Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne zai jagoranci Hawan Idi na bana a cikin shirye-shiryen bukukuwan Sallah.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya, ya fitar a ranar Laraba, gwamnatin ta bayyana cewa za a fara Hawan Idi daga filin Sallar Kofar Mata, kafin a bi hanyoyin da aka tsara zuwa fadar Sarkin Kano.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro, inda ta yi gargaɗin yiwuwar wasu su tayar da rikici a yayin bukukuwan.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta jaddada cewa, duk da ƙoƙarin kare al’adun gargajiya na Kano, tabbatar da zaman lafiya da tsaro shi ne abin da ya fi muhimmanci.
A sabbin matakan da aka ɗauka, za a gudanar da Hawan Nasarawa amma ba tare da dawaki ba, yayin da aka dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau da kuma Hawan Dorayi a wannan lokaci domin dalilan tsaro.
Haka kuma, an umarci hukumomin tsaro da su ƙara sanya ido tare da tabbatar da bin dukkan ƙa’idojin da aka shimfiɗa kafin da kuma bayan bukukuwan Sallah.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu bin doka, su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da guje wa yaɗa jita-jita, tana mai tabbatar da cewa za a gudanar da bukukuwan cikin lumana.