PSG ce kaɗai za ta iya sayen Osimhen - De Laurentiis
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Napoli Aurelio De Laurentiis ya ce PSG ne kadai kulob guda daya kacal a duniya da ke da kuɗin da za ta iya ɓanɓare Victor Osimhen daga Stadio Diego Armando Maradona a bazaran nan.
Napoli ta yi sayo Osimhen mai shekaru 21 a shekara ta 2020 bayan dan Najeriyar ya shafe kaka daya kacal yana buga wa Lille a kan farashin yuro miliyan 70.
Amma kwalliya ta biya kuɗin sabulu, ganin Osimhen ya ci kwallaye 28 a kakar wasanni biyu na farko sannan ya ci 31 a karo na uku.
Kusan 26 daga cikin wadancan kwallayen sun zo ne a gasar Seria A yayin da Napoli ta samu Scudetto na farko cikin shekaru 33 da suka gabata.
Amma rawar da Osimhen ke takawa a Napoli ya jawo hankalin wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa na turai, inda Chelsea da Manchester United da Real Madrid ke buƙatar sabon mai buga gaba.
De Laurentiis, wanda aka sani a duk faɗin duniyar ƙwallon ƙafa a matsayin mutum mai tsattsauran ra'ayi, ya dage a kan cewa Osimhen ba zai bar Napoli ba sai dai in ya sami wani gagarumin tayi kuma ya ce a halin yanzu PSG ne kadai ƙungiyar da ke da kwatankwacin kudin da ake bukata don sayen ɗan wasan.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai