Bayanan juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka cikin sama da shekara 70

An samu kusan juyin mulki 130 da suka yi nasara, a cikin ƙasashen Afrika 36, tun 1952 lokacin da Sarki Farouk na Masar ya zama shugaban wata ƙasa a Afirka na farko da aka hamɓarar.

Shugabannin da aka hamɓarar

An tsara shi daga kan na baya-bayan nan zuwa wanda aka jima da yin su
  • Ali Bongo

    Shugaban ƙasa Gabon Gabon
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohamed Bazoum

    Shugaban ƙasa Nijar Nijar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Paul-Henri Sandaogo Damiba

    Shugaban riƙon ƙwarya Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Rocha Kabore

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Abdalla Hamdok

    Firaminista Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Alpha Condé

    Shugaban ƙasa Guinea Guinea
    Karanta ƙarin bayani...
  • Bah N'daw

    Shugaban ƙasa Mali Mali
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ibrahim Boubacar Keita

    Shugaban ƙasa Mali Mali
    Karanta ƙarin bayani...
  • Omar al-Bashir

    Shugaban ƙasa Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Robert Mugabe

    Shugaban ƙasa Zimbabwe Zimbabwe
    Karanta ƙarin bayani...
  • Blaise Campaore

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohamed Mohamed Morsi

    Shugaban ƙasa Masar Masar
    Karanta ƙarin bayani...
  • François Bozizé Yangouvonda

    Shugaban ƙasa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Amadou Toumani Toure

    Shugaban ƙasa Mali Mali
    Karanta ƙarin bayani...
  • Muammar Gaddafi

    Shugaban ƙasa Libya Libya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Laurent Gbagbo

    Shugaban ƙasa Ivory Coast Ivory Coast
    Karanta ƙarin bayani...
  • Hosni Mubarak

    Shugaban ƙasa Masar Masar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Zine el Abidine Ben Ali

    Shugaban ƙasa Tunisiya Tunisiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mamadou Tandja

    Shugaban ƙasa Nijar Nijar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Kaftin Moussa Dadis Camara

    Shugaban ƙasa Guinea Guinea
    Karanta ƙarin bayani...
  • Marc Ravalomanana

    Shugaban ƙasa Madagascar Madagascar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Aboubacar Somparé

    Shugaban ƙasa Guniea Guinea
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sidi Ould Cheikh Abdallahi

    Shugaban ƙasa Mutaniya Murtaniya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Maaouya Ould Sid' Ahmed Taya

    Shugaban ƙasa Murtaniya Murtaniya
    Karanta ƙarin bayanai...
  • Fradique de Menezez

    Shugaban ƙasa Sao Tome da Principe Sao Tome da Principe
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ange-Felix Patasse

    Shugaban ƙasa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Henri Konan Bédié

    Shugaban ƙasa Ivory Coast Ivory Coast
    Karanta ƙarin bayani...
  • Joao Bernardo Vieira

    Shugaban ƙasa Guinea-Bissau Guinea-Bissau
    Karanta ƙarin labarai...
  • Tadjidine Ben Said Massonde

    Shugaban ƙasa Komoros Komoros
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ibrahim Bare Mainassara

    Shugaban ƙasa Nijar Nijar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Johnny Paul Koroma

    Shugaban ƙasa Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Pascal Lissouba

    Shugaban ƙasa Kongo Kongo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ahmad Tejan Kabbah

    Shugaban ƙasa Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mobutu Sese Seko

    Shugaban ƙasa DR Congo DR Congo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sylvestre Ntibantunganya

    Shugaban ƙasa Burundi Burundi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohammed Farrah Aidid

    Shugaban ƙasa Somaliya Somaliya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mahamane Ousmane

    Shugaban ƙasa Nijar Nijar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Valentine Strasser

    Shugaban ƙasa Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohamed Said Djohar

    Shugaban ƙasa Komoros Komoros
    Karanta ƙarin bayani...
  • Miguel Trovoada

    Shugaban ƙasa Sao Tome da Principe Sao Tome da Principe
    Karanta ƙarin bayani...
  • Dawda Kairaba Jawara

    Shugaban ƙasa Gambiya Gambiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ernest Shonekan

    Shugaban ƙasa Najeriya Najeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Joseph Momoh

    Shugaban ƙasa Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Chadli Bendjedid

    Shugaban ƙasa Aljeriya Aljeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Justin Lekhanya

