Hotunan yadda mata suka fara zuwa kallon kwallo a Saudiyya

A karon farko mata sun fara shiga filayen wasanni don kallon kwallon kafa a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahli sun yi jerin gwano a wajen filin wasa na Sarki Abdallah da ke birnin Jeddah ranar Juma'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matakin barin mata su fara zuwa filayen wasanni yana cikin sauye-sayen da mai jiran gadon sarautar Saudiyya Yarima Mohammed bin Salman ya yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata uwa tana yi wa diyarta kwalliya a fuska a wajen filin wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dimbin mata ne suka rika tururuwa don shiga filin wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magidanta da dama ne suka halarci filin wasan tare da iyalansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyoyin kwallon kafa na Al-Batin da Al-Ahli ne suka nishadantar da 'yan kallon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A bara ne hukumomi a kasar suka amince da bai wa mata izinin fara tuka mota da kansu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A karshen wasan kungiyar Al-Ahli ce ta samu nasara a kan Al-Batin da ci 5-0