Zaben 2019: Hotunan wasu zababbun gwamnonin Najeriya

BBC Hausa ta tattaro maku hotunan wasu 'yan takarar gwamna da suka sami nasara a zabukan gwamnoni da aka yi a Najeriya ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019.

Asalin hoton, Facebook / Dapo Abiodun

Bayanan hoto, Dapo Abiodun na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar jihar Ogun. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.

Asalin hoton, Twitter / @jidesanwoolu ‏

Bayanan hoto, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar Legas. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.

Asalin hoton, Twitter / @Ben_Ayade

Bayanan hoto, Ben Ayade na jam'iyyar PDP ne zababben gwamnan jihar Cross River. Ya ci zaben ne a karo na biyu.

Asalin hoton, Facebook / Inuwa Yahaya

Bayanan hoto, A Gombe kuwa Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC ne wanda ya lashe zaben gwamnan jihar. Ya doke Sanata Bayero Nafada wadanda duk suka nemi takarar a karon farko.

Asalin hoton, Twitter / @GovNiger

Bayanan hoto, Abubakar Sani Bello na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Neja. Ya yi nasara ne a karo na biyu.

Asalin hoton, Twitter / @RealAARahman

Bayanan hoto, Sai kuma jihar Kwara inda Abdulrahman Abdulrazaq na APC ya sami nasara a zaben gwamnan jihar. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.

Asalin hoton, Facebook / David N Umahi

Bayanan hoto, David Nweze Umahi dan jam'iyyar PDP shi ne zababben gwamnan jihar Ebonyi. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamna.

Asalin hoton, Facebook / Muh Badaru

Bayanan hoto, A jihar Jigawa Muhammadu Badaru na APC ne zababben gwamnan jihar. Badaru ya yi nasara ne a karo na biyu.

Asalin hoton, Twitter / @El-Rufai

Bayanan hoto, Mallama Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ne zababben gwamnan jihar

Asalin hoton, Twitter / @SeyiMakinde

Bayanan hoto, A jihar Oyo kuwa, Seyi Makinde na PDP ne ya lashe zabenn gwamna a jihar

Asalin hoton, Facebook / Udom Emmanuel

Bayanan hoto, A jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben mukamin gwamnan jihar