Hotunan zanga-zanga kan Birnin Kudus a fadin duniya

A ranar Juma'a ne dubun-dubatar mutane a kasashe daban-daban a fadin duniya suka gudanar da zanga-zangar adawa da matakin Shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

Bayanan hoto, Rikici tsakanin Yahudawa da Falasdinawa ya barke sakamakon matakin Donald Trump mai cike da ce-ce-ku-ce na mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikici ya barke ne a Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye da kuma Zirin Gasa, inda aka kashe wani Bafalasdine daya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun Isra'ila sun yi arangama da Falasdinawa a biranen Bethlehem da Ramallah da Hebron da Nablus a Yammacin Kogin Jordan, da ma wasu kananan wuraren.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane a birnin Berlin na Jamus sun taru a gaban Brandenburg Gate suna daga tutocin Falasdinu da Turkiyya don nuna adawa da matakin shugaban Amurka Donald Trump na mayar da Kudus babban birnin Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum dubu bakwai ne wadanda mafi yawansu musulmai ne suka halarci zanga-zangar a Jamus.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A kasar Amman ma masu zanga-zanga sun mamaye ofishin jakadancin Amurka da ke kasar don nuna adawarsu da lamarin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Tunisiya ma ba ta sauya zani ba, don masu zanga-zanga sun yi ta kona tutocin Amurka da Isra'ila a yankin Habib Bourguiba da ke Tunis babban birnin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Falasdinawa sun yi fito-na-fito da dakarun Isra'ila a kofar Damascus da ke Tsohon Birnin Kudus a ranar da suka kira 'Ranar nuna fushi' kan matakin Mista Trump.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka yi tururuwa a yayin zanga-zangar adawa da matakin na Trump a Istanbul, babban birnin Turkiyya, dauke da tutocin Falasdinu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Masar ma zancen iri daya ne. Masu zanga-zanga sun yi ta kona tutocin Amurka da na Isra'ila a masallacin Al-azhar da ke birnin Alkahira duk don nuna fushinsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wasu kasashen bakaken fata na Afirka ma kamar su Somaliya, mutane sun fito zanga-zanga dauke da hoton masallacin Kudus a Mogadishu babban birnin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmai a Malaysia sun bi sahun takwarorinsu na sauran kasashen duniya wajen yin wannan zanga-zanga, inda suka mamyi ofishin jakadancin Amurka a Kuala Lumpur a ranar Juma'a, suna cewa matakin na Trump cin fuskar Musulmai ne.