Indonesia: Za a yi wa 'yan luwadi bulala 85 a bainar jama'a
Asalin hoton, AFP
Wata kotun shari'ar Musulunci ta lardin Aceh, a kasar Indonesiya, ta yankewa wasu maza biyu hukuncin bulala 85 a bainar jama'a a kan kama su da laifin yin luwadi.
An kama mutanen ne da laifin karya dokar shari'ar Musulunci wadda ake girmamawa a lardin Aceh, inda za a yi wa ko wannen su bulala 85.
'Yan sintiri ne suka kama mutanen a kan gado tare, a wannan watan na Mayu. Daya dann shekara 20 ne dayan kuma dan shekara 23, sai dai ba a bayyana sunayensu ba.
A lardin Aceh ne kawai aka fi tabbatar da aiki da dokokin shari'ar Musulunci a kasar.
Za a yi musu hukuncin ne a mako mai zuwa.
A baya ana yi wa mutane bulala a bainar jama'a ne kawai a bisa kama su da laifin shan giya da caca.
A shekarun baya-bayan nan ne, lardin Aceh ya kara kaimi wajen ra'ayin mazan jiya. A shekarar 2014 ne aka gabatar da tsauraran dokoki a kan masu aikata luwadi, kuma dokar ta fara aiki a shekarar da ta biyo baya.
Asalin hoton, AFP
A cewar kamfanin dillanci labarai na AFP, Alkali Khairil Jamal ya shaida wa kotu cewa, "Mutanen sun tabbatar da cewa sun aikata laifin luwadi".
A lokacin da aka yanke wa mutanen hukunci, sun rufe fuskokinsu da hannayensu.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na masu fafutuka sun yi Allah-wadai da hukuncin da suka kira 'tsattsaura'.
Gabannin yanke hukuncin, kungiyar kare hakkin bil adam ta 'Human Rights Watch', ta yi kira ga kasar, da a saki mutanen, inda ta ke cewa, "Hukuncin zai kara sa fargaba a tsakanin masu fafutukar kare 'yan luwadi da madugo, ba wai a Aceh kawai ba har ma da wasu wuraren da dama, musamman a lardunan masu 'tsattsauran' ra'ayi na kasar.
Za a yi wa mutanen bulala a lokacin da za a gudanar da wani biki a ranar 23 ga watan Mayu, a lardin birnin Banda Aceh, inda masu sintiri suka kama su.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce, kyamar luwadi na karuwa a kasar.
Tun sama da shekara goma da ta gabata, aka bai wa lardin Aceh dama ta musamman don gabatar da dokokin shari'ar Musulunci nata na kanta.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai