Kalli hotunan bikin Gasar Hikayata ta BBC ta bana

Gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai a bana.

Bayanan hoto, Maimuna da Balkisu da Habiba da kuma Hindatu wadanda suka lashe Gasar Hikayata ta shekarar 2017
Bayanan hoto, An gudanar da bikin karrawar ne a otel din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ranar Juma'a
Bayanan hoto, Wannan ne karo na biyu da BBC ta sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla
Bayanan hoto, Bikin ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Najeriya
Bayanan hoto, Shugaban Sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh yayin da yake gabatar da jawabi a zauren taron
Bayanan hoto, Shugaban ya ce ana aikin yin wani kundi wanda za a wallafa kuma zai kunshi labarai da suka yi zarra a bara da kuma bana
Bayanan hoto, Bikin ya samu halartar tsohon Shugaban Sashen Hausa na BBC Mansur Liman
Bayanan hoto, A bara ne aka fara kirkiro Gasar Hikayata ta mata zalla
Bayanan hoto, Maimuna Idris Sani Beli, wadda ta zama gwarzuwar gasar a bana, ta samu lambar yabo da kuma $2,000
Bayanan hoto, Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu, kuma ta samu lambar yabo da dala $1,000
Bayanan hoto, Habiba Abubakar da kuma Hindatu Sama'ila Nabame Argungu (daga dama), wadanda suka yi na uku, sun samu lambar yabo da $500