Rufewa
Masu bin shafin BBC Hauysa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai kai tsaye dangane da labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya ranar 17/03/2026.
Usman MINJIBIR da Isiyaku Muhammad
Masu bin shafin BBC Hauysa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Landan na Birtaniya domin fara ziyarar aiki ta yini biyu.
Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa sun je ziyarar ne bisa gayyatar sarkin Birtaniya Charles III.
Shugaban ya samu tarba daga wakilan masarautar Bitrtaniyar da jakadan Najeriya a Birtaniya, Muhammed Maidugu.
Shugaba Tinubu na tare da rakiyar wasu daga cikin muƙarraban gwamnatinsa, ciki har da ministan tsaron ƙasar, Christopher Musa.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Alhamis 19 da Juma'a 20 ga watan Maris a matsayin ranakun hutun ƙaramar Sallah a asar.
Cikin wata sanarwa da ministan da babban sakataren ma'aikatar cikin gida ta ƙasa ya fitar a amadadin ministan ma'aikatar, ya taya al'ummar Musulmin ƙasar murnar babbar sallar.
Ana sa ran gudanar da idin ƙaramar sallah tsakanin ranar Alhamis da Juma'a a ƙasar.
Mninistan ya buƙaci ƴan ƙasar su yi amfani da lokutan bukukuwan ƙaramar sallar wajen yi wa ƙasar addu'o'in neman zaman lafiya da ƙaunar juna.
Shugaban Amurka, donald Trump ya ce ''mafi yawan'' ƙawayen Amurka na ƙungiyar Nato sun ce ba sa son a janyo su cikin yaƙin Iran.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka ua ce bai yi ''mamaki ba'' game da martanin nasu.
Mista Trump ya ce ya yi imanin cewa kodayaushe tallafin Nato dama na ''ɓari ɗaya ne''.
Ya ce a yznu ba ma ya son taimakon ƙungiyar.
''Tun da mun riga yin samu nasara, a yanzu ba ma son taimakon nasu, tun da ba su taɓa bamu ba. Babu ga Japan babu ga Australia ballantana Koriya ta Kudu''.
Shugaban Amurka Donald trump ya ce Iran barazana ce, kuma kowace ƙasa ta san irin barazanar da Iran ke da ita.
Trump ya bayayna hakan ne lokacin tattaunawa da manema labarai game a fadarsa.
Yayin da aka tambaye shi game da murabus din daraktan yaƙi da ta'addanci na ƙasar, wanda ya ce ba zai ci gaba da aiki ba saboda ba ya goyon bayan yaƙin Iran.
Trump ya ce "Na karanta sanarwar ajiye aikinsa," in ji Trump.
"Ni kullum tunanina shi ne mutumin ƙwarai ne, amma da ma na san yana da rauni a fannin tsaro, rauni sosai a fannin tsaro.''
Ya ci gaba da cewa ';Ni dama ban san shi sosai, amma da na karanta sanarwar na fahimci cewa dama abin da ya kamata ya yi kenan, saboda yana cewa Iran ba barazana ba ce''.
Hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da yaƙi a yankin gabas ta tsakiya har zuwa ƙarshen watan Yuni, tashin farashin kayayyaki zai iya jefa karin mutane miliyan 45 cikin matsananciyar yunwa.
Mataimakin daraktan hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, Carl Skau ne ya bayyana hakan a matsayin wani hasashe mai ban tsoro, wanda ya ce zai kai matsalar ta yunwa a duniya zuwa wani mataki da ba a taba gani ba.
Yakin ya janyo tashin farashin man fetur a duniya, lamarin da ya ƙara tsadar sufuri da samar da taki da noman zamani.
Fadar Sarkin Musulmin Najeriya ta buƙaci Musulman ƙasar su fara duba wata ƙaramar sallah daga gobe Laraba 18 ga watan Maris.
Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce ranar Larabar 29 ga watan Ramadan za ta kasance ranar duban fari.
