Yadda aka zargi ƴansanda da ƙona gidaje da dukiya a jihar Kano

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Al'ummomin wasu garuruwa a yankin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, da ke Najeriya, sun zargi 'yansanda da kone musu gidaje da wuraren sana'a da kayan abinci da kuma dabbobi a sanadiyyar wata hatsaniya kan mallakar gonaki.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan wani samamen dare wanda ya kai ga arangamar da aka kashe ɗansanda tsakanin mutanen ƙauyukan da jami'an tsaron, a ranar Alhamis 26 ga watan nan na Maris, 2026, da daddare.

Rikicin dai wanda yanzu haka yake gaban shari'a, na da alaƙa da batun mallakar gonakin wata fadama a yankin Wudil da Bunkure.

Al'ummar ƙauyukan Katai da Faudan da Gaba-Gaɗi a Karamar Hukumar Wudil, sun zargi 'yan sandan da ƙone musu gidaje da gonakinsu, tare da jikkata wasu mazauna ƙauyukan, lokacin da suka kai samame domin kama wani mutum, inda mutanen garuruwan suka ce ba za a tafi da shi ba.

A kan haka bayanai suka ce lamarin ya kai ga sa-in-sa, inda har aka yi harbe-harbe, aka kuma lakaɗa wa wani ɗansanda duka, wanda ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Duk wani ƙoƙari da BBC ta yi na ji daga bakin ƙaramar hukumar Wudil kan wannan lamari, ya ci tura, domin mahukuntan sun ƙi cewa komai.

Sai dai wata majiya a yankin ta shaida wa, wakilinmu cewa rikicin gonakin da ke tsakanin Wudil da Bunkure, ya shafe tsawon shekara 20 ba a iya warware shi ba.

Majiyar ta kuma ce washegari ne, ranr Juma'a, 'yansanda suka koma ƙauyukan, inda suka tarar tuni mutane sun tsere, nan take a cewar majiyar suka riƙa bi wuri-wuri suna shaida sunayen mutane kuma suna fito da dukiya da kadarorinsu suna ƙonawa

Shi ma kakakin rundunar 'yansandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa da wakilin namu ya tuntube shi kan lamarin da kuma zarge-zargen da ake yi wa 'yansandan, ya ce za su fitar da sanarwa, wadda har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton BBC ba ta ji daga gare shi ba.

Haka su ma hukumomin jihar Kano ba su ce komai ba kan lamarin.