Tunisia: Ana zanga-zangar kan tashin farashin magani
Asalin hoton, Reuters
An kama mutane fiye da 300 a kasar Tunisiya ranar Laraba daddare, game da zanga-zangar kin jinin gwamnati da yan kasar suke yi.
'Yan sanda sun sa wa mutanen da zanga-zanga kan tashin frashin kayayyakin masarufi hayaki mai sa hawaye.
An kai sojoji garurruwa daban-daban a kasar domin kare gine ginen gwamnati inda masu zanga-zangan suke.
Firayim ministan kasar, Youssef Chahed, ya nuna bacin rai game da lalata kayan gwamnati da masu zanga-zangar suke yi, yana mai cewa suna kokarin karya gwamnati ne.
Mene ne makasudin zanga-zanzar?
An gudanar da zanga-zangar a akalla wurare 10 a fadin kasar ciki har da birnin Tunis.
A makon da ya gabata ne aka fara zanga-zangar cikin lumana, amma a ranar litinin da yamma zanga-zangar ta zama ta tashin hankali, inda aka kama mutane kusan 600 tunda aka fara tashin hankalin a makon ya gabata.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida, Khelifa Chiban, ya fada wa kafafan watsa labarai cewa an kama mutane fiye da 300 a ranar Laraba kawai.
Asalin hoton, Reuters
Daya daga cikin masu zanga-zangar ya fada wa BBC cewa suna yin zanga-zangar ne dan tsadar rayuwa a kasar.
''Kudin magani ya karu, har da komai ma, amma ba'a kara albashi ba. Ba na jin yanzu ne lokacin da komai zai yi tsada."
Ana shirin yin wata gagarumar zanga-zangar a ranar jumma'a.
Masu zanga zangar suna bukatar gwamnatin ta soke kasafin kudin 2018, wanda kungiyoyin 'yan adawa suka ce yana cike da rashin adalci.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai