Super Eagles ta yi tuntuɓe a wasanta da Lesotho
Asalin hoton, NFF/X
Najeriya ta fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 da tuntuɓe inda ta yi kunnen doki da Lesotho 1-1.
A minti na 56 ne Lesotho ta fara jefa ƙwallo a ragar Super Eagles a wasansu na rukunin C a filin wasan Godswill Akpabio da ke Uyo, jihar Akwa Ibom ranar Alhamis.
Amma mintuna 11 bayan haka, mai tsaron baya Semi Ajayi ya farkewa Najeriya.
A ranar Lahadi ne Super Eagles za ta kara da Zimbabwe a filin wasa na Huye da ke Butare, a wasan da ya zame wa Najeriya dole ta yi nasara idan har tana son kara haskaka damarta ta samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai
{{rankTranslation}}