.
Bayanan hoto, Kasar na fama da matsalolin rashin tsaro.
Bayanan hoto, Masu gangamin sun ce ba za su daina fafutika ba sai bukatunsu sun biya.