An yi zanga-zanga kan auren jinsi daya a Australia
Asalin hoton, Getty Images
Daruruwan masu goyon bayan auren jinsi daya Australia sun yi zanga-zanga domin bijirewa yunkurin gudanar da kuri'ar raba-gardama kan batun.
Gwamnatin kasar dai tana so a yi zaben raba-gardaman ne a watan Fabrairu kan ko a hana ko kuma a amince da aure jinsi daya.
Sai dai masu zanga-zangar -- wadanda suka mamaye titunan biranen Sydney da Melbourne -- suna so majalisar dokokin kasar ta amince a rika auren jinsi daya.
Australia na daya daga cikin kasashe masu arziki da suka haramta auren jinsi daya.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai
{{rankTranslation}}