Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa hukumar EFCC ta aika masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je.
Ya bayyana haka ne a wata hira da BBC inda ya ce "Efcc sun rubuto min takadar gayyata zuwa ofishinsu, kuma na amsa musu zan je ranar Litinin mai zuwa"
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da ta ce jami’an tsaro sun ƙwace fasfon ɗin El-Rufai a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe jim kaɗan bayan dawowarsa daga Masar.
Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X cewa "jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama shi ne bayan dawowarsa gida daga ƙasar Masar."
Da yake bayani kan bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta, El-Rufai ya ce ba shi ne ke sa’in-sa da jami’an DSS ba, illa su ne suka tare shi a filin jirgi suka buƙaci ya bi su ofishinsu.
A cewarsa "Ina sauka daga jirgin wani dan matashi ya zo ya ce min sun zo ne daga DSS, kuma suna son su gan ni a ofisihinsu sai na ce ina takardar gayyata, sai suka ce min akwai takarda, za a bani,"
Ya ce da suka fito waje sai wasu manyan jami’an DSS suka sake tare shi, sai ya sake tambayarsu takardar gayyata.
Ya ce ya shaida musu gidansa na kusa da ofishinsu, don haka su je su kawo takardar idan har akwai.
Ya ƙara da cewa babu wata doka a Najeriya ko kundin tsarin mulki da ta ba da damar a tare mutum ba tare da takarda ba.
El-Rufai, wanda ke cikin jagororin adawa a jam’iyyar ADC da ke shirin ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa, ya zargi gwamnatin APC da yi wa ƴan adawar da suka ƙi sauya sheƙa zuwa jam'iyyar barazana ta hanyar kama su da sunan bincike kan ayyukan rashawa.
Ya ce an kama kusan mutum huɗu da suka yi aiki tare da su a Jihar Kaduna, yana mai cewa yana ganin lokaci ne kafin a neme shi ma.