Sanarwar Fadar Sarkin Musulmin ta buƙaci, waɗanda suka ga watan su kai rahoto wurin mai'unguwarsu ko dagaci mafi kusa da su, domin isar da jawabin zuwa fadar sarkin musulmin.
Idan aka samu tabbacin ganin watan a ranar Laraba, za a gudanar da idin Ƙaramar Sallah ranar Alhamis 19 ga watan Maris.
Sai dai idan ba a ga watn a ranar Laraba, hakan na nufin za a cika azumi 30, inda za a yi sallah ranar Juma'a.
Shugaban Najeriya ya umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar su gaggauta komawa birnin Maiduguri na jihar Borno, inda aka kashe aƙalla mutum ashirin da uku a harin bama-bamai a jiya Litinin.
Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da harin, inda ya bayyana su a matsayin muggan ayyukan ‘yan ta’adda a ƙoƙarin su na sanya tsoro a zukatan al'umma.
Jami’ai sun ce an samu fashewar bama-bamai ne bayan da sojoji suka daƙile wani hari da wasu da ake zargin mayaƙan IS ne suka kai a wani sansanin soji da ke kusa da Maiduguri.
Rundunar sojin Najeriya ta yi gargaɗin barazanar ƙaruwar hare-hare a yankin arewa maso gabas a wannan lokaci na ƙarshen watan Ramadan.
Daraktan cibiyar yaƙi da ta'addanci na ƙasar Amurka ya sanar da ajiye aiki a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ce "tunaninsa bai amince masa ya goyi bayan yaƙin da ake yi kan Iran ba".
Majalisar dattawan Amurka dai ta tabbatar da Joe Kent a matsayin mutumin da Trump ya zaɓo domin cike gurbin a watan Yulin bara.
Da yake yi wa Trump bayani a wasiƙar ajiye aikin, Kent ya ce "Iran ba ta barazana ga ƙasarmu, kuma a bayyane take cewa mu ne muka fara wannan yaƙi saboda matsin lamba daga Isra'ila da masu neman mata gindin zama masu ƙarfin faɗa a ji.
"Ina goyon bayan akidu da tsare-tsaren ƙasashen waje da ka yi kamfe da su a 2016 da 2020 da 2024 waɗanda kuma ka ɗabbaƙa a zangon mulkinka na farko.
"Har zuwa watan Yunin 2025, ka fahimci cewa yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya tarko ne aka ɗanawa Amurka na ƙarar da rayukan Amerikawa da arziƙi da cigaban dorewar ƙasarmu.
"A matsayina tsohon soja wanda ya je yaƙe-yaƙe har sau 11 kuma mutumin da ya rasa matarsa a yaƙin da Isra'ila da ƙirƙira, babu yadda za a yi na goyi bayan aikewa da matasa domin yin faɗa da ba zai amfani Amurka ba.."
Kawo yanzu dai za a iya cewa Kent ne mutum na farko da ya ajiye aikinsa bisa rashin amincewa da yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran.
Ƙasar Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai mata.
An sake kai wa babbar cibiyar makamashi ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ke Fujairah hari cikin dare, yayin da wani harin ya faɗa wata tankar mai da ke kusa.
A Iraqi kuma, ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza ya fuskanci hare-hare da jirage marasa matuƙa da roka, daga wasu da ake zaton mayaƙa ne masu goyon bayan Iran.
Farashin man fetur ya ɗan tashi na wani ɗan lokaci bayan da aka samu rahotannin cewa ba lallai ƙasashen Turai ƙawayen Amurka su taimaka wajen buɗe mashigin Hormuz ba.
Bugu da ƙari, rundunar sojin Iran ta fitar da wata sanarwa inda a ciki ta ce ta kai hare-hare kan "cibiyoyi masu muhimmanci" a martani ga rayukan ma'aikatan jirgin Dena.
Sojojin sun ce sun harba makamai masu linzami a kan Rafael Industries da ke ƙera makamai.