    Shugaban ƙasa Lesotho Lesotho
    Karanta ƙarin bayani...
  • Moussa Traore

    Shugaban ƙasa Mali Mali
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohamed Siad Barre

    Shugaban ƙasa Somaliya Somaliya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Hissène Habré

    Shugaban ƙasa Chadi Chadi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Samuel Doe

    Shugaban Mulkin Soji Laberiya Laberiya
    Karanta ƙarin labarai...
  • Ahmed Abdallah Abderemane

    Shugaban ƙasa Komoros Komoros
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sadiq al-Mahdi

    Firaminista Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Habib Bourguiba

    Shugaban ƙasa Tunisiya Tunisiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Thomas Sankara

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Labarai masu alaƙa...
  • Jean-Baptiste Bagaza

    Shugaban ƙasa Burundi Burundi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Tito Lutwa Okello

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Leabua Jonathan

    Firaiminista Lesotho Lesotho
    Karanta ƙarin bayani...
  • Muhammadu Buhari

    Shugaban ƙasa Najeriya Najeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Milton Obote

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Gaafar Muhammad al-Nimeiry

    Shugaban ƙasa Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mohamed Khouna Ould Haidalla

    Shugaban ƙasa Murtaniya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Louis Lansana Beavogui

    Shugaban riƙon ƙwarya Guinea Guinea
    Karanta ƙarin bayani...
  • Shehu Shagari

    Shugaban ƙasa Najeriya Najeriya
    ...
  • Jean-Baptiste Ouedraogo

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Saye Zerbo

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Goukouni Oueddei

    Shugaban ƙasa Chadi Chadi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Hilla Limann

    Shugaban ƙasa Ghana Ghana
    Karanta ƙarin bayani...
  • David Dacko

    Shugaban ƙasa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sangoulé Lamizana

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • Luis Cabral

    Shugaban ƙasa Guinea-Bissau Guinea-Bissau
    Karanta ƙarin bayani...
  • Godfrey Binaisa

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • William Tolbert

    Shugaban ƙasa Laberiya Laberiya
    Karanta ƙarin labarai...
  • Mohamed Mahmoud Ould Louly

    Shugaban ƙasa Murtaniya Murtaniya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Jean-Bedel Bokassa

    Shugaban ƙasa/Sarki Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Francisco Macias Nguema

    Shugaban ƙasa Equatorial Guinea Equatorial Guinea
    Karanta ƙarin bayani...
  • Yusufu Lule

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Fred Akuffo

    Shugaban ƙasa Ghana Ghana
    Karanta ƙarin bayani...
  • Mustafa Ould Salek

    Shugaban ƙasa Murtaniya Murtaniya
    Karanta ƙarin bayanai...
  • Idi Amin Dada

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Joachim Yhombi-Opango

    Shugaban ƙasa Kongo Kongo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Moktar Ould Daddah

    Shugaban ƙasa Murtaniya Murtaniya
    Ƙaranta ƙarin bayani...
  • Ignatius Kutu Acheampong

    Shugaban ƙasa Ghana Ghana
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ali Soilih

    Shugaban ƙasa Komoros Komoros
    Karanta ƙarin bayani...
  • Tafari Benti

    Shugaban ƙasa Habasha Habasha
    Karanta ƙarin bayani...
  • James Mancham

    Shugaban ƙasa Seychelles Seychelles
    Karanta ƙarin bayani...
  • Michel Micombero

    Shugaban ƙasa Burundi Burundi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ahmed Abdallah Abderemane

    Shugaban ƙasa Komoros Komoros
    Karanta ƙarin bayani...
  • Yakubu Gowon

    Shugaban ƙasa Najeriya Najeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • François Tombalbaye

    Shugaban ƙasa Chadi Chadi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Richard Ratsimandrava

    Shugaban ƙasa Madagascar Madagascar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Gabriel Ramanantsoa

    Shugaban ƙasa Madagascar Madagascar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Aman Mikael Andom

    Shugaban ƙasa Habasha Habasha
    Karanta ƙarin bayani...
  • Haile Selassie I

    Sarki Habasha Habasha
    Karanta ƙarin bayani...
  • Hamani Diori

    Shugaban ƙasa Nijar Nijar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Grégoire Kayibanda

    Shugaban ƙasa Rwanda Rwanda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Justin Ahomadegbe- Tometin

    Shugaban ƙasa Benin Benin
    Karanta ƙarin bayani...
  • Philibert Tsiranana

    Shugaban ƙasa Madagascar Madagascar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Dakta Kofi Busia

