Ina neman gafarar Rahama Sadau — Classiq

Bayanan hoto, MOPPAN ta ce rungumar Classiq da Rahama Sadau ta yi ta saba da ka'idojin kungiyar

Mawakin nan mai suna Classiq wanda ya yi waka tare da rungume-rungume da Rahma Sadau, ya ce, yana neman afuwar jarumar.

Mawakin, a shafinsa na Instagram, ya ce "fitowar faifan wakarsa da ya yi wa lakabi da 'i love you' ta jawo kace-nace."

A saboda haka ne Classiq ya ce " zan so na nemi gafarar Rahma Sadau saboda irin halin da wakata ta jefa a ciki."

Classiq ya kara da neman afuwar masoya Rahama Sadau.

To amma mawakin ya bayyana jarumar da mai hazaka da jajircewa, a inda ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kasancewa tare da Rahma Sadau.

A 'yan makonnin da suka gabata ne dai kungiyar masu hada fina-finan Hausa wato MOPPAN, ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkokin fim.

Bayanan hoto, Rahama Sadau da Classiq sun nuna shaukin sosayya a wakar
Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da ta fito a wakar turanci