Yayin da wasu ke ganin zɓen ƙananan hukukomin Abuja zai zama zakaran gwajin dafi ga zaɓukan 2027 masu zuwa, saboda fara aiki da sabuwar dokar zaɓe ta 2025, masana na ganin ba haka ba ne.
A cikin makon nan ne dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyaran fuska.
Hakan ce ta sa wasu da dama ke ganin zaɓen zai haska hanya ko makomar zaɓuka shekarar mai zuwa.
To sai dai masana harkokin siyasa na ganin ba haka lamarin yake ba.
Farfesa Abubakar Umar Kari, masanin harkokin siyasa, kuma malami a Jami'ar Abuja na daga cikin masu wannan ra'ayi.
A hirarsa da BBC Malamin jami'ar ya ce har yanzu jam'iyyun hamayya na ƙoƙarin daidaita ne.
''Idan ka kula har yanzu jam'iyyun adawar ƙasar suna neman bakin zaren ne, ba su gama kafuwa ba, musamman jam'iyyar ADC'', in ji shi
Ya ƙara da cewa sakamakon zaɓen ba zai zama manuniya ga makomar zaɓukan 2027 ba, kodayake ya ce zaɓen zai iya zama gwaji ga hukumar zaɓen ƙasar.
''Saboda hakan zai nuna cewa ko ta shirya wa zaɓukan ko akasin haka, musamman gwajin sabbin na'urorin zaɓen da hukumar ta ce za a yi gwajinsu'', in ji masanin siyasar.