    Firaminista Ghana Ghana
    Karanta ƙarin bayani...
  • Milton Obote

    Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Emile Derlin Zinsou

    Shugaban ƙasa Benin Benin
    Karanta ƙarin bayani...
  • Abdirashid Ali Sharmarke

    Shugaban ƙasa Somaliya Somaliya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sarki Idris I

    Sarki Libya Libya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ismail al-Azhari

    Shugaban ƙasa Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Modibo Keita

    Shugaban ƙasa Mali Mali
    Karanta ƙarin labarai...
  • Alphonse Massamba-Débat

    Shugaban ƙasa Kongo Kongo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Andrew Juxton-Smith

    Shugaban ƙasa Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Christophe Soglo

    Shugaban ƙasa Benin Benin
    Karanta ƙarin bayani...
  • David Lansana

    Jagora Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Siaka Stevens

    Firaminista Saliyo Saliyo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Nicolas Grunitzky

    Shugaban ƙasa Togo Togo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ntare na huɗu

    Sarki Burundi Burundi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Leopold Biha

    Firaminista Burundi Burundi
    Karanta ƙarin bayani...
  • Kwame Nkrumah

    Shugaban ƙasa Ghana Ghana
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sarki Mutesa na biyu na Buganda

    Sarki/Shugaban ƙasa Uganda Uganda
    Karanta ƙarin bayani...
  • Abubakar Tafawa Balewa

    Firaminista Najeriya Najeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Maurice Yemeogo

    Shugaban ƙasa Burkina Faso Burkina Faso
    Karanta ƙarin bayani...
  • David Dacko

    Shugaban ƙasa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sourou-Migan Apithy

    Firaminista Benin Benin
    Karanta ƙarin bayani...
  • Moïse Tshombe

    Firaiminista DR Congo DR Congo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Ahmed Ben Bella

    Shugaban ƙasa Aljeriya Aljeriya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Leon M'ba

    Shugaban ƙasa Gabon Gabon
    Karanta ƙarin bayani...
  • Hubert Maga

    Shugaban ƙasa Benin Benin
    Karanta ƙarin bayani...
  • Fulbert Youlou

    Shugaban ƙasa Kongo Kongo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Sylvanus Olympio

    Shugaban ƙasa Togo Togo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Patrice Lumumba

    Firaminista DR Congo DR Congo
    Karanta ƙarin bayani...
  • Abdallah Khalil

    Firaminista Sudan Sudan
    Karanta ƙarin bayani...
  • Muhammad VIII al-Amin

    Sarki Tunisiya Tunisiya
    Karanta ƙarin bayani...
  • Muhammad Naguib

    Shugaban ƙasa Masar Masar
    Karanta ƙarin bayani...
  • Farouk na Masar

    Sarki Masar Masar
    Karanta ƙarin bayani...

Sabon yayi

Afirka ta fuskanci juyin mulki takwas da suka yi nasara cikin shekara uku da suka gabata. Yayin juyin mulki na baya-bayan nan da aka fuskanta na zuwa ne bayan da sojoji suka farfaɗo bayan shafe kusan shekara 20 rabonsu da yayin juyin mulkin, bayan yayinsa da suka yi a shekarun 1970.

Mutu-ka-raba

Wasu jagororin da suka ƙwace iko, sun yi mulki na gomman shekaru, yayin da wasu kuma aka tumɓuke su cikin kwanaki bayan kwace mulkin.

Alal misali Shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Obiang Nguema ya shafe shekara 44 yana mulki bayan ƙwace iko a shekarar 1979.

A yanzu shi ne shugaban ƙasa a Afirka da yafi jimawa a kan mulki.

Shugabannin da suka sake komawa bayan kifar da su

Juyin mulki a Yammacin Afirka da yankin Sahel

Mafi yawan ƙasashen yankin Sahel sun fuskanci juyin mulkin soji. Juyin mulki na baya-bayan nan a yankin shi ne wanda aka yi a Jamhuriyar Nijar da Gabon a 2023

Shugabannin soji sun kuma ƙwace mulki a Mali a 2020 da 2021 da Chadi da Guinea da Sudan a 2021. Burkina Faso ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a 2022, Duka waɗannan ƙasashe rainon Faransa ne, in ban da Sudan.