Majiyoyi daga sashen binciken gawarwaki na ma'aikatar lafiyar Afghanistan sun bayyana wa BBC cewa an kawo musu gawarwaki sama da 100 bayan hare-hare Pakistan na jiya Litinin.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa wasu daga cikin gawarwakin ko gane su ba a iya yi saboda raunuka. Gwamnatin Afghanistan da sashen agajin gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce an kai hari a asibitin kula da masu taɓin ƙwakwalwa.
Sai dai ita kuma Pakistan ta nanata cewa ta kai harin ne a kan abin da ta kira "ma'ajiyar makaman ƴanbindiga."
Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai mata. An sake kai wa babbar cibiyar makamashi ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ke Fujairah hari cikin dare, yayin da wani harin ya faɗa wata tankar mai da ke kusa.
A Iraqi kuma, ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza ya fuskanci hare-hare da jirage marasa matuƙa da roka, daga wasu da ake zaton mayaƙa ne masu goyon bayan Iran.
Farashin man fetur ya ɗan tashi na wani ɗan lokaci bayan da aka samu rahotannin cewa ba lallai ƙasashen Turai ƙawayen Amurka su taimaka wajen buɗe mashigin Hormuz ba.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kama hanya tare da mai ɗakinsa zuwa Birtaniya domin amsa gayyatar ziyarar aiki da fadar Birtaniya ta yi masa.
Wani bidiyo da gidan talbijin na NTA da fadar shugaban ƙasar ta wallafa ya nuna shugaba Tinubu da maiɗakinsa da mukurrabansa sun tashi daga filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa birnin London.
Wannan ce ziyara ta farko cikin shekara 37 da wani shugaban Najeriya ke kai wa fadar bisa gayyatar sarki.
Sarki Charles III na Birtaniya da mai ɗakinsa Saurauniya Camilla ne za su tarbi Shugaban na Najeriya a lokacin ziyarar da aka shirya manyan liyafa.
Ziyarar aiki da shugaban ƙasa ke kaiwa fadar Buckingham ta kasance wata muhimmiyar hanyar inganta alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashe da Birtaniya, inda ake tattauna hanyoyin cin gajiyar juna.
Rabon da shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyara Birtaniya tun a 1989, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya ziyarci mariganya Sarauniya Elizabeth II, inda ya shafe kwanaki huɗu.
Ziyarar na zuwa ne kwana ɗaya bayan da hare-haren Boko Haram suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 23 a jihar Borno.
A ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu ne kafafen watsa labaran Isra'ila suka ruwaito cewa dakarun Isra'ilar sun kashe Sakataren Majalisar Tsaron ƙasar Iran, Ali Larijani bayan kai masa hari tare da ɗansa a wani gida da "suke ɓoye".
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Kartz ya ce "an kashe" Larijani sannan kuma Firaministan Isra'ila ya bai wa dakarunsa umarnin ci gaba da farautar sauran jagororin ƙasar ta Iran.
To sai dai har kawo lokacin wallafa labarin, hukumomi a Iran ba su tabbatar ko musanta iƙrarin na Isra'ila ba.
Sai dai kuma wasu kamfanonin dillancin labarai na ƙasar, Tasnim da Mehr duka sun ce ba da jimawa ba Ali Larijani ya wallafa wasu saƙonni kuma zuwa ɗan lokaci kaɗan za su wallafa su domin kowa ya gani.
Kafafen watsa labaran ƙasar Iran sun rawaito cewa sakataren Majalisar Tsaron Iran, Ali Larijani da ƙasar Isra'ila ta ce ta kashe ya wallafa saƙo a shafukansa ba da jimawa ba.
Kamfanonin dillancin labarai na Iran Tasnim da Mehr sun ce nan ba da jimawa ba za su wallafa saƙonnin na Larijani.
Kafafen watsa labaran Isra'ila sun ce sun kashe Sakataren Majalisar Tsaron ƙasar Iran, Ali Larijani bayan kai masa hari tare da ɗansa a wani gida da "suke ɓoye".
