Ƙwallon kafar Italiya na cikin wani yanayi mai matukar muni a gasar Champions League, inda akwai yiwuwar babu ko ɗaya daga Serie A da za ta kai zagayen na biyu wato na ƴan 16 a bana.
Tun bayan dawo da tsarin zagayen ƴan 16 a kakar 2003-04, a ko da yaushe akwai aƙalla wakili guda daga Italiya.
A lokuta 12 cikin shekaru 22 da suka wuce ma har ƙungiya uku ne suka kai wa wannan mataki.
Ba a taɓa samun kakar da babu ko ɗaya ba daga mai buga Serie A tun 1987-88, lokacin da Napoli ta fita a zagayen farko na European Cup a hannun Real Madrid.
A kakar bana Inter Milan ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da Bodo/Glimt ta yi waje da ita, wasan da ya bayar da mamaki.
Inter ta fara rashin nasara 3-1 a wasan farko, sannan aka doke ta 2-1 a San Siro, kenan an yi mata 5-2 gida waje kenan.
Wannan ne karo na farko da Inter ta fita daga Champions League a hannun ƙungiya ba daga manyan lig-lig biyar na Turai ba, wato Ingila ko Sifaniya ko Jamus ko Italiya ko kuma ta Faransa.
Yanzu dai hankali ya koma kan Juventus, wadda aka ci 5-2 a wasan farko a Galatasaray - za ta karɓi bakuncin wasa na biyu ranar Laraba.
Ita kuwa Atalanta 2-0 aka doke ta a karawar farko a gidan Borussia Dortmund da za ta karɓi bakuncin karawa ta biyu.
Idan ƙungiyoyin biyu suka kasa kai wa zagaye na biyu, zai zama tarihi mafi muni da ba wata daga Serie A a zagaye na biyu a Champions League cikin shekara 40.
Wannan lamarin zai rage martabar Serie A a Turai da hasarar samun kuɗin shiga da karin matsin lamba ga kociyoyi da shugabanni, sannan za a iya rage ƙungiyoyin da za su shiga babbar gasar tamaula ta Champions League a baɗi.