Tun 2000, kashi uku cikin huɗu na juyin mulkin da suka samu nasara a Afirka sun auku ne a ƙasashe rainon Faransa. Hakan ya sa wasu ke aza ayar tambaya cewa ko tasirin Faransa a Afirka ne ke haddasa hakan.

Juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka tun 1952

Zaɓi daga ƙasashe

Yawan juyin mulki

0

2

4

6

8

Mafi yawan ƙasashen Yammacin Afirka da na Tsakiya sun fuskanci yawan juyin mulkin da ya yi nasara. Kusan rabin ƙasashen yankin 17 sun fuskanci aƙalla juyin mulki huɗu a Yammacin Afirka

Burkina Faso ce ta fi kowace ƙasa yawan juyin mulki a Afirka inda ta fuskanci takwas, daga nan sai Saliyo da Uganda masu bakwai kowannensu.

Kashi ɗaya cikin uku na ƙasashen Afirka, mafi yawancinsu daga Gabashi da Kudanci Afirka ne ba su taɓa fuskantar juyin mulkin da ya yi nasara ba

Mai shekara 34, a 2024, Ibrahim Traore ya kasance shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a duniya. Ya zama shugaban riƙon ƙwarya na Burkina Faso bayan da sojoji suka yi juyin mulki ranar 30 ga watan Satumban 2022, inda suka kifar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Paul-Henry Sandaogo Damiba.

Kwace mulki

Kusan kashi 90 na juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka, sojoji ne suka yi, daga nan sai sojojin haya masu kashi huɗu. Sauran nau'ikan juyin mulki da ka yi a Afirka sun ha ɗa da boren fararen hula, mulkin mallaka, dakarun tawaye da juyin mulkin masarauta.

Gaba kura baya tsayaki

Mafi yawan shugabannin da suka karɓi mulki da ƙarfi, daga baya wasu ne ke hamɓarar da su, a wasu lokuta ma a kashe su

A 1972 Janar Ignatius Kutu Acheampong ya jagoranci juyin mulki da babu zubar da jini, wajen tumbuƙe zaɓaɓɓiyar gwamnatin Firaministan Ghana Dakta Kofi Busia. Shekara shida bayan haka aka tuɓuke shi a wani juyin mulkin masarauta sannan kuma aka kashe shi shekara guda bayan haka.

Thomas Sankara ya zama shugaban Burkina Faso a 1983, bayan wani juyin mulki da sojoji suka yi a madadinsa, a lokacin da yake ƙarƙashin ɗaurin talala. A ranar 15 ga watan Oktoban 1987 wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai suka kashe Sankara a lokacin wani juyin mulki da Blaise Compaore ya jagoranta.

Gaafar Nimeiry ya tunɓuke shugaban Sudan Ismail al-Azhari a 1969, sannan ya karɓe iko, da farko a matsayin shugaban mulkin soji, sannan ya zama shugaban ƙasa, kafin a kifar da gwamnatinsa a 1985.

Jean-Baptiste Bagaza ya tumɓuke shugaban ƙasar Burundi Michel Micombero a 1976 sannan ya karɓe mulki. shekara 11 bayan hakan ne kuma aka hamɓarar da shi, lamarin da tilasta masa gudun hijira.

Omar al-Bashir ya zama shugaban ƙasar Sudan a 1989 a lokacin da yake muƙamin Burgediya Janar a rundunar sojin ƙasar, ya jagoranci sojoji wajen kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatim ƙasar. Daga nan ya ci gaba da zama shugaban Sudan har zuwa 2019 lokacin da wani juyin mulkin soji ya kifar da gwamnatinsa.

François Bozizé Yangouvonda ya ƙwace mulki a 2003. Inda ya zama shugaban ƙasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Shekara 10 bayan haka aka hamɓarar da shi.

Barinsa a cikin dangi

Ƙwace mulki al'ada ce ta dangi a wasu ƙasashen. Alal Misali a Equatorila Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo - wanda ɗan ɗan'uwan shugaban ƙasar Francisco Macias Nguema - ne ya yi masa juyin muyin mulki a 1979. Zuwa shekarar 2024 Teodoro ne shugaban ƙasa - wanda ba na sarauta ba - na biyu mafi jimawa a karagar mulki.

Laurent Kabila ya hamɓarar da Shugaba Mobutu Sese Seko a 1997, sannan ya zama shugaban DR Kongo na uku. Daga baya kuma ɗansa mai shekara 29, Joseph Kabila ya gaje shi bayan da ɗaya daga cikin masu kare lafiyarsa ya kashe shi.