Nigeria: Kalli hotunan yadda aka yi hawan Daushe a Zaria

A ci gaba da bukukuwan Babbar Sallah, BBC ta tattaro muku jerin hotunan Hawan Daushen da aka gudanar ranar Lahadi a birnin Zariya da ke Arewacin Najeriya.

Bayanan hoto, Bushe-bushen kakaki da algaita muhimmin bangare ne na hawan sallah a arewacin Najeriya
Bayanan hoto, Wadansu mata akan dawaki yayn hawan
Bayanan hoto, Ayarin mafarauta da suka halarci hawan
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai tare da Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris yayin hawan
Bayanan hoto, Wani mai wasa da wuta yayin da yake nishadantar da 'yan kallo
Bayanan hoto, Dimbin mutane ne suka halarcin hawan
Bayanan hoto, Hawan shi ne babban hanyar da jama'a suke samun yin tozali da Sarkin Zazzau lokacin bikin sallah