Hotunan yadda ƴan Ukraine ke fama da karancin ruwan famfo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun a ranar Litinin mutane a Kyiv, babban birnin Ukraine suka fara bin layin ɗiban ruwa saban da hare-haren Rasha suka lalata cibiyoyin samar da ruwan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magajin garin birnin na Kyiv Vitaliy Klitschko ya ce kasi 40% na mazauna birnin ba su da ruwa sannan babu wuta a gidaje 270,000.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane sun yi ta bin dogwayen layuka a fadin birnin don ɗiban ruwa a famfunan da ke kan hanya bayan da na gidajensu suka lalace.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kashi 80 cikin 100 na mazauna birnin Kyiv ba su da ruwan sha tun bayan kai hare-haren.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wataƙila wannan yanayi da al'ummar birnin suka samu kansu a ciki shi ne karo na farko da suka ga hakan, saboda yadda aka san yankin Turai ya wadata da abubuwan more rayuwa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumomin Ukraine sun ce suna bakin ƙoƙarinsu don shawo kan lamarin.