Kalli hotunan yadda makiyaya suka yi da dokar hana kiwo a Benue

BBC ta hada hotunan yadda makiyaya suka tinkari kaddamar da dokar hana kiwon-sake a jihar Benue.

Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Benue ta ce ta kaddamar da dokar hana kiwon-sake ne domin ta dakile rikice-rikicen da ake samu tsakaninsu da makiyaya
Bayanan hoto, Dokar dai ta tanadi dauri ko tara da ga duk wanda ya saba mata ta hanyar yawo da dabbobi a kasa
Bayanan hoto, Wasu makiyaya dai sun kai karar gwamnatin jihar Benue kotu suna masu cewa dokar ta take hakkin 'yan Adam
Bayanan hoto, Wasu makiyayan dai suna kalubalantar dokar ta hanyar fita da dabbobinsu kiwo
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar ta Benue dai ta ce yanzu akwai wasu masu kiwo da suka fara bin dokar
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Benue dai ta ce dokar ta fara rage yawan rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma
Bayanan hoto, Makiyaya dai suna kokawa cewa samun wurin tsugunar da dabbobi zai yi tsada
Bayanan hoto, Wasu makiyaya suna ganin dokar za ta hana su walwala
Bayanan hoto, Ita kuma gwamnatin jihar tana neman makiyayan su fahimce ta