Sojojin Najeriya sun ce sun kashe aƙalla mayaƙan masu iƙirarin jihadi 20 a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan da suka daƙile wasu hare-hare da aka kai kan sansanonin soji a farkon makon nan.
Mayaƙan Boko Haram da kuma Iswap sun ƙara tsananta hare-haren da suke kai wa sojoji da fararen hula, yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalar tsaron da ta shafe kusan shekaru 16.
Rahotanni sun ce jerin hare-haren da mayaƙan suka kai a ranar Litinin sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 14, ciki har da sojoji 10 a jihohin Borno da Yobe, kamar yadda majiyoyin farar hula da na soji suka bayyana.
Mai magana da yawun rundunar soji a yankin, Sani Uba, ya ce a cikin wata sanarwa da aka rubuta ranar Laraba kuma aka fitar ranar Alhamis cewa sojoji sun daƙile “hare-haren da aka tsara tare” da mayaƙan ISWAP wanda suka kai kan sansanin soji a Goniri da ke jihar Yobe daga daren Litinin zuwa safiyar Talata.
Ya ce “an kashe sama da mayaƙan masu tayar da ƙayar baya 20, ciki har da wani babban kwamandan su mai suna Abu Yusu, wanda aka bayyana a matsayin Munzir na Dursula.”
Uba ya ƙara da cewa wasu sojoji sun samu raunuka, amma bai bayyana adadinsu ba.
Wani mazaunin ƙauyen Katarko da ke kusa da wurin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a farkon makon da ya gabata cewa mayaƙan sun kashe sojoji huɗu sannan suka ƙona gine-gine da motocin soji a Goniri.
Matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 tare da raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
A makon da ya gabata kuma, mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji bakwai da fararen hula 11 lokacin da suka kai hari kan sansanin soji sannan suka afkawa garin Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza da ke kusa da iyakar Kamaru, inda suka harbe wasu mazauna tare da yin garkuwa da wasu.
A watan Fabrairu ne Amurka ta fara tura sojojinta zuwa Najeriya domin ba da tallafin fasaha da horo ga sojojin ƙasar wajen yaƙar ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.