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Kartz ya ce "an kashe" Larijani sannan kuma firaiministan Isra'ila ya bai wa dakarunsa umarnin ci gaba da farautar jagororin ƙasar ta Iran.
An dai hangi Ali Larijani a cikin jerin gwanon masu nuna goyon bayan ƴancin Falaɗinawa da aka yi a Iran a ranar Juma'ar da ta gabata.
Ali Larijani ne tsohon mai shiga tsakani na Iran kan batun nukiliya sannan kuma aminin marigayi jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Sai dai kuma babu tabbacin bayanin mutuwar tasa daga hukumomin ƙasar Iran.
Karin wasu shugabannin Turai sun yi watsi da buƙatar Shugaban Amurka Donald Trump ta neman taimako wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz, da Iran ta rufe.
Bayan wani taron ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai, babbar jami’ar kula da manufofin ƙasashen waje ƙungiyar, Kaja Kallas, ta ce “babu wanda ke son yin hakan'' inda ta kara da cewa ''Wannan ba yaƙi ne na ƙasashen Turai ba''.
Shi ma shugaban Finland, Alexander Stubb, ya shaida wa BBC cewa Mista Trump ne da kanshi ya yanke shawarar ƙaddamar da yaƙi kan Iran ba tare da shawarar kowa ba, don haka kamata ya yi ya lalubo bakin zaren warware matsalar da ƙashin kansa.
Wakilin BBC ya ce shi ma shugaban gwamnatin Jamus Friedrick Merz, ya ce yaƙin na Iran, ba batu ne da ya shafi NATO ba, yayin da mahukunta a Paris, suka fito ƙarara, suka shaida wa Trump cewa ba za su aika dakarunsu mashigin Hormuz ba.
Tun da farko a Fadar White House, Shugaba Trump ya sake ragargazar kasashen duniya, da ya ce sun ja baki sun yi shiru a kan shirin nasa.
Rundunar ƴansandan jihar Gombe ta ce ta ceto wani malamin addinin Musulunci na ƙungiyar jama'atul IIzalatul bidi'a Wa'iqamatus Sunnah ta tura zuwa garin Dirin Fulani da ke karamar hukumar Nafada a jihar ta Gombe.
Ƙungiyar ta dai tura malamin ne domin yin tafsirin shekara-shekara na watan Ramadan bayan da wasu matasa mabiya ɗariƙa suka yi yunƙurin farma sa.
An dai ce matasan sun rutsa Malamin ne a wani gida bayan zargin sa da yin kalaman da ba su kamata ba kan shehunansu na darika.
Harin da aka kai wa Malam Abubakar Mahmoud Puma ya faru ne a ƙarshen mako kamar yadda rundunar ƴansandan ta Gombe ta sanar.
Ku karanta cikakken labari
Isra’ila ta ce tana kai sabbin hare-hare kan biranen Tehran na Iran da Beirut na Lebanon, yayin da hare-haren ramuwar gayya daga Iran ke ci gaba da ta'adi a ƙasashen gabas ta tsakiya da ma biranen Isra'ila.
Rahotanni sun ce an jiyo ƙarar manyan fashe-fashe a babban birnin Lebanon.
A kudancin ƙasar kuwa, ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin ƙungiyar Hezbollah da sojojin Isra’ila, wadanda ke son mamaya.
Jirage marasa matuka da makamai masu linzami sun kai hari kan harabar ofishin jakadancin Amurka a birnin Bagadaza.
Tun da fari, Iran ta kai hari kan tashar jiragen ruwa ta Fujai-rah da kuma kamfanin mai na Shah a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Masu bibyarmu barka da safiyar ranar Talata. Kamar kullum ma yau mun dawo muku da shafin kai tsaye na BBC Hausa wanda ke kawo muku labarai sahihai dangane da abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.
Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin BBC Hausa.