Hotunan ganawar Osinbajo da shugabannin Igbo

A ranar Laraba ne mukaddashin shugaban Najeirya Yemi Osinbajo ya gana da shugabannin al'ummar Igbo a fadar gwamnati a Abuja, to ko me ya gaya musu?

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, A ci gaba da ganawarsa da shugabannin al-umma daga sassa daban-daban na Najeriya kan yadda za a magance matsalar kalaman kiyayya, mukaddashin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gana da shugabannin al'umma daga yankin Kudu maso gabashin kasar a ranar Laraba.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Osinbajo ya ce tashin hankali da yaki ba zai taimaka wa kowa ba, saboda shi yaki yana da saukin farawa amma da wahala a gama shi har abada.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Osinbajo ya ce dole shuwagabannin su fito su yi tir da kalaman kiyayya da ke faruwa tsakanin al'ummominsu.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Mukaddashin shugaban Najeriyar ya ce babu shakka game da kudurin gwamnati na hukunta duka masu kalaman kiyayya da rarrabuwar kai.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Farfesa Osinbajo ya ce wannan ba lokacin da za a buya karkashin kabila ko addini ba wajen nuna goyon baya ga kalaman da ke rarraba kawunan al'umma.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Taron ya samu halartar shuwagabanni daga yankin kudu maso gabashin kasar da kuma manyan jami'an gwamnati.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Ba a bar mata a baya ba a cikin mahalarta taron, kuma Farfesa Osinbajo ya ce a ranar Litinin zai gana da dukkan shugabannin addinai da manyan kabilun kasar.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Shuwagabbin majalisar dokokin Najeriya ma sun halarci zaman taron.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ce-ce-ku-ce ke dada kamari dangane da fafatukar kafa kasar Biafra da wasu 'yan kudu maso gabashin kasar ke yi.

Asalin hoton, Sunday_Aghaeze@ 2017

Bayanan hoto, Mukaddashin shugaban Najeriya ya bayyana wa shuwagabannin yankin bukatar da ke akwai na wanzuwar zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.